Manyan Labarai A Yau
James Faleke ya musanta zargin Davido na cewa ya matsa wa hukumar INEC lamba kan sakamakon zaben Osun, inda ya ce ya je jihar ne domin tallafa wa APC.
Mawakin Afrobeats Davido ya yi murnar sake zaben kawunsa Ademola Adeleke a matsayin gwamnan Osun, bayan hukumar zabe ta INEC ta tabbatar da nasarar.
Gwamna Ademola Adeleke ya gode wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bayan sake zabensa a jihar Osun, yana yabawa shugaban kasar kan tabbatar da dimokuradiyya.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana Kano a matsayin “karamar Najeriya” saboda yawan jama’a da bambancin al’ummarta, yana cewa mulkinta ba abu ne mai sauki ba.
Ademola Adeleke na Accord Party ya lashe kananan hukumomi 19 cikin 30 a zaben Osun, inda ya samu kuri’u 511,067 kan 444,815 na jam'iyyar APC mai adawa.
Samaila Abdu Sulaiman ya waiwayi talakawan mazabarsa, ya yi rabon miliyoyin kudi ga mata da dattawa. Dujjiman Zazzau ya kashe miliyoyin daf da za a fara kamfe.
Dino Melaye ya ce dukiyarsa ta fito ne daga kiwon akuya, inda ta haihu har ya samu kudin biyan kudin makarantarsa, sannan ya zuba sauran kudin a harkar hannun jari.
Jihar Osun na da dadadden tarihi tun bayan kafuwarta a shekarar 1991. Za a gudanar da zaben gwamna karo na takwas a jihar a ranar Asabar, 15 ga watan Agustan 2026.
Dino Melaye ya zargi tsofaffin shugabannin PDP uku da sayar da jam’iyyar ga Bolabinubu, kafin Wike ya kara dagula rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari