Yadda Aka Sanya Sunayen Sanatoci 3 duk da ba Su Amince da Dakatar da Natasha ba

Yadda Aka Sanya Sunayen Sanatoci 3 duk da ba Su Amince da Dakatar da Natasha ba

  • Adams Oshiomhole ya yi zargin cewa an yi amfani da sunayen wasu sanatoci ba tare da sahalewarsu ba a batun dakatar da Natasha Akpoti-Uduaghan
  • Ya ce akalla sanatoci uku sun ce ba su sanya hannu a rahoton dakatar da Sanata Natasha ba amma kuma aka sanya sunayensu
  • Ya ambaci Sanata Ireti Kingibe a matsayin daya daga cikin wadanda suka musanta sanya hannu kan batun a Majalisar dattawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Sanata mai wakiltar Edo ta Arewa, Adams Oshiomhole, ya yi tone-tone kan batun dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan na tsawon watanni shida.

Ya yi zargin cewa an saka sunayen akalla sanatoci uku a rahoton da ya ba da shawarar dakatar da Sanata Natasha, duk da cewa ba su sanya hannu ko amincewa da rahoton ba.

Kara karanta wannan

Abin tausayi: Bayan daura aure, Amarya ta dauki wuƙa ta yanka wuyan angonta a Kano

Sanata Adams Oshiomhole.
Sanata mai wakiltar Edo ta Arewa a Majalisar dattawa, Adams Oshiomhole Hoto: Adams Oshiomhole
Source: Facebook

Oshiomhole ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi a gidan talabijin na AIT, inda yake mayar da martani ga kalaman shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa, Opeyemi Bamidele.

Tun farko, Sanata Bamidele ya bayyana dakatar da Natasha a matsayin daya daga cikin abubuwan da suka fi bata sunan majalisar dattawa ta 10.

Natasha: Sanatoci 3 ba su sa hannu ba

A cewar Oshiomhole, wasu sanatocin da sunayensu suka bayyana a cikin rahoton sun shaida masa cewa ba su sanya hannu a takardar ba kuma ba su amince da shawarwarin da ke cikinta ba.

Ya ambaci Sanata Ireti Kingibe a matsayin daya daga cikin sanatocin da suka nuna mamaki ganin sunanta a rahoton.

“Kwamitin da aka kafa ya yi zama, sannan mambobi sun sanya hannu domin nuna amincewa da rahoton.
"Idan ba ka yarda ba, za ka iya kauracewa sanya hannu. Amma wasu sun ce ba su sanya hannu ba, duk da haka an wallafa sunayensu,” in ji Oshiomhole.

Kara karanta wannan

Rana ta 3: Masu zanga zanga sun toshe titi mai muhimmanci a Abuja kan matsalar tsaro

Tsohon gwamnan jihar Edo ya ce akwai yiwuwar an yi amfani da rajistar sunayen mahalartar taro a matsayin hujjar sanya hannu, lamarin da ya bayyana a matsayin abin da bai dace ba.

Yadda aka dakatar da Natasha a majalisa

An dakatar da Natasha Akpoti-Uduaghan a watan Maris na shekarar 2025 bayan zarge-zargen rashin da’a da kuma sabawa dokokin majalisar dattawa.

Dakatarwar ta biyo bayan ci gaba da zargin da take yi wa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio na neman lalata da ita.

Matakin ya hana ta shiga harabar Majalisar dattawa, tare da dakatar da albashinta da alawus-alawus diin ta, sannan aka rufe ofishinta, kamar yadda The Cable ga ruwaito.

Majalisa.
Wasu daga cikin sanatocin Najeriya yayin zaman Majalisar dattawa a Abuja Hoto: @senate_leader
Source: Twitter

Oshiomhole ya bukaci a yi nazari

Sanata Oshiomhole ya ce idan har kalaman Bamidele gaskiya ne, ya kamata a dauke su da muhimmanci domin gano yadda aka hada rahoton da kuma ko an bi ka’idojin da suka dace wajen amincewa da shi.

Zargin na iya kara janyo muhawara kan sahihancin tsarin da aka bi wajen dakatar da Natasha da kuma yadda aka gudanar da aikin kwamitin da ya gabatar da rahoton.

Kara karanta wannan

"Talauci da jahilci sun yi kamari a Arewa": Sarki Sanusi II ya ba da mafita

Akpabio da Oshiomhole sun yi cacar baki

Kun ji cewa Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya yi musayar yawu mai zafi da Sanatan Edo ta Arewa, Adams Oshiomhole.

Rikicin ya fara ne yayin da Akpabio ke karanta bayanan zaman majalisa fa ya gabata, inda Oshiomhole ya yi kokarin magana, amma shugaban majalisar ya hana shi.

Rahotanni sun nuna cewa Sanata Akpabio da Oshiomhole, tsohon shugaban APC na kasa sun yi cacar baki mai zafi har tsawon mintuna 15.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262