Zaben Gwamnan Ekiti: Dalilan da Suka Sanya PDP da ADC Kasa Nasara kan APC

Zaben Gwamnan Ekiti: Dalilan da Suka Sanya PDP da ADC Kasa Nasara kan APC

Jihar Ekiti - A ranar Asabar, 20 ga watan Yunin 2026 ne Biodun Oyebanji, ɗan takarar jam'iyyar APC, ya sake lashe zaɓen gwamnan jihar Ekiti.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Gwamna Oyebanji ya samu ƙuri'u 319,224 inda ya doke Wole Oluyede na jam'iyyar PDP, wanda ya sami ƙuri'u 40,543, da kuma Dare Bejide na ADC wanda ya samu ƙuri'u 12,872.

ADC ta fadi zaben gwamnan Ekiti
Wole Oluyede da Dare Bejide na jam'iyyun PDP da ADC Hoto: Wole Oluyede, Amb Dare Bejide
Source: Facebook

Legit Hausa ta fahimci cewa 'yan takarar jam'iyyun PDP da ADC ba su kai labari ba a zaben gwamnan na Ekiti.

Gwamna Oyebanji ya kafa tarihi a Ekiti

Gwamna Oyebanji ya kafa tarihi ta hanyar zama gwamna na farko da ya taɓa samun wa'adin mulki guda biyu a jere tun bayan da aka dawo mulkin dimokuradiyya na Jamhuriya ta huɗu.

Oyebanji ya cimma abin da dukkan tsofaffin gwamnonin da suka gabace shi suka gaza yi a jihar Ekiti, rahoton Premium Times ya nuna hakan.

Hanyarsa ta sake lashe zaɓen ta kasance mai sauƙi mafi yawancinta, kuma yanayin siyasar ya karkata gaba ɗaya domin ba shi fifiko da rinjaye.

Kara karanta wannan

Zaben gwamnan Ekiti: APC ta aika sako ga Oyebanji bayan samun tazarce

Me ya jawo faduwar PDP/ADC a Ekiti

'Yan takarar jam'iyyun PDP da ADC sun zo a matsayin na biyu da na uku a zaben gwamnan jihar Ekiti, bayan gaza yin nasara a kan Biodun Oyebanji.

Jam'iyyar PDP ta shiga zaɓen tana fama da rikicin cikin gida, yayin da jam'iyyar ADC ta gaza samun nasara a kowane zaben tun bayana kafa hadaka a watan Yulin 2025.

Ga wasu dalilan da suka jawo rashin nasarar PDP/ADC a nan kasa:

1. Karfin jam'iyyar APC

Jam'iyyar APC ta shiga zaben a matsayin wadda take kan mulki a jihar Ekiti, inda take da dumbin mabiya da tarin karfin mulki a hannunta.

APC tana da iko da majalisar dokokin jihar Ekiti, 'yan majalisar wakilai na tarayya da sanatoci, wadanda suka ba da ta su gudunmawar wajen cin zaben Gwamna Oyebanji.

2. Ayyukan Gwamna Oyebanji

Gwamna Biodun Oyebanji ya gudanar da ayyukan more rayuwa a jihar Ekiti tun bayan darewarsa kan mulki a shekarar 2022.

Kara karanta wannan

Cikakken sakamakon zaben gwamnan Ekiti kamar yadda INEC ta sanar

Jaridar The Cable ta ce yadda gwamnatinsa ke biyan albashi a kai a kai, saka hannun jari a ayyukan abubuwan more rayuwa, da kuma yanayin siyasa mai ɗan natsuwa duk sun sa masu zaɓe sun ƙara ƙaunarsa.

3. Rikicin PDP

Jam'iyyar PDP ta shiga zaɓen gwamnan a raunace sakamakon rikicin shugabanci, lamarin da ya kawo rarrabuwar kawuna a cikinta.

Wole Oluyede yana ɓangaren sansanin da Kabiru Turaki ke jagoranta, yayin da ɓangaren abokin hamayyarsa da ke marawa Nyesom Wike baya, Ministan Abuja, Nyesom Wike, shi ne wanda INEC ta amince da shi.

Wannan rikici na cikin gida ya bazu zuwa cikin zauren kotu kuma ya jefa fargaba a kan shirye-shiryen jam'iyyar na zaɓen.

Wole Oluyede ya sha kaye a zaben gwamnan Ekiti
Dan takarar gwamnan Ekiti na PDP, Wole Oluyede Hoto: Wole Oluyede
Source: Facebook

4. Rashin tsarin ADC a matakin kasa

Zaben gwamnan jihar Ekiti ya kara nuna rashin karfin tsarin da ADC take da shi a matakin kasa wajen talakawa.

ADC wadda ta gaza samun nasara a kowane zaɓe tun lokacin da ta ɓullo a matsayin haɗaka, ba ta da tsarin da ake buƙata domin fuskantar babban ƙalubale a jihar.

A ƙarshe, rikicin cikin gida na PDP da kuma raunin kasancewar ADC a jihar duk sun ba wa Oyebanji nasara a cikin sauƙi.

Kara karanta wannan

Bayan fafatawar APC da PDP, ADC, INEC ta sanar da wanda ya lashe zaben Ekiti

APC ta taya Oyebanji murna

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar APC ta taya Biodun Oyebanji murnar nasarae lashe zaben gwamnan jihar Ekiti.

APC ta bayyana cewa nasarar gwamnan abin tarihi ce inda ya zama na farko da ya taba samun tazarce a tarihin jihar Ekiti.

Jam'iyyar APC ta kuma nuna godiyarta ga mutanen jihar Ekiti kan yadda suka sake damka amana a hannun dan takararta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng