'Yan Sanda Sun Hallaka Hatsabibin Jagoran 'Yan Bindiga a Kebbi

'Yan Sanda Sun Hallaka Hatsabibin Jagoran 'Yan Bindiga a Kebbi

  • Rundunar 'yan sandan jihar Kebbi ta samu gagarumar nasara a yakin da ta ke yi da 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane domin samar da tsaro
  • Jami'an rundunar tare da hadin gwiwa sauran hukumomin tsaro sun samu nasarar hallaka wani jagoran 'yan bindiga da ke garkuwa da mutane
  • A cewar sanarwar da 'yan sanda suka fitar, jagoran 'yan bindigan ya addabi mutanen da ke kauyuka takwas na karamar hukumar Bagudo ta jihar Kebbi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kebbi - Rundunar 'yan sandan jihar Kebbi, tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro, ta kashe wani da ake zargi shugaban 'yan bindiga masu garkuwa da mutane ne mai suna Jiji Mujugu.

Jami'an rundunar 'yan sandan sun kashe shi ne lokacin wani samame da aka gudanar a karamar hukumar Bagudo ta jihar.

Kara karanta wannan

Matasan 'yan takara 4 a zaben gwamnan jihar Ekiti na shekarar 2026

'Yan bindiga sun shiga hannun 'yan sanda a Kebbi
Taswirar jihar Kebbi, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Jaridar Daily Trust ta ce kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kebbi, SP Bashir Usman, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Asabar, 20 ga watan Yunin 2026.

Yadda 'yan sanda suka kashe jagoran 'yan bindiga

Kakakin rundunar 'yan sandan ya ce ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin da aka kama tun da fari shi ne ya jagoranci jami'an tsaro zuwa maboyar shugaban ƙungiyar.

A cewarsa, Mujugu, yayin da yake ƙoƙarin tserewa, ya buɗe wa jami'an wuta, inda su kuma suka mayar da martani tare da hallaka shi.

Kakakin 'yan sandan ya ce an kama wani mamba na ƙungiyar, Bube Tukur, a maboyar lokacin artabun da aka yi, jaridar Leadership ta kawo rahoton.

Sun addabi mutanen waau kauyuka

Ya ce bincike ya nuna cewa shugaban ƙungiyar da aka kashe da kuma wanda aka kaman sun kasance mambobin wata ƙungiyar mutane takwas da suka daɗe suna tsoratar da al'ummomi da dama a yankin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sama da 100 sun kai hari a Plateau, an kashe jami'an tsaro

Bashir Usman ya lissafa al'ummomin da lamarin ya shafa da suka haɗa da Geza, Adawa, Matsinkai, Sharabi, Illela, Suru, da Dakin Gari a karamar hukumar Bagudo da kewayenta.

An ceto wani mutum a hannunsu

Ya ƙara da cewa ƙungiyar ce ke da alhakin yin garkuwa da wani mazaunin yankin, Alhaji Abu Geza, daga kauyen Geza.

“A lokacin samamen, an kwato wata bindigar tafi-da-gidanka da aka kera ta cikin gida da alburusai daga hannun mamban ƙungiyar, yayin da aka ceto wanda aka yi garkuwar da shi, Alhaji Abu Geza, daga maboyar waɗanda ake zargin."

- SP Bashir Usman

'Yan bindiga sun kashe jagoran 'yan bindiga a Kebbi
Shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya, Olatunji Rilwan Disu Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

'Yan bindiga sun kashe jami'an tsaro

A wani labarin kuma, kun ji cewa hatsabiban 'yan bindiga dauke da miyagun makamai sun kashe akalla mambobin ƙungiyar tsaro ta 'yan sa-kai guda biyu a jihar Plateau.

'Yan bindigan waɗanda aka ce yawansu ya haura mutane 100, sun farmaki ƙauyen Rangarasa da ke yankin Rantya, a karamar hukumar Jos ta Kudu a jihar Plateau.

Majiyoyi sun bayyana cewa jami'an tsaron sa-kai sun haɗa kai da nufin tunkurar maharan, amma ƙarfin makaman 'yan bindigar ya fi ƙarfinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng