Ta Faru Ta Kare: APC Ta Ɗora Sunayen Yan Takarar Gwamna da Mataimakansu a Shafin INEC

Ta Faru Ta Kare: APC Ta Ɗora Sunayen Yan Takarar Gwamna da Mataimakansu a Shafin INEC

  • Jam'iyyar APC ta kammala loda sunayen dukkan ‘yan takararta na gwamnoni, mataimakan gwamnoni da majalisun jihohi a shafin INEC
  • Jam’iyyar ta ce ta loda sunayen ‘yan takarar gwamnoni da mataimakan gwamnoni 56 da na majalisun jihohi 1,015
  • Shugaban APC, Nentawe Yilwatda, ya ce nasarar ta nuna karfin tsari da shirye-shiryen jam’iyyar gabanin zaben 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Jam'iyyar APC ta kammala shigar da sunayen dukkan ‘yan takararta na gwamna, mataimakin gwamna da Majalisun Dokokin Jihohi na zaben 2027 a shafin Hukumar Zabe ta Kasa (INEC).

Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda ne ya bayyana hakan, inda ya ce hakan ya nuna shirin da suke yi gabanin babban zabe mai zuwa.

Shugaban APC.
Shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda a ofishinsa da ke hedkwatar jam'iyya mai mulki a Abuja Hoto: @OfficialAPCNIG
Source: Facebook

Yilwatda ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X ranar Juma’a, inda ya taya shugabannin jam’iyyar, mambobi da ‘yan takara murnar kammala aikin tantancewa da gabatar da sunayen ‘yan takara.

Kara karanta wannan

Rarara ya kira ruwa, PDP ta yi masa tatas kan taba Farfesa Pantami

Hakan ya sa jam’iyya mai mulki ta kammala aikin kafin wa’adin ranar Asabar, 8 ga Agusta, 2026, da INEC ta kayyade domin jam’iyyun siyasa su miƙa sunayen ‘yan takararsu da sauran bayanan da suka dace.

APC ta ce ta samu nasara 100%

Da yake bayar da karin bayani kan aikin, Yilwatda ya ce APC ta samu nasarar loda kashi 100 cikin 100 na sunayen ‘yan takararta a fadin Najeriya.

Ya ce an shigar da sunayen ‘yan takarar gwamna da mataimakan gwamna 56 da kuma ‘yan takarar majalisun dokokin jihohi 1,015 a shafin INEC na tantance ‘yan takara.

“Ina taya shugabanninmu, mambobi da ‘yan takara a fadin kasar nan murnar kammala aikin gabatar da sunayen ‘yan takara na zaben 2027.
“Ina farin cikin sanar da cewa jam’iyyar APC ta samu nasara 100% na tura sunayen ‘yan takarar gwamna da mataimakan gwamna 56 da kuma ‘yan takarar Majalisun Dokokin Jihohi 1,015 a shafin INEC na tantance ‘yan takara,” in ji Yilwatda.

Kara karanta wannan

APC: Dan majalisar tarayya ya rasa tikitin takara, kotu ta sauya sunansa da wani

Tutar APC.
Tutar jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya Hoto: APC Nigeria
Source: Twitter

Yilwatda ya ce APC a shirye take

Shugaban APC ya ce kammala aikin cikin nasara ya nuna cewa jam’iyyar a shirye take domin shiga mataki na gaba na shirin babban zaben 2027.

Ya bayyana nasarar a matsayin wata alama da ke nuna karfin tsari da tsarin gudanarwa na jam’iyyar.

Yilwatda ya ce bayan kammala aikin shigar da sunayen ‘yan takara, APC za ta mayar da hankali wajen tuntubar ‘yan Najeriya da kuma gabatar musu da manufofinta gabanin zaben 2027.

An maka APC a kotu kan tikitin 2027

A baya, kun ji cewa wani babban jigon APC, Alhaji Bayero Lawal, ya tayar da rigima ta hanyar maka jam’iyyarsa kotu kan batun takarar shugaban kasa a zaben 2027.

Bayero Lawal ya kai kara kotu ne bisa zargin APC da hana shi sayen fom din nuna sha’awa da na tsayawa takarar shugaban kasa a zaben fidda gwani da aka gudanar kwanakin baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262