An Dakatar da Soke Rajistar ADC, Kotun Daukaka Kara Ta ba INEC Sabon Umarni
- Kotun daukaka kara ta dakatar da aiwatar da hukuncin babbar kotun tarayya da ya umarci INEC ta soke rajistar ADC da wasu jam’iyyu
- Alkalan kotun sun umarci hukumar INEC da ta jira a kammala sauraron karar da ke gabanta kafin daukar wani mataki kan jam’iyyun
- Kotun ta soki hukuncin da kotun tarayya ta yanke, tana mai bayyana shi a matsayin abin da ya sabawa tsarin shari’ar Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Kotun daukaka kara da ke Abuja ta dakatar da aiwatar da hukuncin da wata babbar kotun tarayya ta yanke na umartar INEC ta soke rajistar jam’iyyar ADC da wasu jam’iyyun siyasa hudu.
Kotun ta kuma umarci INEC da kada ta dauki wani mataki kan soke rajistar jam’iyyun har sai an kammala sauraron karar da jam’iyyun suka shigar domin kalubalantar hukuncin.

Source: Twitter
Umarnin kotu na soke rajistar ADC
Hukuncin kotun daukaka kara ya zo ne bayan ADC da sauran jam’iyyun da abin ya shafa sun garzaya kotun domin neman dakatar da aiwatar da hukuncin da aka yanke a kansu, in ji rahoton Daily Trust.
A ranar Litinin ne Mai shari’a Peter Lifu na babbar kotun tarayya ya umarci INEC da ta soke rajistar ADC, Accord (AP) da wasu jam’iyyun siyasa uku.
Kotun ta ce jam’iyyun sun gaza cika wasu sharuddan kundin tsarin mulkin kasa da ake bukata domin ci gaba da kasancewa cikin jerin jam’iyyun siyasa masu rijista.
Hukuncin ya janyo muhawara sosai a fagen siyasar Najeriya saboda tasirin da zai iya yi ga shirye-shiryen zabukan da ke tafe, kamar yadda rahoton Legit Hausa ya nuna.
Kotun daukaka kara ta soki hukuncin
Sai dai, jaridar Punch ta ruwaito cewa kwamitin alkalai uku na kotun daukaka kara ya dakatar da aiwatar da hukuncin babbar kotun.
Alkalan sun bayyana cewa babu bukatar gaggauta daukar matakin soke rajistar jam’iyyun kafin a kammala sauraron karar da ke gaban kotu.

Source: Getty Images
Rahotanni sun nuna cewa kotun ta yi kakkausar suka ga matakin da kotun tarayya ta dauka, tana mai bayyana shi a matsayin abin da ya sabawa tsarin mutunta matakan shari’a na manyan kotuna.
Da wannan hukunci, jam’iyyun da abin ya shafa za su ci gaba da kasancewa cikin tsarin siyasar kasar nan har sai an yanke hukunci na karshe kan rikicin.
Ana sa ran bangarorin da ke karar za su ci gaba da gabatar da hujjojinsu a gaban kotun domin yanke hukunci kan sahihancin umarnin soke rajistar jam’iyyun.
Kotu ta ci tarar ADC, Argebsola
A wani labari, mun ruwaito cewa, kotun tarayya da ke Abuja ta ci tarar ADC da Rauf Aregbesola N1m bayan ta yi watsi da bukatar cire Mai shari’a Peter Lifu.
Mai shari’a ya ce zargin cewa yana nuna son kai ba shi da tushe kuma yunƙuri ne na neman alkalin da zai yi wa masu karar biyayya.
A yayin zaman kotun na ranar Talata, an kuma tafka muhara game da batun soke rajistar jam'iyyar ADC da yadda hakan zai iya shafar hukuncin da aka yi ranar.
Asali: Legit.ng

