Wata Sabuwa: Trump Ya Sake Barazanar Kai Hari Mai Zafi a Iran duk da Fara Tattaunawa

Wata Sabuwa: Trump Ya Sake Barazanar Kai Hari Mai Zafi a Iran duk da Fara Tattaunawa

  • Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi barazanar kai hari a Jamhuriyar Musulunci ta Iran duk da fara tattaunawa
  • Barazanar Shugaba Trump na zuwa ne yayin da wakilan kasashen Amurka da Iran suka fara tattaunawa a kasar Switzerland
  • Tattaunawar dai na zuwa ne bayan kasashen biyu sun rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna domin kawo karshen yakin da ake yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Birnin Washington, Amurka - Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi barazanar kai hari mai zafi kan ƙasar Iran.

Shugaba Trump ya yi barazanar ne kam idan har ba ta dakatar da ƙungiyar Hezbollah daga “janyo matsala” ba.

Trump ya yi sabuwar barazana ga Iran
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump a wajen taron G7 Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Shugaban kasar na Amurka ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na Truth Social a ranar Lahadi, 21 ga watan Yunin 2026.

Kara karanta wannan

Tayin da Amurka ta yi wa Iran bayan fara tattaunawa a Switzerland

Barazanar Trump na zuwa ne a daidai lokacin da aka fara tattaunawar zaman lafiya tsakanin manyan jami'an Amurka da na Iran a ƙasar Switzerland.

An buɗe tattaunawar ne a tsakiyar takaddama da artabu a kwanakin nan tsakanin sojojin Isra'ila da ƙungiyar Hezbollah, wata ƙungiyar kawance da Tehran a Kudancin Lebanon.

Lamarin da ke barazana ga ruguza yarjejeniyar zaman lafiya ta farko tsakanin Tehran da Washington.

Wace bazazana Trump ya yi ga Iran?

“Dole ne Iran ta dakatar da 'yan amshin shatanta da ake biya da tsabar kuɗi masu yawa a Lebanon nan take daga janyo matsala."
“Idan ba su yi ba, za mu sake kai hari Iran da ƙarfi sosai, daidai kamar yadda muka yi a makon jiya, sai dai wannan karon zai yi zafi fiye da haka!!!”

- Shugaba Donald Trump

Haren-haren sama na Isra'ila sun kashe aƙalla mutane 30 a ranar Asabar a gabashi da kudancin Lebanon, kafin a sami ɗan lafawa a fadan a ranar da yamma, lokacin da aka ba wa sojojin Isra'ila umarnin dakatar da arangama da Hezbollah.

Kara karanta wannan

An dage ci gaba da tattaunawar Iran da Amurka.duk da sanya hannu kan yarjejeniya

Yarjejeniyar fahimtar juna da aka sanya wa hannu a ranar Laraba, 17 ga watan Yunin 2026 tsakanin Amurka da Iran ta tanadi tsagaita buɗe wuta a dukkan fagen fama, har da ƙasar Lebanon.

Trump ya yi barazana ga kasar Iran
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump Hoto: Donald J Trump
Source: Facebook

Yadda tattaunawar ke gudana

The Punch ta ce a farkon tattaunawar a Switzerland ranar Lahadi, 21 ga watan Yunin 2026, mataimakin shugaban Amurka JD Vance ya ce ya ga babban ci gaba a cikin kwanaki biyu da suka gabata wajen tabbatar da cewa an kiyaye tsagaita wutar a Lebanon.

“Dukkanmu muna aiki ne domin samun zaman lafiya a yankin. A gaskiya ina jin daɗin matakin da muke kai a Lebanon. Har yanzu akwai sauran rina a kaba amma za mu ci gaba da aiki a kai.”

- JD Vance

Vance ya jaddada cewa Trump da Amurka sun yi rawar gani fiye da kowace ƙasa a cikin watannin nan wajen dakatar da rikici a Lebanon.

Tayin Amurka ga Iran

A wani labarin kuma, kun ji cewa wakilan Amurka da na Jamhuriyar Musulunci ta Iran sun fara gudanar da tattaunawa a kasar Switzerland.

A yayin tattaunawar, Amurka ta bukaci Iran ta amince da bai wa masu binciken majalisar dinkin duniya damar duba cibiyoyin nukiliyarta.

Idan Iran ta amince da tayin, za a ba ta damar amfani da wani ɓangare na kudaden da aka ƙwace mata, ciki har da dala biliyan 6 da ke kasar Qatar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com