Kotu Ta Yi Fatali da Bukatar Sadiya Umar Farouq a Shari'arta da Hukumar EFCC
- Tsohuwar Ministar jin kai, Sadiya Umar Farouq, ta gabatar da bukata a gaban kotu bayan an ba da umarnin a cafke ta
- Alkalin kotun ya yi fatali da bukatar da tsohuwar Ministar ta gabatar inda take neman a soke umarnin cafke ta da aka ba da
- Ya bayyana cewa tsohuwar Ministar ta gaza kawo kwakkwaran dalilin da zai iya hanata bayyana a gaban kotu kan shari'ar da ake yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Apo Abuja, ta yi watsi da buƙatar da tsohuwar Ministar jin kai, Sadiya Umar-Farouq, ta shigar
Kotun ta yi watsi da bukatar da Sadiya Umar-Farouq ta shigar tana neman soke sammacin kama ta da kotun ta bayar.

Source: Facebook
Alkalin kotun, Jude Onwuegbuzie, ne ya yanke hukuncin a ranar Litinin, 15 ga watan Yunin 2026, kamar yadda hukumar EFCC ta bayyana a shafinta na X.
Alkali ya yi watsi da bukatar Sadiya Farouk
Mai shari'a Jude Onwuegbuzie ya bayyana cewa tsohuwar ministar ta gaza bayyana a gaban kotun ba tare da wani ƙwaƙƙwaran dalili ba.
Sadiya Umar-Farouq tana shari'a ne da hukumar EFCC tare da Bashir Nura Alkali da Sani Nafiu Mohammed, bisa zargin haɗa baki wajen aikata laifuffuka, da kuma karkatar da kuɗaɗen gwamnati da suka kai dala miliyan 1.3 da Naira miliyan 746.7.
“Wadda ake ƙara, wadda ta sani sarai cewa wannan shari'a ce ta laifuffuka, ta gaza bayyana a kotu da gangan ba tare da wani ƙwaƙƙwaran dalili ba, kuma doka ta ba kotu iko, lokacin da aka tabbatar cewa wanda ake ƙara bai zo kotu ba tare da dalili mai ma'ana ba, da ta bayar da sammacin kama shi."
“Babu wani abu a cikin hujjojin da ke bayyana dalilin da ya sa wadda ake ƙara, wadda ke ɗauke da ciwon arthritis kawai da cutar zuciya, ba za ta iya bayyana a gaban kotu ba."
“Shin babu asibitoci ne a Najeriya? Na gamsu cewa wadda ake ƙara tana ƙoƙarin ɓoye gaskiya ne ta hanyar kawo abin da ba gaskiya ba ne."
- Jude Onwuegbuzie

Source: Twitter
Bukatar Sadiya ba ta samu karbuwa ba
Mai shari'a Onwuegbuzie ya ce buƙatar ba ta da wani amfani, saboda haka ya ƙi soke sammacin kama ta ɗin.
Bayan yanke hukuncin, Rotimi Jacobs, lauyan hukumar EFCC, ya buƙaci kotun da ta tilasta aiwatar da alkwarin da lauyan tsohuwar ministar, A.A. Ibrahim, ya yi na cewa zai kawo wadda yake karewa a gaban kotun.
EFCC na neman Sadiya Umar Farouq
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar EFCC ta ayyana neman tsohuwar Ministar jin kai, Sadiya Umar Farouq, ruwa a jallo.
Hukumar EFCC ta buƙaci duk wanda ke da bayanai kan inda tsohuwar ministar take da ya tuntubi ofisoshinta da ke kusa da shi a faɗin ƙasar nan ko ta lambobin waya.
Tsohuwar ministar dai ta yi aiki a gwamnatin tsohon shugaban kasa, marigayi Muhammadu Buhari daga shekarar 2019 zuwa 2023.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

