Janar Abdulsalam Ya Sanya Yada Labaran Karya cikin Abu 2 da Ke Rura Wutar Rashin Tsaro a Najeriya
- Tsohon shugaban kasa a mulkin soja, Janar Abdulsalami Abubakar, ya yi magana kan matsalar rashin tsaron da ke ci gaba da addabar Najeriya
- Janar Abdulsalami Abubakar ya bayyana cewa farfagandar siyasa na taimakawa wajen rura wutar matsalar rashin tsaro
- Tsohon shugaban kasar ya bukaci 'yan Najeriya da su tashi tsaye wajen ba da ta su gudunmawar domin kawo karshen matsalar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar, ya yi magana kan matslaar tsaro da ake fama da ita a Najeriya.
Janar Abdulsalam ya ce farfagandar siyasa da labaran kanzon kurege a shafukan sada zumunta suna ƙara ba wa ƙungiyoyin 'yan ta'adda ƙarfin gwiwa tare da ruruta wutar rashin tsaro a Najeriya.

Source: Twitter
Jaridar TheCable ta ce Janar Abdulsalami ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da aka fitar lokacin bikin cikarsa shekaru 84 da haihuwa.
Me Abdulsalami ya ce kan rashin tsaro?
Tsohon shugaban mulkin sojan ya yi duba ga yanayin da ƙasar take ciki tare da yin kira ga ƙarin haɗin kan ƙasa baki ɗaya a yaƙi da rashin tsaro.
Ya ce mutuwar Janar Rabe Abubakar kwanan nan da sauran mutane da dama da suka fada komar rashin tsaro ya kamata ta zama silar faɗakarwa ga Najeriya.
Janar Abdulsalami ya ƙara da cewa ko da yake rundunonin soji da sauran hukumomin tsaro sun kasance masu jajircewa a yaƙi da ta'addanci, to amma yaƙi da rashin tsaro yana buƙatar haɗin gwiwar 'yan ƙasa baki ɗaya.
“Ya fito fili cewa nasarar cimma wannan buri dole ne ta haɗa da kowa. Rundunonin sojoji da sauran dukkan hukumomin tsaro sun nuna bajinta sosai a yaƙi da ta'addanci. Amma wannan ba yaƙinsu ba ne su kaɗai."
"Kowane ɗan ƙasa yana da rabo a ciki, kuma roƙona ne ga 'yan Najeriya da su haɗa kai domin yaƙar ta'addanci.”

Kara karanta wannan
Maharazu Tsiga: Tsohon janar da 'yan bindiga suka taba sacewa ya ba da shawara kan tsaro
- Janar Abdulsalam Abubakar
Wadanne abubuwa ke rura rashin tsaro?
Tsohon shugaban ya nuna bacin ransa game da abin da ya siffanta da ƙaruwar mayar da batutuwan tsaro su zama na siyasa, jaridar Daily Trust ta kawo rahoton.
“A tsawon shekaru, mayar da al'amuran tsaro su zama na siyasa ya ruruta lamarin, kuma wannan shi ne ya kawo mu inda muke a yau."
“Mu haɗa ƙarfi da ƙarfe da gwamnati da hukumomin tsaro a kowane mataki domin lallasa waɗannan miyagu, waɗanda ba su san ƙabila, addini, jam'iyyar siyasa, rayuwar al'umma ko wasu siffofi na daban na tantance mutum ba."
“Yaɗa manufofin ƙarya domin siyasa ko sauran muradun son kai yana ƙara bai wa ƙungiyoyin 'yan ta'adda gurbin numfashi."
"Yin amfani da labaran ƙarya a shafukan sada zumunta domin yaɗa karairayi ya taimaka wajen ƙarfafa gwiwar 'yan ta'adda da sauran rukunonin masu laifi."
“Nasarar ƙungiyar ta'addanci guda ɗaya tana ƙarfafa gwiwar wata daban, kuma idan har ba mu sake tunani ba, za mu ci gaba da ruruta wannan rikici.”
- Janar Abdulsalami Abubakar

Source: Twitter
Shawarar Abdulsalami ga 'yan Najeriya
Ya kuma yi kira ga 'yan Najeriya da su kasance masu bin doka da oda tare da yin taka-tsantsan.
“Najeriya ita ce ƙasa ɗaya tilo da muke da ita. Na shiga aikin soja ne domin na kare ta da rayuwata. Ni mai cikakken gaskatawa ne a kan dunkulalliyar Najeriya mai zaman lafiya."
- Janar Abdulsalami Abubakar
Shawarar da Abdulsalami ya ba Obasanjo
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban kasa a mulkin soja, Janar Abdulsalami Abubakar, ya bayyana shawarar da ya ba Olusegun Obasanjo.
Abdulsalami ya bayyana cewa bayan sakin Obasanjo daga gidan yari a 1998, ya ba shi shawarar ya hakura da kudirin tsayawa takarar shugaban kasa.
Ya ce ya gaya wa Obasanjo kai tsaye cewa ya koma gida ya gode wa Allah da yake raye bayan wahalhalun da ya sha, sannan ya manta da batun neman shugabancin kasa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

