NDC Ta Kafa Sharadi ga Yan Takarar Gwamna da na Majalisu kafin Mika Sunaye ga INEC

NDC Ta Kafa Sharadi ga Yan Takarar Gwamna da na Majalisu kafin Mika Sunaye ga INEC

  • Jam’iyyar NDC ta umurci dukkan ’yan takarar da ta tsaida su sanya hannu kan takardar rantsuwa kafin a mika sunayensu ga hukumar INEC
  • Takardar ta kunshi sharadin cewa duk wanda ya ci zabe sannan ya fice daga jam’iyyar zai rasa kujerarsa, a cewar NDC
  • Dokar ta shafi ’yan takarar gwamna, majalisun dokokin tarayya da na jihohi, amma ba ta hau kan 'dan takarar shugaban kasa ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Jam’iyyar NDC ta bullo da wata sabuwar doka da za ta tilasta wa ’yan takararta sanya hannu kan takardar rantsuwa da ke tabbatar da cewa za su mika kujerunsu idan suka sauya sheka bayan sun ci zabe.

NDC ta ce sanya hannu kan wannan takarda zai zama sharadi kafin a tura sunayen ’yan takara zuwa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) lokacin da za ta bude shafinta na karbar sunaye a ranar 26 ga watan Yuni, 2026.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya ware rukunin 'yan bindigan da zai yi sulhu da su idan ya zama shugaban kasa a 2027

NDC .
Peter Obi, Sanata Rabiu Kwankwaso da magoya baya a babban taron NDC na kasa Hoto: Peter Obi
Source: Twitter

NDC ta ce kujera ta jam’iyya ce

Jaridar The Nation ta ce shugaban NDC na kasa, Moses Cleopas, ne ya sanar da sabon tsarin yayin wani taron sanya hannu kan takardun rantsuwar a hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja.

A cewarsa, manufar wannan mataki ita ce kare kuri’un jama’a, karfafa da’a a cikin jam’iyya da kuma dakile yawaitar sauya sheka bayan an ci zabe.

“Kujerar ta jam’iyya ce da kuma jama’ar da suka kada kuri’a ta hanyar wannan dandali. Idan ka bar NDC bayan ka ci zabe, ba za ka ci gaba da rike kujerar ba,” in ji Cleopas.

Dalilin kafa sharadi ga 'yan takarar NDC

Cleopas ya kara da cewa wannan tsari ba ya nufin kare muradun wani mutum ko bangare na musamman ba ne, sai dai kariya ga tsarin dimokuradiyya.

Shugaban jam'iyyar ya ce abubuwan da suka faru a wasu jam’iyyun siyasa sun nuna bukatar samar da karin kariya daga sauya sheka.

Kara karanta wannan

Sun yi laifi: Kotu ta ci tarar tsohon gwamna da jam'iyyar ADC Naira miliyan 1

“Mun ga yadda wasu suka ci zabe a karkashin wata jam’iyya sannan suka koma wata. Wannan shi ne abin da muke son dakatarwa,” in ji shi.

Lauyan jam’iyya ya kare matakin NDC

Mai ba NDC shawara kan harkokin shari’a, Reuben Egwuaba, ya ce kundin tsarin mulkin jam’iyyar ya tanadi cewa duk wanda aka zaba a karkashin NDC dole ne ya kasance mai biyayya ga jam’iyyar har zuwa karshen wa’adinsa.

Egwuaba ya kara da cewa ba za a tura sunan duk wani dan takara zuwa INEC ba idan bai sanya hannu kan wannan takardar rantsuwa ba.

NDC .
Tutar jam'iyyar adawa ta NDC a Najeriya Hoto: NDC Party
Source: Facebook

Wasu daga cikin ’yan takarar gwamna da na majalisun dokoki da suka halarci taron sun sanya hannu kan takardun a karshen taron.

Theo Abu, Darektan yada labaran NDC a kafofin sadarwa na zamani ya bayyana a shafinsa na X cewa wannan tsari bai shafi dan takarar shugaban kasa, Peter Obi da mataimakinsa, Sanata Rabiu Kwankwaso ba.

Da yake karin haske a safiyar Laraba, Theo Abu ya ce kundin tsarin mulki ya goyi bayan matsayar da jam'iyyarsu ta dauka, don haka sun kara tabbatar da shi ne kurum.

Kara karanta wannan

An yanke wa Hauwa'u Mukhtar hukuncin kisa, za a rataye ta a Katsina kan ta'addanci

Peter Obi ya fadi shirinsa kan tsaro

A wani labarin, kun ji cewa Peter Obi ya ce gwamnatinsa za ta hada da sulhu da matakan tsaro wajen magance rashin tsaro idan ya samu nasara a zaben 2027.

Bayan yunkurin sulhu, Obi ya kuma lashi takobin yin amfani da karfi kan yan ta'addan da suka dage sai sun ci gaba da tayar da hankali da aikata miyagun laifuffuka.

Ya ce samar da zaman lafiya mai dorewa na bukatar tattaunawa da mutanen da suka nuna aniyar rungumar sulhu da bayar da gudunmawa ga ci gaban kasa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262