Wata Sabuwa: Barcelona Ta Fasa Buga Wasan Sada Zumunci da Moroko, An Ji Dalili

Wata Sabuwa: Barcelona Ta Fasa Buga Wasan Sada Zumunci da Moroko, An Ji Dalili

  • Barcelona ta soke wasan sada zumuncin da za ta yi da Ittihad Riadi Tangier a Morocco saboda rashin tabbas da ke tattare da wani rikici
  • An shirya gudanar da wasan ne a Tangier ranar 15 ga Agusta a matsayin wani ɓangare na shirye-shiryen Barcelona kafin fara sabon kakar wasa
  • Barcelona za ta ci gaba da shirye-shiryenta da wasannin sada zumunci da Nottingham Forest da Al Ahly kafin fara kare kambun La Liga

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza Daudawa ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida

Barcelona - Kungiyar Barcelona ta soke wasan sada zumuncin da aka shirya za ta buga da ƙungiyar Ittihad Riadi Tangier ta Morocco saboda damuwar da ake da ita kan rikicin da ke ci gaba da faruwa a yankin Ceuta.

An shirya gudanar da wasan ne a birnin Tangier ranar 15 ga Agusta, a matsayin wani ɓangare na shirye-shiryen zakarun Spain kafin fara sabon kakar wasan ƙwallon ƙafa.

Kara karanta wannan

Jama'a sun gigice bayan tsoron fashewar 'bam' a Abuja

Barcelona ta fasa buga wasa da Moroko

Sai dai Barcelona ta sanar da cewa ba za a sake buga wasan ba saboda rashin tabbas da ke tattare da halin da ake ciki a yanzu, kamar yadda BBC ta ruwaito.

Ƙungiyar ta ce:

“Dangane da rashin tabbas da kuma yanayin da ake ciki a yanzu, FC Barcelona na ganin cewa bai dace a buga wasan ba.”

Ko da yake Barcelona ba ta bayyana takamaiman dalilin da ya sa ta soke wasan ba, rahotanni sun danganta matakin da tashin hankalin da ke kewaye da Ceuta.

Ceuta wani yanki ne da ke ƙarƙashin Spain a gabar tekun Arewacin Afirka, wanda ke da iyaka da Morocco.

Lamarin ya ja hankalin duniya bayan ƙaruwa da aka samu wajen tsallakawar 'yan ci-rani daga Morocco zuwa yankin, abin da ya haifar da damuwar diflomasiyya da tsaro tsakanin wasu ƙasashen Turai.

Ko da yake da yawa daga cikin waɗanda suka shiga yankin sun koma Morocco, rahotanni sun ce har yanzu akwai dubban mutane da suka rage a Ceuta.

Kara karanta wannan

Jagorori sun hadu a Masar bayan an gano ƙaruwar ƙin Musulmi a Duniya

Wata tangarda ga Barcelona

Soke wasan da Ittihad Riadi Tangier ya ƙara kawo tangarda ga shirye-shiryen Barcelona na tunkarar sabuwar kakar wasa.

Tun da farko, an soke wani wasan sada zumunci da Preston North End bayan Barcelona ta gudanar da sansanin atisaye a Birtaniya, inda ta buga wasa da Birmingham City.

Duk da haka, Barcelona na shirin ci gaba da shirye-shiryenta da wasu wasannin sada zumunci da suka haɗa da karawa da Nottingham Forest a Udine, Italiya.

Ƙungiyar kuma za ta fafata da Al Ahly ta Masar ranar 19 ga Agusta domin kammala shirye-shiryenta kafin fara kakar wasa.

Barcelona za ta fara kare kambu

Kafar watsa labarai ta ESPN ta rahoto cewa kungiyar da koci Hansi Flick ke jagoranta za ta fara kare kambunta na La Liga ranar 23 ga Agusta.

Barcelona za ta kara da Elche a wasan farko na kakar, inda za ta nemi fara kakar wasan da nasara domin samun kyakkyawan yunƙuri na kare kambun gasar.

Ƙungiyar na fatan shirye-shiryen da take gudanarwa za su taimaka mata wajen shiga sabuwar kakar cikin yanayi mai kyau, duk da soke wasu daga cikin wasannin sada zumuncin da aka shirya mata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com