Tuna Baya: Yadda Amaechi Ya Yi Fatali da Batun Zama dan Takarar Mataimakin Shugaba Kasa a ADC

Tuna Baya: Yadda Amaechi Ya Yi Fatali da Batun Zama dan Takarar Mataimakin Shugaba Kasa a ADC

  • Tsohon Ministan sufuri a Najeriya, Rotimi Amaechi, ya samu tikitin zama dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar ADC a zaben 2027
  • A baya Rotimi Amaechi ya taba nuna bai da sha'awa ko kadan ta zama dan takarar mataimakin shugaban kasa a inuwar jam'iyyar mai adawa
  • A wancan lokaci, tsohon ministan har hasala ya yi da aka yi masa tambayar ko zai iya zama dan takarar mataimakin shugaban kasa na ADC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Rotimi Amaechi ya taba yin watsi da batun yiwuwar zama dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar ADC.

A cikin watan Mayun 2026, kwanaki kaɗan kafin zaɓen fitar da gwani na shugaban ƙasa na ADC, ya yi watsi da batun cewa zai iya zama ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam'iyyar.

Amaechi ya samu tikitin jam'iyyar ADC
Rotimi Amaechi da tambarin jam'iyyar ADC Hoto: @ChibuikeAmaechi
Source: Facebook

Amaechi ya bayyana hakan ne a cikin wata tattaunawa da tashar Trust tv, wadda aka yaɗa ranar 19 ga watan Mayun 2026.

Kara karanta wannan

Zabar Amaechi ya jawo matsala ga Atiku, Kenneth Okonkwo ya janye goyon bayansa

Martanin Amaechi kan zama dan takarar mataimaki

Yayin tattaunawar an tambayi Amaechi ko zai amince da tsarin maslaha sannan daga bisani ya karɓi matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa.

A lokacin, Amaechi yana fafatawa ne a zaɓen fitar da gwani na shugaban ƙasa na ADC tare da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da kuma Mohammed Hayatu-Deen, tsohon babban daraktan bankin FSB International Bank da ya rushe.

Sai dai, Amaechi, wanda ya nuna bacin rai a fili game da tambayar, ya gargaɗi mai tattaunawar da kada ya sake taɓo wannan batu.

“Za ka daina wannan shirmen ne? Dakata da wannan. Ban sayi fom ɗin zama mataimakin shugaban ƙasa ba. Kada ka sake faɗar hakan."
"Wannan tattaunawa ta shafi shugabancin ƙasa ce. Idan kana son tattaunawa da mataimakin shugaban ƙasa, ko zan iya janye jiki domin na nemo maka masu neman takarar mataimakin shugaban ƙasa?”

- Rotimi Amaechi

Atiku ya doke kowa zaben tsaida gwanin ADC

Kara karanta wannan

'Dalilin da ya sa tikitin Atiku da Amaechi zai kifar da Gwamnatin Tinubu a 2027'

Kusan mako guda bayan haka, Alhaji Atiku Abubakar ya lashe tikitin takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC mai adawa, jaridar TheCable ta kawo rahoton.

Ya samu ƙuri'u 1,846,370 inda ya doke Amaechi, wanda ya samu ƙuri'u 504,117, yayin da Hayatu-Deen ya zo na uku da ƙuri'u 177,120.

Amaechi ya yi watsi da sakamakon zaɓen fitar da gwanin, inda ya yi zargin hana masu kaɗa ƙuri'a damarsu da kuma tabka maguɗi a lokacin gudanar da zaɓen.

Amaechi ya taba watsi da zaben fitar da gwani na ADC
Amaechi a wajen mayar da fom din neman takara na ADC Hoto: @ChibuikeAmaechi
Source: Twitter

Amaechi ya samu tikiti a ADC

Amma a ranar Litinin, 15 ga watan Yunin 2026, tsohon gwamnan na jihar Rivers ya sauya matsaya lokacin da ADC ta ayyana shi a matsayin abokin takarar Atiku domin babban zaɓe mai zuwa.

Bolaji Abdullahi, mai magana da yawun jam'iyyar, ya sanar da zabar Amaechi a cikin wata sanarwa da ya fitar.

Atiku ya tattauna da Amaechi

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya tattauna da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar.

Atiku ya ce tattaunawar tasu ta fi mayar da hankali kan halin da Najeriya ke ciki musamman matsalar tattalin arziki da rashin tsaro.

'Dan takarar shugaban kasar ya bayyana cewa shi da Amaechi sun yi doguwar tattaunawa kan yadda kasar ke fuskantar kalubale masu yawa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng