Sauki Ya Zo: Matatar Dangote Ta Rage Farashin Man Fetur bayan Yarjejeniyar Amurka da Iran

Sauki Ya Zo: Matatar Dangote Ta Rage Farashin Man Fetur bayan Yarjejeniyar Amurka da Iran

  • Matatar man Dangote ta sanar da rage farashin da take sayar da man fetur ga 'yan kasuwa masu lodawa a mota da jiragen ruwa
  • A cewar matatar, ta rage N75 kan kowace lita biyo bayan saukin bude wuta da aka samu a yankin Gabas ta Tsakiya
  • Rage farashin da matatar ta yi na zuwa ne bayan an cimma yarjejeniya tsakanin Amurka da Iran don sake bude mashigar Hormuz

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Legas - Matatar man Dangote da ke Legas ta rage farashin da take sayar da litar man fetur ga 'yan kasuwa da take hulda da su.

Matatar Dangote ta rage farashin da take sayar da man fetur ga 'yan kasuwar da ke zuwa saya da Naira 75 a kan kowace lita.

Matatar Dangote ta rage farashin man fetur
Motocin daukar mai a matatar Dangote Hoto: Dangote Industries
Source: Facebook

Jaridar The Punch ta kawo rahoton cewa hakan na kunshe ne cikin wata wasiƙar sanarwa da aka raba wa masu sayan mai ranar Litinin, 15 ga watan Yunin 2026.

Kara karanta wannan

Farashin man fetur zai ruguzo a Najeriya bayan kammala yakin Iran da Amurka

Meyasa matatar Dangote ta rage farashin mai?

Matatar man ta ce wannan sauyin ya biyo bayan lafawar takaddama a Gabas Ta Tsakiya, wadda ta yi tasiri ga farashin makamashi a cikin watanni uku da suka gabata.

“Biyo bayan lafawar takaddama a Gabas Ta Tsakiya, wadda ta yi tasiri ga farashin makamashi. Muna son sanar da ku cewa mun sake duba farashin mai na masu lodawa a mota da masu lodawa a jiragen ruwa." Inji sanarwar.

Ta ƙara da cewa sabon farashin lodawa a mota yanzu ya dawo Naira 1,175 a kan kowace lita, kasa da naira 1,250 da ake sayarwa da farko, yayin da aka rage farashin lodawa a jiragen na kowane tan daga Naira 1,595,790 zuwa naira 1,495,215.

Yaushe sabon farashin man zai fara aiki?

Matatar man Dangote ta bayyana cewa sababbin farashin na man fetur za su fara aiki ne daga tsakar dare, jaridar TheCable ta kawo rahoton.

“A lura cewa duk sauran daukacin man da ba a kwashe ba za a sake sanya masu farashi ne a kan sabon lissafin farashin da zai fara aiki daga ƙarfe 12:00 na daren ranar Talata, 16 ga watan Yunin 2026."

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kutsa fadar sarki da dare, sun bindige matarsa bayan garkuwa da shi

“Muna nuna matukar godiya ga ci gaba da mu'amalarku da mu kuma muna tabbatar muku da alƙawarinmu na samar da kayayyaki abin dogaro da kuma kyakkyawan tsarin samar da ayyuka." In ji sanarwar
Matatar Dangote ta rage farashin man fetur
Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote Hoto: Dangote Industries
Source: Facebook

Wannan ragi na baya-bayan nan yana zuwa ne a daidai lokacin da aka samu lafawar takaddama a kasuwar mai ta duniya biyo bayan rahotannin tattaunawa da ake ci gaba da yi tsakanin Amurka da Iran kan sake buɗe mashigar Hormuz.

Matatar Dangote ta kafa tarihi

A wani labarin kuma, kun ji cewa matatar Dangote ta bayyana cewa ta kara karfin da take da shi na tace danyen mai daga ganga 650,000 zuwa sama da haka.

Matatar mai ta Dangote ta sanar da cewa ta ƙara ƙarfin tace ɗanyen mai zuwa ganga 700,000 a kowace rana daga ganga 650,000 da take yi a baya.

A cewarta, ci gaban ya nuna matatar na da damar sarrafa ƙarin ɗanyen mai tare da inganta yadda sassan samar da kayayyaki ke aiki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng