An ga Tashin Hankali da Bam Ya Tarwatse da Sojoji a Sokoto, an Rasa Rayuka

An ga Tashin Hankali da Bam Ya Tarwatse da Sojoji a Sokoto, an Rasa Rayuka

  • An samu asarar rayukan wasu dakarun sojojin Najeriya lokacin da suke kan aikin samar da tsaro a jihar Sokoto da ke yankin Arewa maso Yamma
  • Sojojin sun gamu da tsautsayi ne bayan motarsu ta taka wani bam lokacin da suke kan hanyar kai daukin gaggawa sakamakon harin 'yan bindiga
  • Ana zargin cewa 'yan bindigan ne suka dasa bam din a kan hanyar da sojojin ke wuce a karamar hukumar Isa ta Sokoto

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Sokoto - Akalla sojoji biyu ne aka kashe sannan wasu da dama suka jikkata bayan da wani bam ya fashe a jihar Sokoto.

Bam din ya tashi ne da wata motar soja da ke ɗauke da dakarun sojoji zuwa garin Bargaja da ke karamar hukumar Isa a jihar Sokoto.

Bam ya kashe sojoji a Sokoto
Shugaban rundunar sojojin kasa na Najeriya, Laftanar Janar Waidi Shaibu Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Rahoton jaridar Daily Trust ya nuna cewa dakarun sojojin suna kan hanyarsu ne ta kai ɗauki bayan samun kiran gaggawa sakamakon harin da 'yan bindiga suka kai garin a ranar Asabar, 20 ga watan Yunin 2026.

Kara karanta wannan

Sojoji za su fara shiga daji yaki da 'yan bindiga tare da 'yan jarida

'Yan bindiga sun dasa bam

Mazauna yankin sun bayyana cewa 'yan bindiga sun fada ƙauyen tsakanin ƙarfe 12:30 zuwa ƙarfe 3:00 na dare, inda suka buɗe wuta ba ƙauƙautawa, lamarin da ya tilasta wa mazauna yankin neman ɗaukin sojoji.

Wani mazaunin yankin da ya bukaci a sakaya sunansa ya yi zargin cewa maharan sun dasa bam ɗin ne a kan hanyar Isa zuwa Bargaja kafin isowar dakarun sojojin.

“Suna kan hanyarsu ta zuwa cetonmu ne lokacin da motar ta taka bam ɗin. Sojoji da dama abin ya shafa. Ɗayan sojojin da lamarin ya faru da shi daga baya ya gudu zuwa ƙauyenmu don neman taimako bayan fashewar." Inji shi

Sojoji sun rasu sakamakon harin bam

Mazaunin yankin ya ce lamarin ya faru ne a wani ɓangare na hanyar da ta haɗa Isa da Bargaja, sannan ya nuna damuwa kan abin da ya siffanta da ƙaruwar amfani da bama-bamai da 'yan bindiga ke yi, Premium Times ta kawo labarin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sama da 100 sun kai hari a Plateau, an kashe jami'an tsaro

“Mun ga gawarwakin sojoji biyu, amma ba za mu iya cewa ko akwai ƙarin waɗanda suka mutu ba." Inji shi

An yi wa sojojin Najeriya ta'aziyya

Wani mazaunin yankin daban wanda ya ce ya ziyarci sansanin sojoji da ke garin Isa domin yi wa dakarun ta'aziyya, ya ce sun yi tafiya ne daga Bargaja don nuna alhini ga sojojin sakamakon faruwar lamarin.

“Mun yi hayar motoci guda biyu daga garinmu muka tafi Isa domin yi wa sojoji ta'aziyya kan rashin jami'ansu da suka yi." Inji shi
'Yan bindiga sun dasa bam ga sojoji
Taswirar jihar Sokoto, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Majiyar ta yi zargin cewa sojoji uku, ciki har da direba, ne suka rasa rayukansu a harin, inda ta ƙara da cewa fashewar ta yi mummunar illa ga ɗaya daga cikin mamatan.

Ya ce daga baya aka kwashe gawarwakin jami'an da suka mutun zuwa birnin Sokoto.

Dakarun Sojoji sun kashe 'yan ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa sashen dakarun sama na rundunar Operation Hadin Kai (OPHK) ya kashe mambobin 'yan ta'adda da ba su gaza 27 ba a jihar Borno.

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali da 'yan bindiga suka hallaka basarake a Plateau

Sojojin sun samu nasarar ne a hare-haren sama da suka kai a maboyar 'yan ta'adda a yankin Tumbuns na jihar Borno.

Rundunar sojojin ta ce an kashe 'yan ta'adda 12 a wani harin sama da aka kai a Dawoshe da ke karamar hukumar Kukawa, tare da kashe wasu 15 a Metele.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng