Tattaunawa tsakanin Iran da Amurka Ta Sake Tayar da Sabon Tarnaki bayan Ikirarin Trump
- Iran ta ce ba ta shiga wata tattaunawa da Amurka ba, duk da cewa Shugaba Donald Trump ya ce za a fara sababbin tattaunawa ranar Litinin
- Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta ce tattaunawarta da Oman ta shafi samar da hanyar zirga-zirga a mashigar Hormuz
- Trump ya ce sababbin tattaunawar za su mayar da hankali kan mashigar Hormuz da kuma shirin nukiliyar Iran
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Tehran, Iran - Iran ta musanta cewa tana tattaunawa da Amurka, bayan Shugaba Donald Trump ya ce za a fara sabbin tattaunawa ranar Litinin domin kawo karshen yakin da ya shiga wata na shida.
Martanin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya biyo bayan ikirarin Trump cewa ya dakatar da shirin kai sababbin hare-hare kan kasar domin bai wa kokarin diflomasiyya karin dama.

Source: Twitter
Tashar Aljazeera ta ce mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Iran, Esmaeil Baqhaei, ya bayyana hakan yayin da yake tattaunawa da manema labarai.
Iran ta musanta tattaunawa
A makon da ya gabata, Trump ya yi barazanar kai wa Iran hari “mai tsanani”, yayin da rahotanni suka ce shugaban na Amurka yana duba yiwuwar sake kai hare-hare, ciki har da kan kayayyakin samar da makamashi.
Sai dai shugaban ya ja da baya daga barazanar ranar Asabar, yana cewa an samu wasu muhimman sharuddan da za su iya haifar da yarjejeniya.
Sai dai ma’aikatar harkokin wajen Iran ta ce babu wata tattaunawa da Amurka a halin yanzu. Mai magana da yawun ma’aikatar, Esmaeil Baqaei, ya ce:
“Ba ma tattaunawa da Amurka a halin yanzu. Tattaunawarmu da Oman ta shafi tabbatar da hanyar wucewa ta mashigin Hormuz.” In ji shi
Rikicin mashigar Hormuz
Mashigar Hormuz ya zama daya daga cikin manyan batutuwan da ke kawo cikas ga kokarin kawo karshen yakin.
Iran ta hana wasu jiragen ruwa wucewa ta wannan muhimmiyar hanyar kasuwanci, tare da harba wasu jiragen ruwa na kasuwanci.
Kafin fara yakin, jiragen ruwa suna wucewa cikin ’yanci ta mashigar, amma Iran yanzu ta ce za ta ci gaba da kula da hanyar tare da karbar kudin wucewa, matakin da Amurka ta ki amincewa da shi.
Haka kuma, Tehran ta ki amincewa jiragen ruwa su bi wata hanya daban da wadda ta yi kusa da gabar tekun Iran.
Tashar Channels tv ta ce a ranar Lahadi, Baqaei ya shaida wa gidan talabijin na kasar cewa an kusa cimma yarjejeniya da Oman kan yadda za a gudanar da zirga-zirga a mashigar.
“Yanzu muna dab da cimma matsaya kan hanyar da bangarorin biyu za su amince da ita, wadda ba ta arewa ba ce kuma ba ta kudu ba, amma za ta mutunta ikon bangarorin biyu tare da kare muradun kasarmu da tsaronta.” In ji shi
Sai dai ya jaddada cewa irin wannan yarjejeniya ba ta nufin za a sake bude mashigin Hormuz.

Source: Getty Images
Trump ya ya magana kan tattaunawa
Trump ya shaida wa manema labarai ranar Lahadi, 2 ga watan Agustan 2026 cewa sababbin tattaunawar da za a yi da Iran za su shafi mashigin Hormuz da kuma batun kawar da makaman nukiliya daga Iran.
Trump ya ce:
“Yanzu abin da muke yi shi ne muna tattaunawa da su a matsayin wani bangare na shawarwari. Za a fara ranar gobe da rana.”
Shugaban kasar na Amurka bai bayyana inda za a yi tattaunawar ko wadanda za su halarta ba.
Jirgin yakin Amurka ya yi hatsari
A wani labarin kuma, kun ji cewa wani jirgin yaƙin F-35B na rundunar sojojin ruwan Amurka ya yi hatsari kusa da sansaninsu da ke San Diego a jihar California.
Rundunar Amurka ta bayyana cewa an ayyana lamarin a matsayin ɗaya daga cikin manyan hatsurran jiragen sama na soji.
Asali: Legit.ng


