Dan Majalisa Ya Rasu a Bauchi Kwana 1 bayan Mutuwar Tsohon Mataimakin Gwamna
- An yi rashi na daya daga cikin 'yan majalisar dokokin jihar Bauchi bayan ya yi fama da 'yar gajeruwar jinyar rashin lafiya
- Dan majalisa mai wakiltar mazabar Sakwa a majalisar dokokin jihar Bauchi, Wanzam Mohammed Zaki, ya yi bankwana da duniya
- Shugaban majalisar dokoki da Gwamnan Bauchi, Sanata Bala Mohammed, sun aika da sakon ta'aziyyarsu kan rasuwar marigayin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Bauchi - Ɗan majalisar dokokin jihar Bauchi mai wakiltar mazabar Sakwa, Hon. Wanzam Mohammed Zaki, ya rasu a Bauchi bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.
Har zuwa lokacin rasuwarsa, Hon Wanzam Mohammed Zaki shi ne shugaban kwamitin majalisar kan kasafin kudi da samar da kudade.

Source: Facebook
An yi ta'aziyyar dan majalisa a Bauchi
Jaridar Daily Trust ta ce kakakin majalisar dokokin jihar, Rt. Hon. Abubakar Y. Sulaiman, ne ya sanar da rasuwarsa a cikin wata sanarwa da kakakin sa, Mukhtar Garba Kobi, ya sanyawa hannu a ranar Lahadi, 21 ga watan Yunin 2026.
Ya bayyana marigayin a matsayin mai yi wa jama'a hidima da sadaukarwa wanda ya yi wa mazabarsa da jihar hidima bisa iya bakin kokarinsa.
"Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un. Cikin bakin ciki da mika wuya ga kaddarar Allah Madaukakin Sarki, ina sanar da rasuwar dan majalisar dokokin jihar Bauchi mai wakiltar mazabar Sakwa, Hon. Mohammad Wanzam."
"An gudanar da sallar jana'izar marigayin a ranar Lahadi, 21 ga watan Yunin 2026 a masallacin Juma'a na Gwallaga da ke Bauchi da misalin karfe 11:00 na safe."
- Hon. Abubakar Y Sulaiman
Kakakin majalisar ya yi addu'ar Allah Ya yafe wa marigayin kurakuransa, yYa karbi ayyukansa na kwarai, kuma Ya sanya shi a Aljannatul Firdausi.
Gwamna Bala ya yi ta'aziyya
Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya bayyana marigayin a matsayin dan majalisa jajirtacce, shugaba mai tawali'u, kuma mai yi wa jama'a hidima, sadaukarwa, wanda rayuwarsa ta kasance mai cike da sauki da jajircewa wajen kulawa da jin dadin mutanen mazabarsa da kuma ci gaban jihar Bauchi.
Ya bayyana hakan ne a cikin sakon ta'aziyyar da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai da hulda da jama'a, Mukhtar Gidado, ya fitar a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan
Jerin gwamnonin jihar Ekiti daga 1999 zuwa yau yayin da ake shirin sabon zabe a 2026
Gwamnan ya lura cewa dan majalisar ya bambanta kansa ta hanyar kwazo, girma, da kishin kasa, musamman a matsayinsa na shugaban kwamitin majalisar kan kasafin kudi da samar da kudade.

Source: UGC
Gwamnan Bauchi ya yi wa marigayin addu'a
Ya yaba da gudunmawarsa wajen tsarawa da sa ido kan manufofi da shirye-shiryen da aka yi niyyar inganta rayuwar jama'a.
Gwamna Bala Mohammed ya yi addu'ar Allah Ya gafarta masa kurakuransa kuma ya ba shi hutu na har abada a Aljannatul Firdausi.
Tsohon mataimakin gwamnan Bauchi ya rasu
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin gwamnan jihar Bauchi, Arch. Audu Sule Katagum, ya riga mu gidan gaskiya.
Audu Sule Katagum, wanda ya rike mukamin mataimakin gwamna tsakanin 2018 zuwa 2019 ya yi bankwana da duniya ne yana da shekara 69.
Baya ga harkokin siyasa, Audu Sule Katagum ya kasance basarake wanda ke rike da sarautar Wazirin Katagum a Bauchi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
