Mataimakin Kwamishinan 'Yan Sanda, Khan Salihu Ya Rasu bayan Ya Dawo daga Masallaci
- Mataimakin kwamishinan yan sanda, DCP Khan Salihu, mai kula da harkokin kudi da gudanarwa a Rundunar ’Yan Sandan Lagos, ya rasu
- Rahotanni sun ce ya koka da cewa yana jin gajiya bayan dawowarsa daga masallaci ranar Lahadi, washe gari kuma kawai rai ya yi halinsa
- Rundunar ’yan sanda ta yi alhini, inda ta bayyana rasuwarsa a matsayin babban rashi ga hukumar baki daya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Lagos, Nigeria - Mataimakin Kwamishinan ’Yan Sanda mai kula da harkokin kudi da gudanarwa a Rundunar ’Yan Sandan Jihar Legas, DCP Khan Salihu, ya riga mu gidan gaskiya.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a bayyana a musabbabin rasuwarsa a hukumance ba.

Source: Facebook
Shin yana fama da rashin lafiya ne?
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa majiyoyi daga hedikwatar rundunar yan sanda sun bayyana cewa bayan marigayin ya dawo daga masallaci a ranar Lahadi, ya nuna alamun gajiya.

Kara karanta wannan
Bincike: 'Yan bindiga ne suka mika gawar Janar Rabe hannu da hannu? Gaskiya ta fito
Rahotannin sun ce ya nemi izinin hutun gaggawa domin ya huta a gida bayan ya ji jikinsa ba dadi.
Sai dai bayanan da aka tattaro sun nuna cewa an garzaya da shi asibiti bayan isa gida, inda likitoci suka tabbatar da rasuwarsa.
An tabbatar da rasuwar DCP Khan Salihu
A cikin wata sanarwa da jami’ar hulda da jama’a ta rundunar yan sandan Legas, SP Abimbola Adebisi, ta fitar, rundunar ta tabbatar da cewa DCP Khan Salihu ya rasu a ranar Litinin, 15 ga Yuni, 2026.
Sanarwar ta bayyana marigayin a matsayin jami’i mai kwazo, ladabi da cikakken kwarewa wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen yi wa kasa hidima.
Rundunar 'yan sanda ta yabi gudunmawar marigayin
Rundunar 'yan sandan ta ce marigayin ya yi aiki da cikakken kwarewa, aminci da rikon amana a duk tsawon lokacin da ya shafe yana aiki.
Ta kara da cewa gogewarsa da basirarsa wajen gudanar da ayyuka sun taimaka matuka wajen inganta tafiyar da harkokin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Legas.
Sanarwar ta ce:

Kara karanta wannan
"Ba ciwon sukari ba ne": Yaron Janar Rabe ya fallasa abin da ya yi zargin ya kashe mahaifinsa
“Rasuwarsa ta zo da matukar girgiza da alhini ga jami’ai da ma’aikatan rundunar. Ya kasance jagora mai kwarewa, mai tawali’u da kishin kasa.”
Kwamishinan ’yan sanda ya yi ta’aziyya
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Legas, Tijani Fatai, ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan mamacin, abokansa da abokan aikinsa a madadin jami’ai da ma’aikatan rundunar.
Ya yi addu’ar Allah Ya bai wa iyalansa hakurin jure wannan babban rashi tare da gafarta masa kurakuransa, kamar yadda Tribune Nigeria ta ruwaito.

Source: Facebook
DCP Khan Salihu zai ci gaba da kasancewa cikin a zukatan abokan aikinsa saboda sadaukarwa, kwarewa, tawali’u da kuma gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban Rundunar ’Yan Sandan Najeriya.
Rundunar ta bayyana cewa kyakkyawan tarihin aikinsa zai ci gaba da zama abin koyi ga jami’an ’yan sanda masu zuwa.
Shugaban ma'aikatan gwamnati ya rasu
A wani labarin, kun ji cewa Shugaban ma'aikatan gwamnatin jihar Benuwai da ke Arewa ta Tsakiya a Najeriya, Agbgbo Ode ya riga mu gidan gaskiya.
Rahotanni sun nuna cewa marigayin ya rasu ne bayan fama da gajeruwar rashin lafiya, lamarin da ya jefa gwamnati da ma'aikata cikin alhini da jimami.
Gwamnatin Benue ta bayyana marigayin a matsayin ginshiki a bangaren aikin gwamnati na jihar, tana mai yabawa da irin kwarewa da gudunmawar da ya bayar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng