'Yan Bindiga Sama da 100 Sun Kai Hari a Plateau, an Kashe Jami'an Tsaro
- 'Yan bindiga masu yawa da ke tafiya a kan babura dauke da makamai sun kai wani sabon hari a jihar Plateau da ke yankin Arewa ta Tsakiya
- Hatsabiban 'yan bindigan sun farmaki wani gari a karamar hukumar Jos ta Kudu inda suka yi artabu da jami'an tsaro
- 'Yan bindigan sun hallaka wasu jami'an tsaro biyu yayin artabun da aka yi, ciki har da wanda matarsa ba ta dade da haihuwa ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Plateau - 'Yan bindiga dauke da makamai sun kashe akalla mambobin ƙungiyar tsaro ta 'yan sa-kai guda biyu a jihar Plateau.
'Yan bindigan waɗanda aka ce yawansu ya haura mutane 100, sun farmaki ƙauyen Rangarasa da ke yankin Rantya, a karamar hukumar Jos ta Kudu a jihar Plateau.

Source: Facebook
Jaridar Vanguard ta ce wani mazaunin yankin, John Mancha, wanda ya shaida harin, ya bayyana hakan ga manema labarai a Jos ranar Alhamis, 18 ga watan Yunin 2026.
'Yan bindiga sun kai hari a Plateau
Ya bayyana cewa maharan sun zo ne a kan babura kuma suka buɗe wuta ba ƙauƙautawa yayin da suke ƙoƙarin shiga cikin garin ta hanyar yankin Rangarasa, a daren ranar Laraba, 17 ga watan Yunin 2026.
A cewarsa, maharan sun zo ne cikin manyan rukunoni, inda mutane uku zuwa huɗu ɗauke da makamai ke kan kowane babur guda, Jayfm ta kawo rahoton a Facebook.
“Jiya da daddare a Rantya, ba mu yi barci ba. Mun ga maharan. Sun zo ne a kan babura. A kan kowane babur, akwai mutane uku ko huɗu ɗauke da manyan bindigogi."
"Sun yi ta harbe-harbe tare da ƙoƙarin shiga garin Rantya ta hanyar yankin Rangarasa da ke da iyaka da wurin."
- John Mancha
'Yan sa-kai sun yi artabu da 'yan bindiga
Mancha ya bayyana cewa jami'an tsaron sa-kai sun haɗa kai da nufin tunkurar maharan, amma ƙarfin makaman 'yan bindigar ya fi ƙarfinsu.
“Wasu jami'an sa-kai sun haɗa kansu kuma a gaskiya sun yi iya ƙoƙarinsu wajen tunkurar maharan. Abin takaici, an harbe biyu daga cikinsu kafin maharan su tsere."
- John Mancha
An bayyana sunayen mamatan jami'an sa-kan da Joshua da Emmanuel. Mancha ya ce Joshua ya bar 'ya'ya huɗu, yayin da matar Emmanuel kuma ta haihu kwanan nan ta hanyar tiyata.

Source: Original
Ya koka da cewa jami'an tsaro sun ziyarci garin ne kawai a safiyar ranar Alhamis bayan faruwar lamarin.
'Yan bindiga sun sace mutane a Sokoto
A wani labarin kuma, kun ji cewa hatsabiban 'yan bindiga sun kai munanan hare-hare a ƙananan hukumomin Sabon Birni da Wurno a jihar Sokoto.
'Yan ta'addan sun kashe mutane biyu tare da yin garkuwa da wasu 17, ciki har da matan aure da yara ƙanana a yayin munanan hare-haren da suka kai.
A yayin hare-haren, maharan sun kashe wani mutum mai suna Nazifi Lauwali Kamtsa, sannan suka harbi wani mutumi a ƙafa.
Asali: Legit.ng

