'Dalilin da Ya Sa Tikitin Atiku da Amaechi Zai Kifar da Gwamnatin Tinubu a 2027'
- Jam'iyyar ADC mai adawa a Najeriya ta tsayar da Atiku Abubakar da Rotimi Amaechi a matsayin 'yan takararta na shugaban kasa da mataimaki a zaben 2027
- Sakataren yada labarai na ADC na kasa, Bolaji Abdullahi, ya bayyana cewa tikitin Atiku da Amaechi zai iya kifar da Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu
- Bolaji Abdullahi ya bayyana cewa ADC ta yi amanna cewa dukkanin masu neman takarar shugaban kasa a karkashinta za su fi Tinubu tabuka abin kirki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Sakataren yaɗa labarai na jam'iyyar ADC na kasa, Bolaji Abdullahi, ya yi magana kan tikitin Atiku Abubakar da Rotimi Amaechi a zaben 2027.
Bolaji Abdullahi ya yi amanna cewa tikitin takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC wanda ya haɗa da Atiku Abubakar da Rotimi Amaechi zai doke Shugaba Bola Tinubu a babban zaɓen shekarar 2027.

Kara karanta wannan
"Muna kira ga fannin shari'a"; Atiku ya dauki zafi kan umarnin kotu na soke rajistar ADC

Source: Twitter
Sakataren yada labaran na ADC ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a shirin Politics Today na Channels tv a ranar Litinin, 15 ga watan Yunin 2026.
Me ADC ta ce kan tikitin Atiku, Amaechi?
Bolaji Abdullahi ya ce jam'iyyar ta yi amanna cewa kowane ɗaya daga cikin masu neman takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashinta zai samar da shugabanci mafi kyau fiye da gwamnati mai ci yanzu.
Kakakin na ADC ya bayyana haɗakar Atiku da Amaechi a matsayin ƙwaƙƙwarar tawagar da ke da ikon lashe zaɓen 2027.
“Mun yi amanna cewa duk wanda ya tsaya takara a dandalin ADC, ko Atiku ne ko Rotimi Amaechi ko Mohammed Hayatu-Deen, zai yi rawar gani fiye da yadda Shugaba Bola Tinubu yake yi."
“Mun yi amanna cewa samar da Atiku Abubakar da Rotimi Amaechi a matsayin ɗan takararmu na shugaban ƙasa da mataimakinsa ya ba mu ƙwaƙƙwarar tawagar da ke da kyakkyawar damar lashe wannan zaɓe."
"Don haka ba mu yi mamakin irin dabarun shirin maƙarƙashiya da suka fara ɓulla ba muna sanar da Rotimi Amaechi a matsayin ɗan takararmu na mataimakin shugaban ƙasa."
- Bolaji Abdullahi

Source: Facebook
ADC za ta shiga zaben 2027?
A cewar Bolaji Abdullahi, jam'iyyar ADC “za ta kasance a cikin takardar ƙuri'a a babban zaɓen 2027” kuma nan ba da jimawa ba za ta gudanar da wani babban taro domin gabatar da tikitin takararta na shugaban ƙasa ga 'yan Najeriya a hukumance.
Amaechi, ya fafata a zaɓen fitar da gwani na shugaban ƙasa na ADC, ya sha kaye a hannun Atiku kafin daga bisani aka sanar da shi a matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam'iyyar.
Martanin Atiku kan hukuncin soke rajistar ADC
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya kausasa harshe kan umarnin kotu na soke rajistar jam'iyyar ADC.
Atiku Abubakar ya yi Allah-wadai da hukuncin da ke neman soke rajistar ADC da wasu jam'iyyun siyasa na adawa da dama.
'Dan takarar shugaban kasar ya bayyana hukuncin a matsayin babban karan tsaye ga tsarin mulki na dimokuradiyya da kuma wani shiri da aka tsara don rage karfin adawa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
