Gwamna Abba Ya Amince da Auren Gata a Kano, Ya Ware N1.5bn don Rage Gwauraye

Gwamna Abba Ya Amince da Auren Gata a Kano, Ya Ware N1.5bn don Rage Gwauraye

  • Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta shirya gudanar da auren gata ga dubunnan mutane
  • Shugaban hukumar Hisbah na jihar Kano, Aminu Ibrahim Daurawa ya bayyana cewa shirye-shirye sun yi nisa don gudanar da shirin
  • Sheikh Daurawa ya bayyana cewa gwamnati za ta biya sadaki tare da ba da jari ga amare domin su samu jari bayan aure

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Babban kwamandan hukumar Hisbah ta jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya bayyana cewa shirye-shirye sun yi nisa domin gudanar da auren gata na ma'aurata 1,500.

Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya ce gwamnatin jiha ke ɗaukar nauyin shirin, inda aka ware kuɗi Naira biliyan 1.5 domin gudanar da shi.

Gwamna Abba ya amince da auren gata a Kano
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ce Sheikh Daurawa ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a Kano ranar Litinin, 15 ga watan Yunin 2026.

Kara karanta wannan

Abin tausayi: Ɗan kasuwa ya mutu a wani yanayi a ɗakin fitacciyar 'yar TikTok a jihar Kano

Ana shirin auren gata a jihar Kano

Sheikh Daurawa ya ce ɓangare na shirye-shiryen ya ƙunshi gwaje-gwajen lafiya na kafin aure kamar su kwayar cutar kanjamau (HIV), cutar hanta juna biyu, da kuma gwajin nau'in jini (genotype) da sauran su.

Ya bayyana cewa za a kashe kusan N1m a kan kowane ma'aurata domin samar musu da kayan gida da suka haɗa da gado, katifa, zanen gado, matashin kai, kujeru da kayan abinci.

Gwamnatin Abba za ta biya sadaki

A cewarsa, za a biya sadaki naira 100,000 ga kowace amarya, yayin da za a sake ba amaryar ƙarin naira 100,000 a matsayin kuɗin jari domin tallafa wa ƙananan sana'o'i bayan aure, jaridar The Punch ta kawo rahoton.

“Auren gata yana ɗaya daga cikin alƙawuran da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi wa al'ummar Kano lokacin yakin neman zaɓensa, kuma yanzu ya cika shi."
“Gwamnan ya amince da Naira biliyan 1.5 don ma'aurata 1,500, inda kowane ma'aurata za su amfana da kusan N1m da aka ware domin kujeru, kayan abinci, da tallafi.”

Kara karanta wannan

Jerin gwamnonin jihar Ekiti daga 1999 zuwa yau yayin da ake shirin sabon zabe a 2026

- Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

Gwamna Abba zai yi auren gata a Kano
Shugaban hukumar Hisbah na Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa Hoto: Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa
Source: Facebook

Hisbah ta kafa sharadin aure

Babban kwamandan ya kuma bayyana cewa Hukumar Hisbah ta sanar da waɗanda ke da niyyar auren wata ƙa'ida ta jagoranci wadda ke hana sakin aure ba tare da sa hannun hukumar ba.

Ya shawarci masu niyyar auren da su tabbatar sun yi gwajin nau'in jini (genotype) kafin aure saboda haɗarin da ke tattare da haifar yara masu ɗauke da cutar amosanin jini.

Daurawa ya ƙara da cewa za a sanar da ranar gudanar da auren gatan da zarar Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da ita.

Ba auren gata ba ne matsalarmu

Ibrahim Zulkiful da ke Kano ya soki shirin auren gatan da gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf ke yi.

"Ba auren gata ba ne matsalarmu. Wannan barnatar da kudi ne ta hanyar da ba ta dace ba. Akwai abubuwa da yawa da gwamnati ya kamata ta magance."
"Almubazzaranci ne kashe N1.5bn don gudanar da auren gata yayin da har yanzu an gagara samar da ingantaccen ruwan sha."

Kara karanta wannan

Sarki Sanusi II ya yi magana kan beli 'mai tsauri' da aka saka wa El Rufa'i

- Ibrahim Zulkiful

Hisbah za ta yi gwajin lafiya don auren gata

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kammala shirye-shiryen gudanar da gwajin lafiya a kan ma’aurata 3,000 da ake sa ran za su amfana da shirin auren gata.

hukumar ta Hisbah ta bayyana cewa ma’auratan da za a yi wa gwaje-gwajen lafiya na dole sun haɗa da mata 1,500 da maza 1,500 domin tabbatar da lafiyarsu.

Hisbah ta yi gargaɗin cewa duk wanda ya kasa bayyana domin yin gwajin za a cire sunansa daga cikin waɗanda za su amfana da shirin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng