Matasa Za Su Warwasa, An Bude Damar Tallafa wa Mutane 50,000 a Jihohin Najeriya
- Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da shirin Tinubu Light Initiative domin samar da wutar lantarki mai tsafta ga kananan yan kasuwa miliyan ɗaya
- Shirin na da burin ƙirƙira tare da sama wa yan Najeriya 50,000 ayyukan yi tare da rage kuɗin gudanar da kasuwanci
- An kuma ƙaddamar da shirin NextGen Innovation Challenge 2026 domin tallafa wa masu ƙirkire-ƙirkire a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da Tinubu Light Initiative (TLI), wani shiri na samar da makamashin lantarki mai tsafta a faɗin ƙasa.
Shirin na da nufin Oyebanji samar da wutar lantarki mai araha ga ƙananan, matsakaita da ƙananan masana'antu (MSMEs) akalla miliyan ɗaya.

Source: Facebook
Jaridar Tribune Nigeria ta ruwaito cewa an ƙaddamar da shirin ne tare da NextGen Innovation Challenge 2026, shirin tallafawa mutane masu fasahar kirkire a Abuja.

Kara karanta wannan
Trump ya rattaba hannu kan dokokin da za su kawo cikas ga 'yan Najeriya da wasu kasashe
Ministan Ƙirkire-ƙirkire, Kimiyya da Fasaha, Dakta Kingsley Tochukwu Udeh, wanda Sakatare na Dindindin a ma'aikatar, Dakta Mukhtar Yawale Muhammad, ya wakilta, ne ya jagoranci kaddamar da shirye-shiryen.
Ya bayyana cewa shirye-shiryen za su taimaka wajen mayar da sababbin dabaru zuwa kasuwanci tare da bunƙasa masana'antu ƙarƙashin Ajandar Renewed Hope ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Yadda shirin zai samar da ayyuka 50,000
Muhammad ya ce Tinubu shirin Light Initiative zai samar da makamashi mai araha ga kananan yan kasuwa miliyan ɗaya, rage kuɗin gudanar da kasuwanci, ƙarfafa haɗa mutane cikin harkokin kuɗi da kuma inganta tattalin arziki mai ɗorewa.
A cewarsa, ana sa ran wannan shiri zai samar da ayyukan yi kai tsaye sama da 50,000, ga yan Najeriya tare da rage farashin gudanar da kasuwanci.
A cewarsa:
"Idan muka samar wa 'yan kasuwa makamashi mai tsafta da araha, ba wai muna kunna fitilu kawai ba ne, muna kunna kasuwanci, masana'antu da tattalin arzikin Najeriya."
NextGen Innovation Challenge ya samu karɓuwa
Darakta Janar na hukumar National Board for Technology Incubation (NBTI), Dakta Kazeem Kolawole Raji, ya ce shirin ya samar da gagarumar nasara tun daga farkon ƙaddamar da shi.
Ya bayyana cewa wani daga cikin mahalarta shirin ya samu alkawarin jarin fam miliyan 1.5, yayin da wasu sababbin fasahohin noma suka fara inganta amfanin gona a jihohin Kaduna da Bauchi.

Source: Twitter
Raji ya ce shirin na shekarar 2026 ya samu dubban masu neman shiga daga fannoni daban-daban da suka haɗa da fasahar AI, makamashi mai tsafta, ilimin halittu, lafiya, masana'antu, ilimi, fintech da fasahar sauyin yanayi.
An bude shafin tallafin N50,000 a Najeriya
Rahoto ya zo cewa gwamnatin tarayya ta hannun hukumar SMEDAN ta sake bude shirin ba da tallafin N50,000 ga kananan 'yan kasuwa a Najeriya.
An tsara tallafin ne domin taimaka wa kananan 'yan kasuwa wajen inganta harkokinsu, fadada kasuwanci da kuma samar da karin guraben ayyukan yi.
A cewar SMEDAN, shirin zai kuma taimaka wajen bunkasa harkokin kasuwanci , kara yawan masu sana'o'i da habaka tattalin arziki a matakin kananan hukumomi.
Asali: Legit.ng
