Hashim: Dan Takarar Shugaban Kasa a Najeriya Ya Yi Magana kan Yarjejeniyar Amurka, Iran
- Kasashen Amurka da Iran sun rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna domin kawo karshen yakin da ake yi a yankin Gabas ta Tsakiya
- Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Accord a zaben 2027, Gbenga Olawepo-Hashim ya tofa albarkin bakinsa kan yarjejeniyar da kasashen biyu suka cimma
- Gbenga Olawepo Hashim ya yabawa gwamnatoci da abokan hulda na kasa da kasa wadanda suka taimaka wajen ganin an cimma yarjejeniyar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Dakar, Senegal - Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Accord a zaben 2027, Gbenga Olawepo-Hashim, ya yi magana kan yarjejeniyar da aka kulla tsakanin Amurka da Iran.
Gbenga Olawepo-Hashim ya yi maraba da yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Amurka da Iran domin kawo ƙarshen yaki da kuma dawo da daidaito a yankin Gabas Ta Tsakiya.

Source: Facebook
Jaridar The Nation ta kawo rahoton cewa ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a lokacin wata takaitacciyar ziyara a birnin Dakar na ƙasar Senegal.
Me Hashim ya ce kan yarjejeniyar Amurka, Iran?
Hashim ya yaba wa gwamnatoci da abokan haɗin gwiwa na ƙasa da ƙasa waɗanda ƙoƙarinsu na diflomasiyya ya taimaka wajen samar da yanayi na tattaunawa da kuma sasanta takaddama cikin lumana, jaridar Vanguard ta kawo labarin.
“Ina mai maraba da yarjejeniyar tsakanin Amurka da Iran da nufin kawo ƙarshen rikici da kuma dawo da daidaito a Gabas Ta Tsakiya."
“Ina jinjinawa Shugaba Donald Trump, gwamnatocin ƙasashen Iran, Qatar, da Pakistan, tare da sauran abokan haɗin gwiwa na ƙasa da ƙasa waɗanda ƙoƙarinsu ya taimaka wajen samar da sharuddan zaman lafiya."
- Gbenga Olawepo-Hashim
Ya yaba kan diflomasiyya
Hashim ya lura cewa diflomasiyya ta sake nuna darajarta a matsayin mafi ingancin makami na warware rikitattun takaddamar ƙasa da ƙasa a daidai lokacin da ake fuskantar rashin tabbas a duniya.
A cewarsa, daidaito a yankin Gabas Ta Tsakiya yana da tasiri mai nisa da ya wuce yankin kaɗai, inda yake shafar tsaron duniya, kasuwannin makamashi, kasuwancin ƙasa da ƙasa, kwararar zuba jari, da kuma bunƙasar tattalin arziki.

Source: Facebook
Amfanin da Najeriya da Afrika za su samu
Ɗan takarar shugaban ƙasar na jam'iyyar Accord ya jaddada cewa Najeriya da sauran ƙasashe a faɗin Afirka suna da babban rabo a cikin tsarin ƙasa da ƙasa mai dorewa da zaman lafiya.
Ya buƙaci ƙasashe da su ci gaba da tallafa wa tsare-tsaren da ke haɓaka tattaunawa, haɗin gwiwa, da kuma fahimtar juna a matsayin hanyoyin samun zaman lafiya mai dorewa.
Trump ya zagi masu sukar yarjejeniya da Iran
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi martani mai zafi kan masu sukarsa saboda yarjejeniyar da ya kulla da Iran.
Shugaba Trump ya kira masu sukarsa da ke ganin bai matsawa Iran sosai ba a matsayin 'yan hassada, miyagun mutane kuma wawaye.
Trump ya kare kansa ta hanyar nuna irin tagomashin da aka samu a kasuwar hannun jarin Amurka da faduwar farashin danyen man fetur sakamakon cimma yarjejeniyar.
Asali: Legit.ng

