Manyan Labarai A Yau
Gwamnan Osun, Ademola Adeleke, ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ya kira shi yayin takaddamar EFCC, inda ya yi masa alkawarin zaɓe cikin adalci.
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar AAC, Omoyele Sowore, ya bayyana cewa zai dawo da tallafin man fetur idan ya samu nasarar zama shugaban kasa.
NHRC ta bukaci gwamnati ta kama tare da gurfanar da Sheikh Yahaya Jingir bisa zargin kalaman ƙiyayya da tunzura jama’a gabanin zaɓen shekarar 2027.
Gwamnan Katsina Dikko Radda ya karɓi ’yan siyasa da magoya baya daga PDP da ADC da suka koma APC a Safana, yayin da ake samun sauye-sauyen siyasa.
Tarayyar Turai ta musanta rahotannin cewa ta ƙi gayyatar INEC na sanya ido kan zaɓen shekarar 2027, tana mai cewa za ta tura ƙwararrun masu sa ido.
Zanga-zangar NLC ta dakatar da zirga-zirgar jirage a Legas, inda fasinjojin Air Peace suka makale yayin da ake bukatar ma’aikatan kamfanin su shiga kungiyar kwadago
Tsohon Ministan Muhalli Mohammed Hassan Abdullahi ya kalubalanci sakamakon zaɓen fidda gwani na ADC a Nasarawa, inda kotu ta sanya ranar 29 ga Satumba.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa ya kamata a dora alhakin kashe mutanen da aka yi a a Gabas ta Tsakiya kan kasar Jamhuriyar Iran.
Kwamitin kamfen na Imole ya zargi jam'iyyar APC da ƙoƙarin matsa wa INEC lamba domin rufe rumfunan zaɓe da wuri a wasu sassan Osun yayin zaɓen gwamna.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari