"Bai da Kwarewa": Babban Sanata a Amurka Ya Soki Trump saboda Yarjejeniyar Iran
- Ana ci gaba da muhawara kan yarjejeniyar fahimtar juna da aka cimma tsakanin Amurka da Iran domin kawo karshen yaki
- Shugaban marasa rinjaye na Majalisar dattawan Amurka, Chuck Schumer, ya ragargaji Shugaba Donald Trump kan yarjejeniyar
- Chuck Schumer ya bayyana cewa rashin kwarewar Trump da rashin son gaskiyarsa sun jefa Amurka a cikin wani yanayi mai muni
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Washington, Amurka - Babban sanatan jam'iyyar Democratic ta Amurka, Chuck Schumer, ya soki ‘rashin kwarewar’ Shugaba Donald Trump.
Chuck Schumer wanda shi ne shugaban marasa rinjaye na jam'iyyar Democratic a Majalisar dattawan, ya ce Shugaba Trump ya jefa Amurka cikin wani yanayi mafi muni.

Source: Getty Images
Chuck Schumer ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na X a ranar Alhamis, 18 ga watan Yunin 2026.
Chuck Schumer ya ragargaji Donald Trump
Shugaban marasa rinjayen ya bayyana cewa rashin kwarewar Trump da girman kansa sun sanya Amurka cikin matsala.
"Amurka ta tsinci kanta a cikin mafi munin yanayi saboda rashin kwarewar Trump, da girman kansa, da kuma rashin iyawarsa na sauraron gaskiya.”
- Chuck Schumer
Sanatan ya yi kaca-kaca da Trump
Chuck Schumer ya kuma soki abin da ya kira shirin Trump na tura daruruwan daloli ga Iran domin sake gina kasar.
“Idan Trump yana son aika daruruwan biliyoyin daloli zuwa Iran, zai bukaci yin hakan ne da kuri'un 'yan jam'iyyar Republican."
"Yan jam’iyyar Democratic ba za su taya Trump aika dala biliyan 300 zuwa Iran ba.”
- Chuck Schumer
Ana sukar yarjejeniyar Amurka da Iran
Masu sukar yarjejeniyar fahimtar juna da aka cimma tsakanin Washington da Tehran sun zargi Trump da amincewa ya bai wa Iran dala biliyan 300 domin taimakawa wajen sake gina abubuwan more rayuwa na ƙasar da kuma farfado da tattalin arzikinta da ke cikin wani yanayi.
Sai dai, Trump da sauran manyan jami'an Amurka sun bayyana cewa ƙasar ba za ta bai wa Iran kowane irin kuɗi ba, tashar Aljazeera ta kawo rahoton.
Sun bayyana cewa maƙwabtan Tehran, da ma sauran ƙasashen da ke son shiga ciki, su ne za su iya samar da kuɗaɗen.
Wasu mambobin jam'iyyar Republican a majalisa, musamman masu ra'ayin rikau (masu son zafafa al'amura) a cikinsu, sun kafa hujjar cewa an bai wa Iran rangwame mai yawa a cikin wannan yarjejeniya ta fahimtar juna.
Sun yi nuni musamman da janye takunkumin da aka sanya wa jigilar man fetur na Iran nan take a matsayin misali na yadda gwamnatin ta nuna sassauci da rauni sosai ga Iran.

Source: Twitter
Gwamnatin Trump ta yi martani
Gwamnatin ta mayar da martani da cewa tana ƙoƙarin yin abin da ya fi dacewa ne ga Amurka, kuma hakika tana yin abin da ya fi dacewa ga Amurkan.
Hakazalika, mataimakin shugaban ƙasa, JD Vance, ya bayyana cewa babu ko taro guda na kuɗin Amurka da zai tafi Iran a ƙarƙashin wannan sasanci.
Trump ya amince Iran ta mallaki makamai
A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya amince Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta mallaki makamai masu linzami da ke cin dogon zango.
Trump ya bayyana cewa ya kamata a bai wa Iran damar ci gaba da mallakar wasu makamai domin kare kanta daga barazana.
Shugaban kasar na Amurka ya bayyana cewa zai zama rashin adalci a hana Iran mallakar makaman idan har wasu kasashe suna da su.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


