Firaministar Italiya Ta 'Karyata' Trump kan Abin da Ya Ce Ya Faru a Taron G7

Firaministar Italiya Ta 'Karyata' Trump kan Abin da Ya Ce Ya Faru a Taron G7

  • An yi musayar yawu tsakanin Firaministar Italiya, Giorgia Meloni da shugaban kasar Amurka, Donald Trump bayan ya yi wasu kalamai a kanta
  • Giorgia Meloni ta fito ta karyata shugaban kasar na Amurka bayan da ya yi ikirarin cewa ta nemi alfarma a wajensa
  • Firaministan ta Italiya ta bayyana cewa ta kadu matuka da ta ga ikirarin da Trump ya yi, inda ta nuna cewa ba gaskiya cikin abin da ya fada

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Rome, Italiya - Gwamnatin ƙasar Italiya ta yi watsi da iƙirarin da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi na cewa Firaminista Giorgia Meloni ta roke shi.

Trump dai ya yi ikirarin cewa Giorgia Meloni ta roke shi domin su ɗauki hoto tare a lokacin taron ƙasashe masu arziƙi na G7 da aka gudanar kwanan nan a ƙasar Faransa.

Kara karanta wannan

Ekiti: Zaben gwamna ya zo da zafinsa, an kona ofishin yan sanda kurmus

Meloni ta soki Donald Trump
Giorgia Meloni tare da Donald Trump a wajen taro a Egypt Hoto: Evan Vucci
Source: Getty Images

Tashar CNBC ta ce takaddamar ta ɓalle ne a ranar Juma'a, 19 ga watan Yunin 2026 bayan da Trump ya yi waɗannan kalaman a lokacin wata hira da aka yi da shi wadda aka nuna a gidan talabijin na La7.

Trump ya ce Giorgia Meloni ta buƙaci da ya ba ta damar ɗaukar hoto lokacin taron G7 a Evian-les-Bains, sannan ya yi iƙirarin cewa ya amince duk da yake ba lallai ba ne ya yi hakan.

An soki Shugaba Donald Trump

Wannan iƙirari na batun hoto ya janyo martani cikin gaggawa daga jami'an gwamnatin Italiya, inda Ministan harkokin waje Antonio Tajani ya siffanta kalaman da cewa “masu tsanani ne da kuma cin mutunci” ga Meloni da kuma ƙasar Italiya baki ɗaya.

Antonio Tajani ya kuma soke shirin tafiya ƙasar Amurka da ya tsara yi a wannan ƙarshen mako, tashar BBC ta kawo rahoton.

Wane martani Giorgia Meloni ta yi?

Kara karanta wannan

Trump ya yi maganar ci gaba da kai hari Iran duk da cimma yarjejeniya

Yayin da take mayar da martani, Meloni ta yi watsi da bayanan na Trump, inda ta ce ta ji cewa ya zama tilas a kanta ta fito fili ta yi magana kan batun.

“Kalaman Donald Trump ƙirƙararru ne baki ɗayansu. A gaskiya na girgiza. Ban san me yasa shugaban Amurka yake nuna irin wannan ɗabi'a ga abokan kawancensa ba. Sannan kuma, wannan ba shi ne karon farko da hakan ke faruwa ba.”
Meloni ta ce tana mayar da martani ne saboda “wasu abubuwa sun cancanci a ba su amsa nan take.”

- Giorgia Meloni

Meloni ta ragargaji Donald Trump

Firaministar ta Italiya ta kuma soki tsarin da Trump ke amfani da shi ga abokan kawance, inda ta ce:

“Abin da zan iya fada kawai shi ne, abin takaici ne yadda ba ya nuna irin wannan taurin kai ga maƙiyan kasashen Yamma, ga maƙiyan Amurka, ga shugabannin da shi kuma a gefe guda yake sassautawa da lallabawa sosai.”
“Amma akwai abu guda ɗaya da dole ne ya tuna: Italiya da ni ba mu roƙon alfarma ta kaskanci.”
Meloni ta yi wa Trump martani
Shugaba Donald Trump da Giorgia Meloni a wajen taro a kasar Egypt Hoto: Pool
Source: Getty Images

Wannan rashin jituwa yana zuwa ne a daidai lokacin da ake samun ƙaruwar sabani tsakanin Washington da Rome a kan batutuwa da dama na ƙasa da ƙasa.

Kara karanta wannan

2027: Salon Peter Obi ya fita daban, ya bayyana tsare-tsarensa ga Najeriya

Ko da yake a can baya ana kallon Meloni a matsayin ɗaya daga cikin na kusa-kusa da Trump a Turai, alaƙar ta yi tsami saboda rikicin ƙasar Iran, yaƙin Ukraine, harajin Amurka, da kuma tallafin da Amurka ke ba wa Isra'ila a yankin Gaza.

Trump ya caccaki masu sukarsa kan Iran

A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya ragargaji masu sukarsa kan yarjejeniyar da ya kulla da Iran.

Trump ya kira wadanda suke ganin bai matsa lamba ga Jamhuriyar Musulunci ta kan sharuddan yarjejeniyar, da 'yan hassada kuma wawayen mutane.

Yarjejeniyar dai ta sanya wasu suna cewa sharuɗɗan kamar sun ƙarfafa ikon Tehran ne saboda abubuwan da ke kunshe a cikinta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng