Battujo: Kotu Ta Yanke wa Mahaifiyar Kasurgumin Dan Bindiga da 'Yar'uwarsa Hukunci
- Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke wa mata biyu hukuncin zaman gidan yari na shekaru 40 bisa kama su da laifin taimakawa ta'addanci
- Rahoto ya nuna cewa matan biyu sun hada da mahaifiya da ’yar’uwar Kachallah Ibrahim Battujo, wani fitaccen ɗan ta’adda da aka kashe
- Matan sun amsa laifuffukan taimakawa ayyukan ta’addanci da boye bayanan da za su taimaka wajen cafke dan ta'addan tun yana raye
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke wa mata biyu da Hukumar Tsaro ta DSS ta kama bisa zargin hannu a ayyukan ta’addanci hukuncin zaman gidan yari na shekaru 40.
Matan da aka samu da laifin su ne Safiya Salihu da Halima Abdullahi, mahaifiya da ’yar’uwar Kachallah Ibrahim Battujo, wani shugaban dabar ’yan ta’adda da jami’an tsaro suka kashe a ranar 10 ga Yuni, 2026 a jihar Kogi.

Source: Twitter
Tashar TVC News ta rahoto cewa mai shari’a Hauwa Joseph Yilwa ce ta yanke hukuncin bayan matan sun amsa laifuffuka uku daga cikin tuhume-tuhume biyar aka shigar a kansu.
Laifuffukan matan suka amsa a kotu
Matan sun amsa laifi kan taimakawa da ba da bayanai ga Battujo ta hanyar tattaunawar waya, wanda ya saba da Sashe na 26 na Dokar Hana da Yakar Ta’addanci ta 2022.
Baya ga haka, Safiya Salihu ta amsa laifin boye bayanan da suka shafi ayyukan dan ta’addan, yayin da Halima Abdullahi ta amsa laifin boye bayanan da za su taimaka wajen cafke shi.
Sai dai kotun tarayya ta wanke su daga tuhume-tuhume biyu da suka shafi karbar N490,300 daga Battujo da kuma samun tallafin zuwa aikin Hajji da kudaden da ake zargin sun fito daga ayyukan ta’addanci.
Lauyan gwamnati, Oyedepo Rotimi SAN, ne ya bukaci kotun ta soke wadannan tuhume-tuhume biyu.
Yadda kotu ta yanke hukuncin
Kotu ta bayyana cewa hukuncin kowanne daga cikin laifukan da suka amsa shekaru 20 ne a gidan yari, kamar yadda jaridar Guardian ta tattaro.
Sai dai Mai shari’a Hauwa'u Yilwa ta umarci a tafiyar da hukuncin lokaci guda, wanda hakan ke nufin za su yi shekaru 20 ne kacal a gidan yari maimakon tara hukuncin.
Bayan kammala zaman yarin, kotun ta umarci a saka su cikin shirin gyaran hali da tarbiyya.

Source: Getty Images
Kachallah Ibrahim Battujo ya kasance daya daga cikin fitattun shugabannin ’yan bindiga da hukumomin tsaro ke nema kafin a kashe shi a wani samame da aka kai a Jihar Kogi a watan Yuni, 2026.
Kotu ta daure Halima Umar a kurkuku
A wani rahoton, kun ji cewa kotu ta yanke wa wata mata, Halima Umar hukuncin daurin shekaru 20 a gidan gyaran hali bisa mallakar tarin makamai ba bisa ka'ida ba.
Wacce aka yankewa hukuncin ta amsa laifuffuka biyu daga cikinNtuhume-tuhume hudu da Hukumar Tsaro ta DSS ta shigar a kanta.
Tun farko dai hukumar tsaro ta DSS ta gurfanar da Halima Umar a gaban kotu ne a ranar 11 ga Maris, 2026 bayan kama ta da makamai da ake zargin za ta kai wa 'yan bindiga a jihar Filato.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

