Manyan Labarai A Yau
Jami’ar Jihar Abia ta dakatar da Farfesa Nnamdi Nwaeze kan wani rubutun Facebook da ya yi ikirarin cewa farfesoshi a jami’ar suna samun kasa da N400,000 a wata.
Mataimakin Shugaban Amurka JD Vance ya ce manufofin Amurka a yakin da Iran sun ta’allaka ne kan makamashi da hana Tehran mallakar makamin nukiliya.
Faransa ta gargadi ‘yan kasarta da su guji Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma na Najeriya saboda barazanar hare-haren kungiyoyin jihadi da ake samu.
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APM kuma gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya bukaci 'yan adawa su dunkule waje guda don tunkarar zaben 2027.
Femi Fani-Kayode ya bukaci Sultan da Shugaba Tinubu su gargadi Sheikh Sani Yahaya Jingir kan kalaman da ake danganta masa game da Kiristoci a Najeriya.
Karoline Leavitt ta sanar da cewa za ta bar mukamin sakatariyar yada labaran Fadar White House a karshen Agusta domin mai da hankali ga ‘ya’yanta.
Shugaban masu rinjaye na Majalisar Dokokin Bauchi, Saleh Hodi, ya yi murabus daga kujerarsa domin neman shugabancin Karamar Hukumar Shira a Bauchi.
Shugaban jam'iyyar Peoples Redemption Party (PRP) na kasa, Hakeem Baba-Ahmed, ya ce APC za ta fadi a zaben 2027 idan an gudanar da zabe cikin gaskiya da adalci.
Gwamnan Kebbi Nasir Idris ya amince da kafa sabon gunduma mai kauyuka takwas a Dandi tare da nada sabbin shugabannin gargajiya da za su yi jagoranci.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari