Maharazu Tsiga: Tsohon Janar da 'Yan Bindiga Suka Taba Sacewa Ya Ba da Shawara kan Tsaro

Maharazu Tsiga: Tsohon Janar da 'Yan Bindiga Suka Taba Sacewa Ya Ba da Shawara kan Tsaro

  • Tsohon shugaban hukumar NYSC , Birgediya Janar Maharazu (mai ritaya), ya yi tsokaci kan matsalar 'yan bindiga da ake fama da ita
  • Janar Tsiga wanda ya taba fadawa komar 'yan bindiga ya bayyana cewa hatsabiban mutanen suna tsoron mutuwa kamar kowa
  • Ya bayyana cewa sulhu ba zai sanya 'yan bindiga su daina ayyukansu, inda ya bukaci a dauki matakan da suka dace

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kaduna - Tsohon shugaban hukumar NYSC, Birgediya Janar Maharazu Tsiga (mai ritaya), ya yi magana kan matsalar rashin tsaro.

Birgideya Janar Maharazu Tsiga ya yi kira da a ɗauki ƙwararan matakai domin tunkarar matsalar rashin tsaro.

Maharazu Tsiga ya yi magana kan 'yan bindiga
Tsohon shugaban hukumar NYSC, Birgediya Janar Maharazu Tsiga (mai ritaya) Hoto: Abdullahi Rabo Tsiga
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ce yi waɗannan kalaman ne ranar Alhamis, 18 ga watan Yunin 2026 a Kaduna yayin da yake amsa tambayoyi a wurin taron manema labarai da abokan aiki, abokai na Manjo Janar Abubakar Rabe (mai ritaya) suka shirya.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sama da 100 sun kai hari a Plateau, an kashe jami'an tsaro

Me Janar Tsiga ya ce kan 'yan bindiga?

Yayin da yake tsokaci kan rashin tsaro da sulhu da 'yan bindiga, ya bayyana tsaro a matsayin nauyin da ya rataya a wuyan kowa, sannan ya sanya alamar tambaya kan ingancin tattaunawa da ƙungiyoyin masu laifi ba tare da an rushe babban rukunin da ke ba su goyon baya ba.

Yayin da yake kafa hujja da abubuwan da suka faru da shi lokacin da yake tsare a hannun masu garkuwa, Tsiga ya ce ƙungiyoyin 'yan ta'adda da na 'yan bindiga ba su da alamun za su ajiye makamai da kansu ta hanyar sulhu.

Wace shawara ya ba da kan 'yan bindiga?

A cewarsa, ana buƙatar tsari mai ƙarfi da haɗin gwiwa domin tarwatsa ayyukansu da kuma dawo da zaman lafiya.

“Waɗannan mutane ne kamar mu; suna tsoron mutuwa kuma suna tsoron fuskantar juna. Idan muka cire wannan tsoron ta hanyar ɗaukar ƙwararan matakai da fuskantarsu gaba-da-gaba, za mu samu sakamako mafi inganci fiye da batun sulhu marasa ƙarewa."

Kara karanta wannan

An bukaci Shugaba Tinubu ya ayyana wani shirin watanni 6 don magance matsalolin Najeriya

- Birgediya Janar Maharazu Tsiga

Tsiga ya kuma yi magana kan rawar da masu ba da bayanai da abokan haɗin gwiwa ke takawa waɗanda ake zargi suna ba da tallafi ga ƙungiyoyin masu laifi, inda ya lura cewa wasu suna gudanar da ayyukansu a cikin mutane da kuma hukumomin gwamnati.

“Su wa muke tattaunawa da su da gaske? Kana iya yin sulhu da 'yan bindiga, amma waɗanda ke ba su kayayyaki da kuma cin riba daga rikicin ba za su bari zaman lafiya ya dore ba domin sun fi sha'awar samun kuɗi fiye da rayuka da dukiyoyin 'yan ƙasa marasa laifi."

- Birgediya Janar Maharazu Tsiga

Janar Tsiga ya yi magana kan rashin tsaro
Birgediya Janar Maharazu Tsiga (mai ritaya) Hoto: Abdullahi Rabo Tsiga
Source: Facebook

Ya ce sojoji kadai ba za su iya ba

A cewarsa, ayyukan soja kaɗai ba za su yi nasara ba tare da haɗin gwiwar jama'a da kuma musayar bayanan sirri ba.

“Idan har sojoji suna yin nasu ɓangaren amma al'umma ta gaza tallafa wa waɗannan ƙoƙari, to dukkanmu mun gaza. Tsaro nauyinmu ne baki ɗaya."

Kara karanta wannan

'Zabe ne a gabansa': Yan majalisa sun dura kan Tinubu game da tsaron ƙasa

- Birgediya Janar Maharazu Tsiga

'Yan bindiga sun kashe jami'an tsaro a Plateau

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga dauke da makamai sun hallaka jami'an tsaro na 'yan sa-kai a wani hari a jihar Plateau.

'Yan bindigan waɗanda aka ce yawansu ya haura mutane 100, sun kashe 'yan sa-kai biyu bayan sun farmaki ƙauyen Rangarasa da ke yankin Rantya.

Majiyoyi sun bayyana cewa maharan sun zo ne a kan babura kuma suka buɗe wuta ba ƙauƙautawa yayin da suke ƙoƙarin shiga cikin garin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng