Peter Obi Ya Bukaci Tinubu Ya Kwaikwayi Starmer wajen Yin Murabus daga Mulki
- Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NDC a zaben, Peter.Obi, ya yi kira da babbar murya ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu
- Peter Obi ya bukaci shugaban kasar da ya yi murabus saboda gaza cika dumbin alkawuran da ya daukarwa 'yan Najeriya
- Dan takarar shugaban kasar ya bukaci hakan ne bayan ganin yadda Firaministan Burtaniya, Keir Starmer, ya yi murabus daga mukaminsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi, ya bukaci Shugaba Bola Tinubu ya yi murabus daga mukaminsa.
Peter Obi ya bukaci hakan ne biyo bayan murabus din da Firaminiatan Burtaniya, Keir Starmer, ya yi daga mukaminsa.

Source: Facebook
Dan takarar shugaban kasar ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na X a ranar Litinin, 22 ga watan Yunin 2026.

Kara karanta wannan
"Firaministan Birtaniya zai yi murabus," Donald Trump ya yi magana kan Keir Starmer
Obi ya yi nazari kan murabus din Keir Starmer
Peter Obi ya ce sauraren bayanin da Keir Starmer ya yi inda yake sanar da murabus dinsa, ya sanya ya yi nazarin abin da ya sa kasashen da suka ci gaba suke yin abubuwa daidai da kuma kalubalen da wasu ke fuskanta wajen gudanar da hakan.
Ya ce shirin murabus din Starmer yana zuwa ne a daidai lokacin da ake samun karuwar bacin ran jama'a game da matsalar tattalin arziki da.kuma gaza cika manyan alkawuran da ya dauka lokacin yakin neman zabe.
Obi ya nuna gazawar Tinubu
"Idan muka kalli cikin gida a kasarmu, za mu iya tunawa da namu yanayin. Kafin shekarar 2015, Shugaban kasarmu a lokuta da dama ya jagoranci kiran da akayi wa Shugaba Goodluck Jonathan na wancan lokacin da ya yi murabus saboda matsin tattalin arziki da rashin tsaro da ke addabar 'yan Najeriya."
"A lokacin da lamarin garkuwa da 'yan matan makarantar Chibok ya faru, ya bukaci da Shugaba Jonathan ya yi murabus cikin gaggawa, inda ya kafa hujjar cewa gwamnati ta gaza a cikin babban aiki mafi muhimmanci na kare rayuka."

Kara karanta wannan
An bukaci Shugaba Tinubu ya ayyana wani shirin watanni 6 don magance matsalolin Najeriya
"A lokacin yakin neman zaben shekarar 2023, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dauki alkawura da dama, ciki har da inganta samar da wutar lantarki."
"Ya kuma kalubalanci masu zabe da kada su sake zabensa a wa'adi na biyu idan har ya gaza cika wadannan alkawura, musamman wajen samar da ingantacciyar wutar lantarki, yaki da cin hanci da rashwa, da kuma inganta jin dadin 'yan Najeriya."
"Sai dai a halin yanzu, wadannan sharudda sun kara tabarbarewa. Samar da wutar lantarki ya kasance abin da ba za a iya dogaro da shi ba, rashin tsaro ya tsananta a yankuna da dama, ciki har da garkuwa da mutane, sannan matsin tattalin arziki ya kara zurfi maimakon ya saukaka."
"Irin wadannan damuwoyi suna bayyana a daukacin sauran bangarori masu muhimmanci kamar su tsaro, abubuwan more rayuwa, sufuri, da kokarin yaki da cin hanci da rashawa, wadanda duka sun koma baya. Muna cikin mafi mummunan yanayi da za a iya fuskanta."
- Peter Obi

Source: Twitter
Meyasa Obi ya ce Tinubu ya yi murabus
Peter Obi ya bayyana cewa ya bi sahun 'yan Najeriya wajen kiran shugaban kasar da ya yi murabus, saboda gaza sauke nauyin da ke kansa.
"Don haka, na bi sahun 'yan Najeriya masu kishin kasa wajen kiran shugaban kasa da ya yi murabus saboda mummunar gazawa a fannin gudanar da mulki."
"Irin wannan mataki zai taimaka wajen kafa tsarin siyasa da ke da tushe a kan daukar alhakki da sauke nauyi, maimakon kara karfafa dabi'ar ci gaba da rashin hukunta laifi"
- Peter Obi
Peter Obi ya shirya sulhu da 'yan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa dan takarar shugaban kasa a zaben 2027, Peter Obi, ya yi magana kan batun sulhu da 'yan bindiga.
Peter Obi na jam'iyyar NDC ya bayyana tsarin da zai bi wajen dawo da zaman lafiya idan aka zabe shi shugaban kasa a 2027
Ya ce gwamnatinsa za ta bude kofar tattaunawa da ’yan bindiga da sauran kungiyoyin masu tada kayar baya da suka shirya rungumar sulhu.
Asali: Legit.ng
