Lokaci Ya Yi: Alhaji daga Najeriya Ya Yi Bankwana da Duniya a Saudiyya
- Daya daga cikin Alhazan Najeriya da suka kammala aikin Hajji a kasa mai tsarki watau Saudiyya, ya gamu da ajalinsa kafin ya dawo gida
- Marigayin wanda ya fito daga jihar Neja ya yi bankwana da duniya ne sakamakon wani hatsarin mota da ya ritsa da shi a birnin Makkah na Saudiyya
- Hukumar jin dadin Alhazai ta jihar Neja ta aika da sakon ta'aziyyarta ga iyalan mamacin da al'ummar Musulmi baki daya kan wannan rashin da aka yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Makkah, kasar Saudiyya - An tabbatar da mutuwar wani maniyyaci ɗan shekara 43 daga Jihar Neja, Alhaji Salisu Ibrahim, a birnin Makkah na kasar Saudiyya.
Marigayin ya yi bankwana da duniya ne bayan ya kammala aikin Hajjin bana na shekarar 2026 a kasa mai tsarki watau Saudiyya.

Source: Facebook
Jami’an hulɗa da jama’a (PRO) na hukumar jin dadin Alhazai ta jihar Neja, Jibrin Usman-Kodo, ya bayyana hakan a ranar Litinin, 15 ga watan Yunin 2026, rahoton jaridar Vanguard ya nuna hakan.
Hatsarin mota ya ritsa da marigayin
A cewarsa, Alhaji Salisu Ibrahim, wanda ɗan asalin karamar hukumar Kontagora ne, ya rasu ne sakamakon raunukan da ya samu a wani hatsarin mota a birnin Makkah.
Ya ce marigayin ya samu hatsarin ne lokacin da yake dawowa daga Masallacin Harami bayan ya gudanar da ibada, Daily Post ta kawo rahoton.
An yi jana'izar Alhaji daga Neja
A cewar jami'an hulɗa da jama'an, mamacin ya rasu ne ranar Asabar, 13 ga watan Yuni, kuma an birne shi a birnin Makkah daidai da tsarin shari'ar Musulunci.
"Hukumar tana bayyana matsanancin alhini game da wannan babban rashi mai ban takaici sannan tana mika saƙon ta'aziyya ga iyalan mamacin, al'ummar karamar hukumar Kontagora, da daukacin al'ummar Musulmi baki ɗaya."

Kara karanta wannan
Fada ya barke tsakanin kungiyoyin 'yan bindiga a Kaduna, an kashe manyan jagorori 4
- Jibril Usman-Kodo
Ana jigilar Alhazan Neja zuwa Najeriya
Jibril Usman-Kodo ya ce an riga an kwaso daukacin Alhazai 343 daga jihar zuwa gida Najeriya a rukunin farko, yayin da rukuni na biyu na mutane 345 ake sa ran isarsu ranar Litinin, 15 ga watan Yunin 2026.
Ya ce rukuni na biyu ya ƙunshi Alhazai ne da aka zabo daga karamar hukumar Kontagora, Rijau, Mashegu da kuma Chanchaga.
“Rukuni na biyu na alhazai 345 masu dawowa gida zuwa jihar Neja sun isa filin jirgin sama na kasa da kasa na King Abdulaziz da ke Jeddah, inda suke fuskantar aikin tantancewa da shiga jirgi gabanin tafiyarsu ta komawa gida."
- Jibril Usman-Kodo

Source: Twitter
Alhaji dan Najeriya ya rasu a Makkah
A wani labarin kuma, kun ji cewa wani Alhaji daga Najeriya wanda ake kyautata zaton ya fito ne daga jihar Bauchi, ya yi bankwana da duniya a Muzdalifah.
Jami’an tsaron Saudiyya da ma’aikatan lafiya na gaggawa sun kwashe gawar mamacin daga wurin da ya rasu bayan mahajjata sun kwana suna tafiya daga Arafa zuwa Muzdalifah.
Marigayin ya rasu ne a wani lokaci mai wahala na aikin Hajji wanda ke tattare da yawan zirga-zirgar mahajjata tsakanin wurare masu tsarki karkashin tsananin yanayin zafi da dumbin jama’a.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
