Kwana Ya Kare: Fitacciyar Mai Zanen Tufafin Kwalliya, Sadia Sanusi Ta Riga Mu Gidan Gaskiya

Kwana Ya Kare: Fitacciyar Mai Zanen Tufafin Kwalliya, Sadia Sanusi Ta Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Fitacciyar mai tsara tufafin kwalliyar mata, Sadia Sanusi, wacce ta kafa kamfanin kaya da ta radawa sunanta, ta rasu a ranar 14 ga Yuni, 2026
  • Iyalanta sun tabbatar da rasuwarta a wata sanarwa da suka fitar ranar Litinin, 15 ga watan Yuni, 2026 a shafin sada zumunta
  • Kamfanin ya ce harkokinsa za su ci gaba kamar yadda aka tsara kuma za a sanar da makomar shirin Kente Artistry Masterclass nan gaba kadan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

An shiga jimami bayan tabbatar da rasuwar fitacciyar mai zanen tufafin mata kuma sananniyar mai amfani da kafafen sada zumunta, Sadia Sanusi.

Marigayiyar, wacce ta kafa kamfanin zanen tufafin mata na Sadia Sanusi, ta rasu salin-alin a ranar Lahadi, 14 ga Yuni, 2026.

Sadia Sanusi.
Fitacciyar mai tsara kayan adon mata, Sadia Sanusi Hoto: Sadia Sanusi
Source: Instagram

An tabbatar da rasuwar Sadia Sanusi

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da iyalanta da tawagar kamfanin suka fitar, kuma suka wallfa a shafin Sadiya Sanusi na Instagram a ranar 15 ga Yuni.

Kara karanta wannan

Yadda aka karbo gawar Manjo Janar Rabe Abubakar bayan ya rasu a hannun 'yan Bindiga

Sun bayyana rasuwarta a matsayin babban rashi ga iyali, abokai, abokan hulda da kuma daukacin masana’antarta ta kere-kere.

Sanarwar ta bayyana marigayiyar a matsayin mace mai manufa, kirkira da mutunci, wacce tasirinta ya zarce fannin kayan kwalliya da na zamani.

Ta ce:

“Sadia ba kawai mai zanen kaya ba ce, ta kasance mace mai hangen nesa, kirkira da kima, wacce ta yi tasiri mai zurfi a rayuwar mutane da dama.”

Iyalan marigayiyar sun bukaci jama’a, kafafen yada labarai da masu yi musu ta’aziyya da su mutunta sirrin iyalanta tare da ba su damar gudanar da zaman makoki cikin natsuwa.

Wane mataki kamfaninta ya dauka?

Kamfanin Sadia Sanusi ya tabbatar wa kwastomomi, abokan hulda da masu ruwa da tsaki cewa harkokin kasuwancinsa za su ci gaba da gudana yadda aka tsara.

Sanarwar ta ce tawagar kamfanin za ta ci gaba da gudanar da ayyuka bisa tsarin da marigayiyar ta kafa.

An kuma bayyana cewa duk tufafin da ake kan kera wa za a kammala su tare da mika su ga masu su a kan lokaci.

Kara karanta wannan

Mataimakin kwamishinan 'yan sanda, Khan Salihu ya rasu bayan ya dawo daga masallaci

Haka zalika, duk shawarwari, gwajin kaya da sauran alƙawuran da aka tsara tun da farko za su ci gaba kamar yadda aka tsara karkashin kulawar mahukuntan kamfanin.

Batun Kente Artistry Masterclass

Kamfanin ya ce yana sane da tambayoyin da ake yi kan taron Kente Artistry Masterclass da aka shirya gudanarwa a ranar 22 ga Yuni, 2026.

Sai dai ya ce za a fitar da sanarwa ta musamman nan ba da jimawa ba domin bayyana matakin da za a dauka game da shirin.

Sadia Sanusi.
Shugabar kamfanin tsara tufafin kwalliyar mata, Sadia Sanusi Hoto: Sadia Sanusi
Source: Instagram

An bukaci mahalarta taron, masu daukar nauyi da sauran masu ruwa da tsaki da su kara hakuri yayin da ake nazarin halin da ake ciki.

Iyalan marigayiyar sun jaddada cewa za su ci gaba da tafiyar da abubuwan da Sadia ta assasa, wadanda suka hada da nagarta, gaskiya da karfafa gwiwar mata da matasa.

DCP Khan Salihu ya rasu a Legas

A wani labarin, kun ji cewa mataimakin kwamishinan yan sanda na jihar Legas, DCP Khan Salihu, mai kula da harkokin kudi da gudanarwa, ya kwanta dama.

Majiyoyi daga hedikwatar rundunar yan sanda sun bayyana cewa bayan marigayin ya dawo daga masallaci a ranar Lahadi da ta gabata, ya nuna alamun gajiya.

Sai dai bayanan da aka tattaro sun nuna cewa an garzaya da shi asibiti bayan ya koma gida, inda likitoci suka tabbatar da rasuwarsa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262