Oshiomhole Ya Yi Amai Ya Lashe, Ya Canza Magana kan Batun Dakatar da Sanata Natasha

Oshiomhole Ya Yi Amai Ya Lashe, Ya Canza Magana kan Batun Dakatar da Sanata Natasha

  • Adams Oshiomhole ya musanta cewa ya yi zargin an hi cushen sa hannun sanatoci a rahoton da ya kai ga dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan
  • Sanatan Edo ta Arewa ya ce an yi masa gurguwar fahimta a kalaman da ya yi kan batun dakatarwar da aka yi wa Natasha
  • Tsohon gwamnan Edo ya ce babu wani sanata da ya kai masa ƙorafin cewa an yi amfani da sa hannunsa ba tare da izininsa ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Sanata mai wakiltar Edo ta Arewa, Adams Oshiomhole, ya musanta rahotannin da ke cewa ya zargi wasu da ƙirƙirar sa hannun sanatoci a lokacin da aka dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan.

Sanata Oshiomhole ya ce zargin cewa ya ce an ƙirƙiri sa hannun wasu sanatoci ba gaskiya ba ne kuma ya sabawa abin da ya faɗa.

Kara karanta wannan

Yadda aka sanya sunayen sanatoci 3 duk da ba su amince da dakatar da Natasha ba

Sanata Oshiomhole.
Sanata mai wakiltar Edo ta Arewa a Majalisar dattawa ta 10, Adams Oshiomhole Hoto: Adams Oshiomhole
Source: Facebook

A wata sanarwa da ya fitar a Abuja, Oshiomhole ya ce an karkatar da abin da ya faɗa yayin wata hira da ya yi a shirin Politics Today na gidan talabijin na AIT.

Ya ce bayanin da kakakin Majalisar Dattawa, Sanata Yemi Adaramodu, ya yi, wanda ya bayyana cewa babu wani sa hannu da aka ƙirƙira a tsarin da ya kai ga dakatar da Natasha Akpoti-Uduaghan gaskiya ne.

Oshiomhole ya yi amai ya lashe

A cewarsa, babu wani sanata da ya zo wajensa da ƙorafin cewa an yi amfani da sa hannunsa ta hanyar da ba ta dace ba.

“Abin da kawai na faɗa shi ne cewa wani sanata da ke cikin kwamitin ya yi iƙirarin cewa an haɗa sa hannun rajistar halarta ta wasu sanatoci da rahoton ƙarshe.
“Duk wata magana da ke nuna cewa na ce an ƙirƙiri sa hannun wani sanata ƙarya ce kuma ya kamata a yi watsi da ita,” in ji shi.

Kara karanta wannan

Abin tausayi: Bayan daura aure, Amarya ta dauki wuƙa ta yanka wuyan angonta a Kano

Rahoton Daily Trust ya hakaigo sanatan na cewa batun dakatar da Natasha Akpoti-Uduaghan ya riga ya zama tarihi, kuma Majalisar Dattawa ta ci gaba da gudanar da ayyukanta.

Abin da ya jawo kalaman Oshiomhole

Ya bayyana cewa kalamansa sun fito ne yayin da ake tattaunawa kan wata magana da mai gabatar da shirin ya danganta ga shugaban masu rinjaye na Majalisar Dattawa, Sanata Opeyemi Bamidele.

A cewarsa, idan har Bamidele ya faɗi cewa lamarin Natasha ya kasance ɗaya daga cikin mafi ƙasƙancin lokuta a tarihin Majalisar Dattawa ta 10, to kalamansa sun cancanci a ɗauke su da muhimmanci.

Majalisar dattawa.
Sanatoci yayin da suke taakiyar aiki a zauren Majalisar dattawa da ke Abuja Hoto: @NGRSenate
Source: Facebook

A karshe, Oshiomhole ya janye kalamansa, inda ya ce:

“Na yi nadama idan kalamaina sun haifar da wata damuwa ko kunya ga wani sanata ko ga Majalisar Dattawa a hukumance."

Halin da Oshiomhole ya shiga a 2020

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon shugaban APC na kasa, Adams Oshiomhole ya bayyana irin halin kadaicim da ya tsinci kansa a ciki bayan an tsige shi a 2020.

Oshiomhole, wanda ke wakiltar Edo ta Arewa a Majalisar dattawan Najeriya ta 10, ya ce mutanen da ke tare da shi sun watse sun bar shi bayan ya rasa mukaminsa a APC.

Ya ce gwamnan Ribas a wancan lokacin, Nyesom Wike ne kadai ya jawo shi a jiki, ya gayyace shi zuwa Fatakwal kuma ya ba shi lambar yabo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262