Gwamna Ya Shirya Sadaukar da Ransa don Ceto Daliban da Aka Sace a Oyo
- Dalibai da malaman da 'yan bindiga suka sace a Oyo na ci gaba da zama a tsare a cikin daji wata guda bayan da aka yi garkuwa da su
- Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya bayyana cewa hukumomi na ci gaba da kokarin ganin an kubutar da su cikin aminci
- Seyi Makinde ya nuna cewa a shirye yake ya sadaukar da ransa idan har hakan zai sanya yaran su kubuta daga hannun 'yan bindiga
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Oyo - Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya bayyana cewa a shirye yake ya sadaukar da rayuwarsa kan daliban da 'yan bindiga suka sace.
Gwamna Makinde ya ce zai yi hakan ne idan har wannan zai tabbatar da kubutar da dalibai da malamai da wasu 'yan bindiga suka yi garkuwa da su a jihar.

Kara karanta wannan
Peter Obi ya ware rukunin 'yan bindigan da zai yi sulhu da su idan ya zama shugaban kasa a 2027

Source: Twitter
An yi zanga-zanga kan sace daliban Oyo
Jaridar TheCable ta ce Makinde ya yi wannan jawabi ne ranar Talata, 16 ga watan Yunin 2026 yayin da yake zantawa da masu zanga-zanga ƙarƙashin jagorancin Martins Otse, wanda aka fi sani da VeryDarkMan (VDM), a gidan gwamnatin jihar Oyo da ke Ibadan.
Daruruwan masu zanga-zanga ne suka yi tattaki ta manyan hanyoyi a babban birnin na Oyo kafin su taru a gidan gwamnatin domin neman a gaggauta ceto waɗanda aka yi garkuwa da su, waɗanda suka cika wata guda cif a tsare ranar Litinin, 15 ga watan Yunin 2026.
Gwamnan ya ce hukumomin tsaro suna ci gaba da ƙoƙari domin tabbatar da kubutar da mutanen, inda ya ƙara da cewa jami'an da ke da hannu a aikin sun fuskanci asarar rayuka, rahoton Daily Trust ya nuna hakan.
Gwamna Makinde ya shirya ba da ransa
Gwamnan mai shekara 60 ya nuna a shirya yake ya bada ransa domin wadannan mutane su kubuta.
“Jihar Oyo ba Chibok ba ce, kuma ba za ta taɓa zama Chibok ba. Mun rasa mazaje, sojoji a kan wannan batu. Zan iya tabbatar muku cewa an kashe wani Laftanar a rundunar sojojin kasa ta Najeriya kwanaki kalilan da suka gabata."
“Idan ka tambaye ni, ko zan iya sadaukar da kaina domin waɗannan yara su fito, zan yi hakan. Na yi rayuwa mai kyau. Ina kusa da shekaru 60. Wannan ba matsala ba ne. Mahaifina ma ya rasu yana da shekaru 76."
“Wannan Jihar Oyo ce. Sun sani cewa wannan ba Chibok ba ce, kuma yaranmu ba za su taɓa kasancewa a cikin yanayi irin na yaran Chibok ba."
“Muna yin duk mai yiwuwa, tare da abin da kuka ba da shawara. Amma akwai fargabar asarar rayuka. Mun riga mun rasa malami guda."
“Idan za mu iya kauce wa asarar wasu rayukan, za mu kauce mata. Amma idan muka kai ga matsayin da ya kamata a sadaukar da wasu mutane, ciki har da ni kaina, za mu yi hakan.”
- Gwamna Seyi Makinde

Source: Facebook
Makinde ya ce gwamnati ba za ta yi sulhu da masu garkuwar ba, ya yi gargaɗin cewa yin hakan zai zama tamkar mika ikon jihar ga ƙungiyoyin masu laifi ne.

Kara karanta wannan
Yan bindiga sun kutsa fadar sarki da dare, sun bindige matarsa bayan garkuwa da shi
'Yan bindiga sun kashe basarake
A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga dauke da makamai sun hallaka wani basarake a jihar Plateau da ke yankin Arewa ta Tsakiya.
'Yan bindigan sun kashe Dagacin Gwande da ke karamar hukumar Bokkos a jihar Plateau, Saf Samuel Alaket, a wani harin kwanton bauna.
Majiyoyi sun bayyana cewa 'yan bindigan sun farmake shi ne lokacin da yake kan hanyarsa ta komawa gida bayan kammala harkokinsa a kasuwa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
