"Muna Kira ga Fannin Shari'a"; Atiku Ya Dauki Zafi kan Umarnin Kotu na Soke Rajistar ADC
- Wata kotun tarayya ta ba da umarnin soke rajistar jam'iyyar ADC da wasu jam'iyyu hudu na siyasa a ranar Litinin, 15 ga watan Yunin 2026
- Dan takarar shugaban kasa na ADC a zaben 2027, Atiku Abubakar, ya yi Allah wadai da hukuncin da kotun ta yanke
- Atiku Abubakar ya bayyana cewa hukuncin kotun ya nuna wani kokari da ake yi domin ruguza jam'iyyun adawa a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma ɗan takarar Shugaban Ƙasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya yi martani kan hukuncin kotundin sake rajistar jam'iyyar.
Atiku ya ya yi Allah-wadai da hukuncin da ke neman soke rajistar ADC da wasu jam'iyyun hamayya da dama.

Source: Twitter
Jaridar Daily Trust ta ce Atiku ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da hadiminsa, Phrank Shaibu, ya fitar a ranar Litinin, 15 ga watan Yunin 2026.
Me Atiku ya ce kan hukuncin kotu
Dan takarar shugaban kasar ya siffanta matakin a matsayin babban karan tsaye ga tsarin mulki na dimokuradiyya da kuma wani shiri da aka tsara don kawar da 'yan adawa gabanin babban zaɓen 2027.
Atiku ya ce ya kamata wannan hukunci ya tayar wa kowane ɗan Najeriya da ya yi imani da dimokuradiyya, jam'iyyu masu yawa, da bin doka da oda hankali, rahoton The Punch ya nuna hakan.
Ya lura cewa hukuncin yana da matukar damuwa musamman saboda an bayar da shi ne a daidai lokacin da akwai umarni na kotun ɗaukaka ƙara wanda ya dakatar da duk wani abu har sai an kammala sauraren ƙarar da aka ɗaukaka.
Atiku ya yi zargin yi wa dimokuradiyya karan tsaye
“Wannan hukunci yana nuna wani babban haɗari na salon mulkin kama-karya da kuma karan tsaye na fili ga dimokuradiyyar Najeriya."
“Abin da ya sa lamarin ya fi ban tsoro shi ne cewa an bayar da wannan hukuncin ne duk da cewa akwai bayyanannen umarnin kotun ɗaukaka ƙara."
- Atiku Abubakar
Atiku ya ce hukuncin ya dace da wani salon zaluncin siyasa da amfani da hukumomi da ake yi don raunana jam'iyyun hamayya kafin zuwan zaɓe mai zuwa.
“Yana ƙara fitowa fili cewa gwamnatin Tinubu ta mayar da hankali ne kawai wajen kawar da manyan abokan hamayyar siyasa gabanin 2027."
“Maimakon fuskantar tarin matsalolin da ke damun ƙasar, kamar rashin tsaro da ya yi yawa, wahalar tattalin arziki, ƙaruwar talauci, rashin aikin yi, gwamnatin ta shagaltu da neman hanyar lallata kowane fage na hamayya mai ƙarfi."
“Wannan ba shugabanci ba ne. Kawar da abokan hamayya ne ta wasu hanyoyin."
- Atiku Abubakar

Source: Facebook
Atiku ya ce ana kokarin ruguza adawa
“Al'ummar Najeriya suna ganin abin da ke faruwa. Ana kai hari ga jam'iyyun hamayya. Ana matsa wa hukumomin dimokuradiyya lamba. Ana ƙara yin amfani da ikon gwamnati ba don ci gaban ƙasa ba, sai don rayuwar siyasa.”
“Za mu ci gaba da bin dukkan hanyoyi na doka da tsarin mulki domin kare jam'iyyarmu, kare 'yancin dimokuradiyya, da kiyaye tsarin jam'iyyu da dama wanda shi ne ginshiƙin tsarin mulkinmu."
“Muna kira ga fannin shari'a, ƙungiyoyin fararen hula, kafafen yaɗa labarai, da duk 'yan Najeriya masu kishin ƙasa da su kasance cikin shiri kuma su bijire wa duk wani yunƙuri na murƙushe hukumomin dimokuradiyya don amfanin kai."
- Atiku Abubakar
ADC ta ba Amaechi tikitin takara a 2027
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar ADC ta zabi Rotimi Amaechi a matsayin dan takararta na mataimakin shugaban kasa a zaben 2027.
Jam'iyyar ta ce zabar Amaechi ya biyo bayan yin shawarwari masu zurfi, kuma hakan ya nuna bajintarsa da kwarewarsa a siyasa.
A cewar jam'iyyar ADC, gogewar siyasa da ta gudanarwa ta Rotimi Amaechi ta sa ya dace sosai da wannan matsayi.
Asali: Legit.ng


