Zabar Amaechi Ya Jawo Matsala ga Atiku, Kenneth Okonkwo Ya Janye Goyon Bayansa
- Zabar Rotimi Amaechi a matsayin abokin takarar Atiku Abubakar a zaben shugaban kasa na 2027 bai yi wa Kenneth Okonkwo dadi ba
- 'Dan siyasar ya bayyana cewa ya janye goyon bayansa ga dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC a zaben shekarar 2027 da ake tunkara
- Okonkwo ya nuna cewa ba zai goyi bayan tikitin da babu Ibo a dan takarar shugaban kasa ko mataimakin shugaban kasa daga yankinsa ba a zaben 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Fitaccen ɗan wasan kwaikwayo wanda ya zama ɗan siyasa, Kenneth Okonkwo, ya janye goyon bayansa ga tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar.
Kenneth Okonkwo ya janye goyon bayansa ne biyo bayan zabar tsohon Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, a matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC domin zaɓen shekarar 2027.

Source: Twitter
Kenneth Okonkwo ya sanar da matsayarsa ne a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X ranar Litinin, 15 ga watan Yunin 2026
Martanin Okonkwo kan zabar Amaechi
Tsohon mai magana da yawun kamfen ɗin shugaban ƙasa na jam'iyyar LP ya bayyana bacin ransa game da abun da ya bayyana da ci gaba da kin shigar shiyyar Kudu-maso-Gabas a cikin manyan mukaman siyasar Najeriya.
“Na ji a shafukan sada zumunta cewa ADC ta zaɓi ɗan takararta na mataimakin shugaban ƙasa daga shiyyar Kudu-maso-Kudu. Idan har wannan gaskiya ne, abin takaici ne, domin hakan zai ci gaba da nuna wariya ga shiyyar Kudu maso Gabas."
- Kenneth Okonkwo
Okonkwo ya ce ana ware yankinsa
Okonkwo ya addada cewa shiyyar ta kasance a ware cikin tsarin raba madafun iko na Najeriya tun bayan dawowar mulkin dimokuradiyya a shekarar 1999.
“Wannan shiyyar ta fannin siyasa ba ta taɓa samar da shugaban kasa ko mataimakin shugaban kasa ba tun 1999. Hana Kudu maso Gabas damar samar da shugaban kasa ko mataimakin shugaban kasa a ADC a 2027 zai zama daidai da ci gaba da tabbatar da wannan wariya."

Kara karanta wannan
"Muna kira ga fannin shari'a"; Atiku ya dauki zafi kan umarnin kotu na soke rajistar ADC
- Kenneth Okonkwo
A cewarsa, tun da farko ya buƙaci Atiku da ya zabo mataimakinsa daga Kudu maso Gabas domin damawa da yankin.
“Alfarma ɗaya tilo da na nema da farko a hannun Atiku Abubakar, wanda ya bayyana a fili cewa shi ne hanyar da za ta kai Kudu maso Gabas ga kujerar shugabancin ƙasa, ita ce ya nuna hakan ta hanyar zaɓen wani daga yankin ya zama mataimakinsa."
- Kenneth Okonkwo

Source: Twitter
Okonkwo ba zai goyi bayan Atiku ba
Okonkwo ya kammala da cewa ba zai goyi bayan kowane tikitin shugaban ƙasa da ya cire Kudu maso Gabas daga samun dan takarar shugaban ƙasa ko na mataimakin shugaban ƙasa ba.
“Idan har ta tabbata cewa ya zaɓi ɗan takara daga Kudu maso Kudu, ina yi masa fatan alheri. Ba ni da sha'awar yin yakin neman zaɓe ga kowane tikitin shugaban ƙasa da ba shi da mutumin da ya fito daga Kudu-maso-Gabas a matsayin shugaba ko mataimaki a 2027."
- Kenneth Okonkwo
Atiku ya yi wa Babachir martani
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yi martani ga tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal.
Atiku Abubakar ya zargi Babachir da yin kalamai da ka iya rusa hadin kan da ke tsakanin 'yan Najeriya da kuma nuna bambancin kabila.
'Dan takarar shugaban kasar na jam'iyyar ADC a zaben 2027 ya ce abin takaici ne yadda Babachir ya zabi yin zarge-zarge da wasu hasashe ba tare da gabatar da hujjojin da za su gaskata maganganunsa ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

