Matasan 'Yan Takara 4 a Zaben Gwamnan Jihar Ekiti na Shekarar 2026
- An samu 'yan takarar gwamna guda huɗu masu shekaru tsakanin 35 zuwa 38 a zaɓen jihar Ekiti, lamarin da ke nuna ƙaruwar shigar matasa cikin harkokin siyasar jihar
- Hakan ya nuna tasirin dokar "Not Too Young To Run" wadda ta rage adadin shekaru ga masu neman muƙaman siyasa
- Matasan masu fafutukar sun gudanar da kamfen ɗinsu a kan batutuwan da suka haɗa da haɓakar tattalin arziki, lafiya, ilimi, noma, walwalar jama'a da kuma sanya matasa a fagen jagoranci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Ekiti - Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) za ta gudanar da zaben gwamnan jihar Ekiti, a ranar 20 ga Yuni, 2026.
Daga cikin 'yan takarar da ke neman kujerar gwamnan jihar Ekiti, akwai wasu matasa da suka fito domin gwada sa'arsu.

Source: Facebook
Legit Hausa ta tattaro 'yan takara hudu a zaben gwamnan jihar Ekiti wadanda suka kasance matasa masu kananan shekaru.
Matasan 'yan takara a zaben gwamnan Ekiti
A baya, fagen siyasa a al'adance ya kasance filin wasa da tsofaffin 'yan siyasa suka mamaye, a yanzi matasa sun fara yunkurin shiga domin a dama da su.
Yayin da Ekiti ke shirin fita zaɓe a ƙarshen mako, matasa huɗu masu karsashi da buri waɗanda shekarunsu ba su kai 40 ba sun shiga takara domin fafatawa a zaben.
Matasan sun nuna a shirye suke su ƙalubalanci tsohon tsari kuma su nemi babbar kujera a jihar Ekiti da ke yankin Kudu maso Yamma.
Ga jerinsu nan kasa:
1. Abegunde Abayomi Blessing (NNPP) - Shekaru: 35
A daidai shekaru 35 kacal da haihuwa, Abegunde Abayomi Blessing na jam'iyyar NNPP ya kasance ɗan takara mafi ƙarancin shekaru a zaben gwamnan jihar Ekiti, kamar yadda bayanai daga shafin INEC suka nuna.

Source: Facebook
Kamfen ɗinsa ya ginu ne kacokan a kan gaskiya, gyare-gyare na zamani, da kuma sanya matasa kai tsaye cikin harkoki.
2. Akande Oluwasegun Samuel (AAC) - Shekaru: 36
'Dan takara na biyu mafi karancin shekaru a zaben shi ne Akande Oluwasegun Samuel mai shekaru 36 na jam'iyyar AAC.

Source: Facebook
Akande Oluwasegun Samuel ya kasance daya daga cikin matasan 'yan takarar da za su fafata a zaben gwamnan jihar Ekiti.
Takararsa ta nuna shirin jam'iyyar AAC na ba matasa dama domin a rika damawa da su a cikin harkokin siyasa Daily Trust ta kawo rahoton.
Tushen siyasarsa ya ginu ne kacokan a kan walwalar al'umma, fafutukar haƙƙin ɗan adam, da kuma farfado da aikin gwamna.
3. Awogbemi Bidemi Olaiya (APP)- Shekaru: 36
Awogbemi Bidemi Olaiya, shi ne ɗan takarar jam'iyyar Action People’s Party (APP) a zaben gwamnan jihar Ekiti.
Awogbemi mai shekaru 36 a duniya ya kasance daya daga cikin 'yan takara matasa a zaben gwamnan na jihar Ekiti.
Legit ta wallafa cewa takarar Awogbemi ta nuna kokarin da kananan jam'iyyu suke yi domin kalubalantar manyan jam'iyyu a siyasar jihar Ekiti.

Kara karanta wannan
Bincike: 'Yan bindiga ne suka mika gawar Janar Rabe hannu da hannu? Gaskiya ta fito
Manufa ta mayar da hankali sosai a kan faɗaɗa ƙananan masana'antu da matsakaita (SMEs) da kuma magance karancin abubuwan more rayuwa a jihar.
4. Adetunji Victor Damilola (ZLP) - Shekaru: 38
Wanda ke cikon wannan rukunin matasa huɗu shi ne Adetunji Victor Damilola mai shekaru 38, wanda ke wakiltar jam'iyyar Zenith Labour Party (ZLP).
Adetunji Victor Damilola ya shiga cikin sahun matasa masu neman mukaman siyasa a jihar Ekiti, rahoton ICIR ya nuna hakan.
Manufofinsa sun mayar da hankali ne a kan tsarin kiwon lafiya mai sauƙi, inganta tsarin ilimi, da kuma mayar da Ekiti ta zama matattarar yawon buɗe ido.
INEC ta cire sunan dan takarar PDP
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta fitar da sunayen 'yan takarar da za su fafata a zaben gwamnan jihar Ekiti.
Sai dai, ba a ga sunan dan takarar jam'iyyar PDP a cikin sunayen da INEC ta fitar don zaben na ranar Asabar, 20 ga watan Yunin 2026.
Jerin sunayen ya ƙunshi ’yan takara daga jam’iyyun siyasa 12 da ke shirin gwabza wa domin neman kujerar gwamna da mataimakinsa a jihar Ekiti.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

