Gwamna Inuwa Ya Gabatar da Dan Takarar Gwamnan APC a Gombe ga Tinubu

Gwamna Inuwa Ya Gabatar da Dan Takarar Gwamnan APC a Gombe ga Tinubu

  • Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya gabatar da dan takarar gwamnan APC ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu
  • Muhammadu Inuwa Yahaya ya gabatar da Dr. Jamilu Isiyaku Gwamna ga Shugaba Bola Tinubu a fadar shugaban kasa da ke Abuja
  • Shugaba Bola Tinubu ya taya dan takarar gwamnan murnar nasarar da ya samu a zaben fitar da gwani na APC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja Najeriya - Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya gabatar da ɗan takarar gwamna na jam'iyyar APC ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

Gwamna Inuwa Yahaya ya gabatar da Dr. Jamilu Isiyaku Gwamna ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu a fadar shugaban kasa da ke birnin tarayya Abuja.

An gabatar da Jamilu Gwamna ga Tinubu
Jamilu Gwamna, Muhammadu Inuwa Yahaya tare da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu Hoto: Ismaila Uba Misilli
Source: Facebook

Kakakin yada labaran Gwamna Inuwa, Ismaila Uba Misilli ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a shafinsa na Facebook ranar Lahadi, 21 ga watan Yunin 2026.

Kara karanta wannan

Siyasar Pantami ta kara karfi a Gombe da tsohon hadimin gwamna ya koma PDP

Wannan gabatarwa ta biyo bayan zaman Dr. Jamilu Gwamna a matsayin ɗan takarar gwamna na APC bayan ya samu nasara a zaɓen fitar da gwani na jam'iyyar APC gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

Me Tinubu ya gayawa Jamilu Gwamna?

A cewar Ismaila Uba Misilli, Shugaba Tinubu, yayin da yake karɓar bakuncin Gwamna Inuwa Yahaya da Dr. Jamilu Gwamna, ya taya ɗan takarar murna kan nasarar da ya samu, sannan ya yaba wa gwamnan saboda misalin jagoranci na gari da yake nuna wa.

Tinubu ya kuma bayyana kwarin gwiwarsa ga shugabancin APC a jihar, inda ya nuna fatan cewa jam'iyyar za ta dore da nasarorin ci gaba da ta samu da kuma daidaiton siyasa a ƙarƙashin tsarin 'Renewed Hope Agenda'

Inuwa ya yabawa Shugaba Tinubu

Yayin da yake jawabi a lokacin taron, Gwamna Inuwa Yahaya ya jinjinawa Shugaba Tinubu saboda samar da jagoranci mai kyau, wanda ke ci gaba da ƙarfafa haɗin kai, daidaiton al'umma, da kuma shugabanci na gari a faɗin ƙasar.

Ya nuna godiyarsa ga shugaban kasar saboda goyon bayan da yake ba wa jihar Gombe ba tare da tangarda ba, musamman a ɓangarorin haɓaka abubuwan more rayuwa, haɓakar tattalin arziki, da kuma manufofin da aka tsara domin tallafa wa ci gaba mai dorewa.

Kara karanta wannan

2026: Tinubu ya yi martani da dan takarar APC ya lashe zaben gwamnan jihar Ekiti

Isiyaku Gwamna ya gana da Shugaba Tinubu
Jamilu Isiyaku Gwamna tare da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu Hoto: Ismaila Uba Misilli
Source: Facebook

Gwamna Inuwa Yahaya ya lura cewa gabatar da Dr. Jamilu Gwamna ga shugaban kasar ba wai kawai alama ce ta haɗin kan jam'iyya da dorewarta ba, har ma nuni ne na shirye-shiryen APC na dorawa kan nasarorin da aka samu a jihar Gombe tsawon shekaru.

Tinubu ya taya Oyebanji murna

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya taya gwamnan jihar Ekiti, Biodun Oyebanji, murnar nasarar sake lashe zabe.

Shugaban kasar ya ce yadda jama’ar jihar suka sake ba Oyebanji dama ya nuna sun amince da salon mulkinsa da ayyukan da gwamnatinsa ta gudanar a wa’adin farko.

Tinubu ya kuma jinjina wa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa kan yadda ta gudanar da zaben da hukumomin tsaro bisa kokarin tabbatar da doka da oda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng