"Mutanenmu ne": Gwamna Okpebholo Ya Fadi Masu Haddasa Rashin Tsaro a Edo

"Mutanenmu ne": Gwamna Okpebholo Ya Fadi Masu Haddasa Rashin Tsaro a Edo

  • Gwamnan jihar Edo, Sanata Monday Okpebholo, ya yi tsokaci kan matsalar rashin tsaro da ta ki ci ta ki cinyewa a sassa daban kasar nan
  • Monday Okpebholo ya yi zargin cewa akwai mutanen da ke zuwa suna dauko hayar miyagu domin su aikata munanan abubuwa a jihar
  • Gwamnan ya nuna cewa wasu da yawa daga cikin rahotannn rashin tsaro da ake yadawa a shafukan sada zumunta ba gaskiya ba ne

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Edo - Gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo, ya yi magana kan matsalar rashin tsaron da ake fama da ita.

Gwamna Okpebholo ya yi zargin cewa wasu mazauna jihar Edo suna zuwa wani sashe na Najeriya domin ɗauko hayar miyagu don gudanar da garkuwa da mutane, fashi da makami, da sauran manyan laifuffuka a jihar.

Kara karanta wannan

Rana ta 3: Masu zanga zanga sun toshe titi mai muhimmanci a Abuja kan matsalar tsaro

Monday Okpebholo ya yi magana kan rashin tsaro
Gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo, na jawabi a wajen taro Hoto: Senator Monday Okpebholo
Source: Twitter

Okpebholo ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga mahalarta taron malaman majami'a na shekarar 2026, wanda kungiyar kiristoci ta Najeriya (CAN) reshen jihar Edo ta shirya ranar Laraba, 17 ga watan Yunin 2026 a birnin Benin, cewar rahoton Premium Times.

Me Okpebholo ya ce kan rashin tsaro?

A cewar Gwamna Okpebholo, taron an yi shi ne domin tattaunawa kan rashin tsaro a Edo da ma Najeriya baki ɗaya, jaridar The Punch ta kawo rahoton.

Ya bayyana cewa galibin rahotannin da ake yaɗawa a shafukan sada zumunta game da rashin tsaro na ƙanzon kurege ne.

Gwamnan ya ce ya samu rahoton wani lamari da ya faru a kan hanyar Sapele, inda ya umarci jami'an tsaro da su gaggauta zuwa yankin, sai dai daga baya aka gano cewa rahoton ba gaskiya ba ne.

Okphebolo ya ce ana dauko hayar miyagu

“Mutanenmu a yanzu suna ɗauko hayar miyagu domin taya su yin aikin, za su yi garkuwa da mutum sannan su miƙa shi ga mutanen da ke cikin daji."

Kara karanta wannan

"Talauci da jahilci sun yi kamari a Arewa": Sarki Sanusi II ya ba da mafita

“Gobe za ku gan su suna tuka tsada-tsadan motoci, suna gina gidaje, ta yaya suke samun waɗannan abubuwan? Za su shaida muku cewa su 'yan Yahoo (masu damfarar intanet) ne."
“Su ne kaza, su ne kaza, idan kuka ji cewa mun kama wani, kada ku zo kuna yi mini magiyar na sake shi."
“Wasu rahotannin kan rashin tsaro an shirya su ne kawai domin katsalandan ga wannan gwamnati, a ba wannan gwamnati mummunan suna, amma ba wai babu rashin tsaro ba ne, maganganun ƙarya na fargaba wata matsala ce ta daban a wannan ƙasa."

- Gwamna Monday Okpebholo

Gwamna Okpebholo ya yi magana kan rashin tsaro
Gwamna Monday Okpebholo na jihar Edo Hoto: Senator Monday Okpebholo
Source: Facebook

Gwamnan ya ce akwai dakarun sa-kai waɗanda a yanzu haka aka tura su cikin dazuzzuka domin tabbatar da cewa miyagu ba su samu gurbi ko wurin zama a jihar Edo ba.

Okpebholo ya kare Shugaba Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo, ya bayyana cewa akwai makarkashiyar da ake yi wa Shugaba Bola Tinubu.

Gwamna Monday Okpebholo ya yi zargin cewa wasu mutane na karawa rashin tsaro karfi domin karkatar da hankalin Shugaba Bola Tinubu.

Ya ce rashin tsaro ya karu kwatsam a kasar nan, yana mai zargin cewa ana shirya hakan ne domin bata shugabancin Shugaba Bola Tinubu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng