Rarara Ya Zargi Kwankwaso da Jefa Najeriya cikin Halin Kunci, Ya Kawo Dalili

Rarara Ya Zargi Kwankwaso da Jefa Najeriya cikin Halin Kunci, Ya Kawo Dalili

  • Shahararren mawakin siyasa, Dauda Adamu Kahutu Rarara ya zargi madugun Kwankwasiyya da jefa Najeriya cikin halin kunci
  • Rarara ya yi zargin cewa duk wani hali na kunci da ake ciki a kasar nan a yanzu, madugun na Kwankwasiyya ne sila
  • Mawakin ya kafa hujja da cewa matsalolin sun samu asali ne saboda wasu matakai da Kwankwaso ya dauka a lokacin mulkinsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Shahararren mawakin siyasa, Dauda Adamu Kahutu, wanda aka fi sani da Rarara, ya yi zargi kan tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso.

Rarara ya zargi Kwankwaso da laifin bayar da gudunmawa ga wasu daga cikin kalubalen tattalin arziki da na mulki da Najeriya ke fuskanta a halin yanzu.

Rarara ya yi zargi kan Kwankwaso
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a wajen taron NDC Hoto: Hon. Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Rarara ya yi wannan zargin ne a lokacin wata hira da ya yi da wata kafar yada labarai ta intanet, SL Update da aka sanya a Tiktok a ranar Lahadi, 21 ga watan Yunin 2026.

Kara karanta wannan

Jerin gwamnonin jihar Ekiti daga 1999 zuwa yau yayin da ake shirin sabon zabe a 2026

Dauda Rarara ya yi zarge-zarge

Mawakin ya ce yawancin matsalolin da ke damun kasar a yau sun samo asali ne daga manufofi da shawarwari da aka dauka a baya.

A cewarsa, daya daga cikin manyan matsalolin ita ce rike kudaden kananan hukumomi da manyan matakan gwamnati ke yi maimakon barin ciyamomi su gudanar da cikakken ikon sarrafa kudadensu domin gudanar da ayyukan ci gaba ga talakawan karkara.

Wane zargi Rarara ya yi kan Kwankwaso?

"Duk bala'in da ake ciki a Najeriya Kwankwaso ne ya sanya mu. Tun da ya dawo kan mulki ya rike kudin kananan hukumomi. Daga rike kudin kananan hukumomi zuwa yanzu tun daga nan ne Najeriya take cikin bala'i har yanzu ba a fita ba. Kuma shi ya sa mu a wannan."
"Shi ne sila. Ai rike kudin kananan hukumomi ka rike jijiyar wuyan mutane ne. Daga rike kudin kananan hukumomi zuwa yanzu shi ya saka Najeriya cikin wannan bala'in."

- Dauda Kahutu Rarara

Kara karanta wannan

Davido: Malamin Musulunci ya yi wa Rarara wankin babban bargo kan tsaro

Rarara ya ce Kwankwaso ne silar wahala

Mawakin ya kafa hujjar cewa wahalhalun da kasar ke ciki a yau sun fara ne tun lokacin da aka kirkiro wannan dabi'a, inda ya kara da cewa har yanzu ana jin radadin illar hakan a bangarori daban-daban.

Ya yi ikirarin cewa rashin cin gashin kai na kudi ga kananan hukumomi ya jinkirta kokarin samar da ci gaba, musamman a bangarorin ilimi, kiwon lafiya, samar da ruwa, da abubuwan more rayuwa na karkara.

Rarara ya yi zarge-zarge kan Kwanwaso
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Dauda Kahutu Rarara Hoto: Hon. Saifullahi Hassan, Dauda Adamu Kahutu
Source: Facebook

Rarara ya kara da cewa idan har Najeriya tana son samun ci gaba mai dorewa da bunkasar tattalin arziki, dole ne a bai wa kananan hukumomi cikakken iko na gudanar da al'amuransu da kudadensu ba tare da tsoma baki ba.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, Rabiu Musa Kwankwaso da wakilansa ba su mayar da martani ba game da wadannan zarge-zarge.

Muhuyi ya yi zargi kan Kwankwaso

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban hukumar PCACC, Muhuyi Magaji Rimin Gado, ya yi zarge-zarge kan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Kara karanta wannan

Mutuwar Janar Rabe: Kwankwaso ya kai ziyara Katsina, ya bada mafita kan matsalar tsaro

Muhuyi ya zargi dan takarar mataimakin shugaban kasar na NDC, da karkatar da biliyoyin Naira daga kudaden jihar domin amfanin kansa.

Tsohon shugaban hukumar ta PCACC ya kalubalanci Kwankwaso da ya garzaya kotu idan har zarge-zargen da yake yi ba gaskiya ba ne.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng