An Rasa Rayuka da Wani Bam Ya Tarwatse da Motar Sulken 'Yan Sanda a Jihar Zamfara

An Rasa Rayuka da Wani Bam Ya Tarwatse da Motar Sulken 'Yan Sanda a Jihar Zamfara

  • Jami’an rundunar ’yan sanda uku sun rasa rayukansu yayin da motarsu ta taka bam kuma ya tashi da su a jihar Zamfara
  • Lamarin ya faru ne lokacin da suka fito sintiri a titin Anka zuwa Bagega kuma jami’an da suka mutu kwararru ne a fannin lalata bama-bamai
  • Bayan fashewar bam din, ’yan bindiga sun kona motar sulke ta jami’an yan sandan suka fito sintiri da ita

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Zamfara, Nigeria - Jami’an rundunar ’yan sanda uku sun rasa rayukansu bayan wata motar sulke da suke ciki ta taka bam da ake zargin ’yan ta’adda sun birne a kan hanya a Jihar Zamfara.

Mai taimaka wa Gwamnan jihar Zamfara kan harkokin yada labarai, Mugira Yusuf, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.

Kara karanta wannan

Zargin rashawa: An samu matsala a shari'ar tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El Rufai

Dakaru.
Dakarun rundunar yan sanda suna tsakiyar aikin sintiri a Najeriya Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Bam ya tashi da motar 'yan sanda

A cewar sanarwar, jami’an suna gudanar da sintiri ne a hanyar Anka zuwa Bagega domin dakile ayyukan kungiyoyin yan bindiga lokacin da hatsarin ya afku, kamar yadda Premium Times ta rahoto

Rahoton ya ce daya daga cikin motocin sulke na rundunar yan sanda ta taka wata na’urar fashewa ta IED da aka birne a kasa.

Sunayen jami’an da suka rasu

An bayyana sunayen dakarun 'yan sandan da suka mutu wanda suka hada da Sufuritanda Janar Abdulrazak Hassan, Sufeta Murtala Musa da kuma Sufeta Auwal Ahmad

Hadimin gwamnan ya ce dukkansu kwararru ne a bangaren ganowa da lalata bama-bamai (EOD) da ke aiki da rundunar ’yan sandan Jihar Zamfara.

Bayan fashewar bam din, an ce wasu ’yan bindiga sun fito daga cikin daji, inda suka banka wa motar sulken da ta lalace wuta kafin daga bisani su koma cikin daji.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a samu jin ta bakin kakakin rundunar ’yan sandan Zamfara, DSP Yazid Abubakar, kan lamarin ba.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun lalata shirin kai harin bama bamai kan matafiya a jihar Zamfara

Sabuwar dabara daga ’yan bindiga

Masana harkokin tsaro sun bayyana amfani da bama-baman da ake birnewa a hanyoyi a matsayin wata sabuwar dabara da kungiyoyin ’yan bindiga suka fara amfani da ita a Arewa maso Yamma.

A baya, galibin hare-haren ’yan bindiga a Zamfara sun fi karkata ne kan sace mutane, satar shanu da kai farmaki kan kauyuka ta amfani da bindigogi, kamar yadda Punch ta kawo.

Dauda Lawal.
Gwamna Dauda Lawal a taron Majalisar tsaro ta jihar Zamfara Hoto: Dauda Lawal
Source: Facebook

Sai dai rahotanni sun nuna cewa yanzu wasu daga cikin wadannan kungiyoyi sun fara amfani da dabarun yaki irin na kungiyoyin Boko Haram da ISWAP da ke aiki a yankin Arewa maso Gabas.

'Yan sanda sun lalata bama-bamai

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar ’yan sandan Zamfara ta gano wasu bama-baman da ake zargin ’yan bindiga ne suka dasa a kan titin Kunchin Kalgo.

Rahotanni sun nuna cewa jami'an tsaro sun lalata abubuwan fashewar cikin nasara ba tare da sun jawo asarar rai ko dukiya ba.

Rundunar ta tabbatar wa jama’a cewa tana ci gaba da kokarin gano tare da cafke wadanda ke da hannu wajen dasa bama-baman domin gurfanar da su a gaban kuliya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262