Rashin Tsaro: Gwamna Radda Ya Sanya Labule da Sarakunan Gargajiya a Katsina

Rashin Tsaro: Gwamna Radda Ya Sanya Labule da Sarakunan Gargajiya a Katsina

  • Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya gudanar da wani taro tare da manyan sarakunan gargajiya kan matsalar rashin tsaro
  • Taron ya hada da sarakunan Katsina da Daura tare da Hakimai da Dagatai daga sassa daban-daban na jihar domin tattauna muhimman batutuwa
  • Gwamna Radda ya nuna muhimmancin da sarakunan gargajiya suke da shi wajen tabbatar da dorewar zaman lafiya a cikin al'umma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya gana da sarakunan gargajiya kan matsalar rashin tsaro.

Gwamna Radda ya jaddada muhimmancin sarakunan gargajiya wajen haɓaka zaman lafiya, tsaro, da kuma ci gaban al'ummomin mazauna karkara a faɗin jihar.

Gwamna Radda ya gana da sarakunan gargajiya
Gwamna Dikko Umaru Radda tare da wasu masu rike da sarauta a wurin taron da suka yi Hoto: Ibrahima Kaulaha Mohammed
Source: Facebook

Gwamna Radda ya bayyana hakan ne yayin wani taron da ya yi da sarakunan gargajiya a ranar Alhamis, 18 ga watan Yunin 2026, kamar yadda sakataren yada labaransa, Ibrahima Kaulaha Mohammed ya sanya a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Dakarun gandun daji: Tinubu amince a dauki sababbin ma'aikata 1,000 a Katsina

Gwamna Radda ya gana da sarakunan gargajiya

Taron ya gudana tsakaninsa da Mai Martaba Sarkin Katsina, HRH Abdulmumini Usman; da Mai Martaba Sarkin Daura, HRH Umar Farouq Umar; tare da haɗin gwiwar Hakimai da Dagatai daga sassa daban-daban na jihar.

Taron wanda aka gudanar zauren taro na Ggdan gwamnati da ke Katsina, yana daga cikin ƙoƙarin da gwamnatin ke yi na zurfafa alaƙa da shugabannin gargajiya tare da ƙarfafa matakan da suka ginu a kan al'umma domin gudanar da mulki, tsaro, da kuma ci gaba mai dorewa a faɗin jihar Katsina.

A kan me Radda da sarakuna suka tattauna?

Ganawar ta fi mayar da hankali ne a kan muhimman batutuwan da suka shafi shugabanci, ci gaban al'umma, da kuma tsaro, tare da ba da fifiko na musamman wajen ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin jihar da sarakunan gargajiya.

Gwamna Radda ya lura cewa sarakunan gargajiya sun kasance abokan haɗin gwiwa masu mahimmanci wajen dorewar zaman lafiya, haɓaka haɗin kai, da kuma tallafa wa manufofi da shirye-shiryen gwamnati a matakin karkara.

Kara karanta wannan

Ran shugaban gwamnonin Arewa ya baci kan surutu babu aiki, ya kawo mafita

Ya jaddada buƙatar ci gaba da haɗin gwiwa domin tunkarar ƙalubalen tsaro da kuma hanzarta kawo ci gaba a cikin al'ummomi daban-daban.

Sarakunan gargajiya sun gana da Gwamna Dikko Radda
Sarkin Katsina, Abdulmumin Kabir Usman da Sarkin Daura, Umar Farouq Umar a wurin taron Hoto: Ibrahima Kaulaha Mohammed
Source: Facebook

Manyan jami'an gwamnati sun halarci taron

Taron ya haɗa manyan jami'an gwamnati, ciki har da Shugaban Majalisar dokokin jihar Katsina, Nasir Daura, babban alƙalin jihar Katsina, Musa Abubakar.

Sauran sun hada da shugaban ma'aikatan fadar gwamnati, Abdulkadir Nasir; sakatare na musamman ga gwamna, Abdullahi Turaji da sauran mambobin majalisar zartarwa ta jihar Katsina.

Yusuf Ahmad da ke zaune a Katsina, ya bayyana cewa yana da kyau a rika tattaunawa da iyayen kasa kan matsalar rashin tsaro.

"Sarakunan sune mutanen da ke tare da al'umma a koda yaushe. A ganina suna da rawar da za su taka wajen magance rashin tsaro."
"Muna rokon dai Allah ya kawo mana karshen wannan bala'in."

- Yusuf Ahmad

'Yan bindiga sun kashe dan kasuwa a Katsina

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga sun yi aika-aika a jihar Katsina ta hanyar hallaka wani fitaccen dan kasuwa kuma manomi, mai suna Bala Sanin Kawo.

Kara karanta wannan

Tsaro: An kafa zafafan dokoki a Katsina, an hana POS, cajin waya da sauransu

Majiyoyi sun nuna cewa yan ta'addan sun kashe mutumin ne kwanaki kaɗan bayan sun yi garkuwa da shi a ƙaramar hukumar Dandume ta jihar Katsina.

Iyalan mamacin sun tattara kuɗin fansar da aka bukata tare da miƙa su kamar yadda masu garkuwar suka umarta, amma bayan an kai kuɗin sai maharan suka fadi wurin da suka ajiye gawarsa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng