An Yi Babban Rashi: Tsohon Mataimakin Gwamna, Katagum Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

An Yi Babban Rashi: Tsohon Mataimakin Gwamna, Katagum Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • An tabbatar da rasuwar tsohon gwamnan jihar Bauchi kuma wazirin Katagum, Arch. Audu Sule Katagum a safiyar yau Asabar, 20 ga Yuni, 2026
  • Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed ya mika sakon ta'aziyya ga iyalan marigayin, tare da addu'ar Allah Ya masa rahama
  • Ya bayyana marigayi Wazirin Katagum a matsayin shugaba kuma tsayayyen dattijo, wanda rashinsa babban gibi ne ga jihar Bauchi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Bauchi, Nigeria - Tsohon mataimakin gwamnan jihar Bauchi, Arch. Audu Sule Katagum, ya riga mu gidan gaskiya yana da shekaru 69 a duniya.

Katagum, wanda ya rike mukamin mataimakin gwamna tsakanin 2018 zuwa 2019 a gwamnatin tsohon gwamna Mohammed Abdullahi Abubakar, ya rasu ne da safiyar ranar Asabar.

Audu Sule Katagum.
Tsohon mataimakin gwamnan jihar Bauchi, Audu Sule Katagum Hoto: Senator Bala Muhammad Abdulkadir
Source: Facebook

Tsohon mataimakin gwamnan Bauchi ya rasu

Leadership ta ce Shamsuddeen Lukman Abubakar, mai ba tsohon gwamna Mohammed Abdullahi Abubakar shawara kan harkokin yada labarai, shi ne ya sanar da rasuwar a wata sanarwa.

Kara karanta wannan

Jerin gwamnonin jihar Ekiti daga 1999 zuwa yau yayin da ake shirin sabon zabe a 2026

Ya ce:

"Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un. Cikin alhini da jimami muke sanar da rasuwar Arch. Audu Sule Katagum, Wazirin Katagum kuma tsohon mataimakin gwamnan Jihar Bauchi."

Ya kara da cewa marigayin ya rasu ne bayan rayuwar da ya sadaukar wajen yi wa al'ummarsa, Jihar Bauchi da kasa baki daya hidima.

Mukaman da ya Audu Katagum ya rike

Kafin nadinsa a matsayin mataimakin gwamna, marigayin ya taba rike mukamin shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin Jihar Bauchi.

Baya ga harkokin siyasa, Audu Sule Katagum ya kasance basarake wanda ke rike da sarautar Wazirin Katagum.

Audu Sule ɗa ne ga Alhaji Sule Katagum ne, fitaccen dattijon kasa wanda ya kasance shugaban farko na Hukumar Kula da Ayyukan Ma'aikatan Gwamnatin Tarayya ta Najeriya.

Gwamna Bala ya mika sakon ta'aziyya

Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya mika sakon ta'aziyya ga iyalan marigayin, tare da addu'ar Allah Ya masa rahama.

A wata sanarwa da ya wallafa a Facebook, Gwamna Bala ya ce,:

Kara karanta wannan

Mutuwar Janar Rabe ya taba tsofaffin sojoji da abokansa, sun kawo mafita

"Innalillahi wa Inna Ilaihi Rajiun, tare da fawwala komai ga Allah, muka wayi gari da rasuwar jigo, shugaba kuma tsayayyen dattijo, kwararren ma'aikacin gwamnati, tsohon mataimakin gwamnan jiharmu ta Bauchi, Alhaji Audu Sule Katagum (Wazirin Katagum).
"Rashin jajirtacce irin Waziri, zai haifar da giɓi me zurfi a zukatanmu al'ummar jihar Bauchi la'akari da irin gudunmawar da yake bayarwa wajen ciyar da jiha gaba ba tare da la'akari da bambancin jam'iyya ko siyasa ba.
A madadin ni kai na, iyali, gwamnati da ɗaukacin al'ummar jihar Bauchi, ina miƙa saƙon ta'aziyya ga iyalan marigayin, masarauta da al'ummar ƙasar Katagum, tare da addu'ar Allah ya gafarta masa Ya kyautata bayan sa."
Gwamna Bala.
Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed a gidan gwamnatinsa Hoto: @SenBalaMohammed
Source: Twitter

DCP Khan Salihu ya kwanta dama

A wani rahoton, kun ji cewa Mataimakin kwamishinan rundunar yan sanda na jihar Legas, DCP Khan Salihu ya riga mu gidan gaskiya.

Majiyoyi daga hedikwatar rundunar yan sanda sun bayyana cewa bayan marigayin ya dawo daga masallaci a ranar Lahadi, ya nuna alamun gajiya.

Sai dai bayanan da aka tattaro sun nuna cewa an garzaya da shi asibiti bayan koma gida, inda likitoci suka tabbatar da rasuwarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262