Manyan Labarai A Yau
Amurka ta ɗage CoE kan jiragen ruwa daga Najeriya bayan shekaru 12, matakin da ake sa ran zai rage jinkiri da kuɗaɗen jigilar kaya da ƙarfafa tashoshin Najeriya.
Jonathan Vatsa ya bukaci Tinubu ya sauya salon mulkinsa tare da komawa ga talakawa, yana mai cewa zaben Osun gargadi ne ga APC kafin zaben shekarar 2027.
Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya ba da umarnin rushe dukkan gidajen da aka gina a hanyoyin ruwa a Abuja ba tare da kyalewa ko wani jigon siyasa ba.
APC ta amince cewa rikicin cikin gida, rashin jituwa kan dan takara da raina karfin Ademola Adeleke sun taimaka wajen kayen jam’iyyar a zaben Osun.
Osita Chidoka ya ce zaben shekarar 2027 zai yi wahala a yi masa magudi idan INEC ta gudanar da shi kamar yadda ta gudanar da zaben gwamnan jihar Osun.
Donald Trump ya ce hana Iran mallakar makamin nukiliya shi ne babban burin Amurka, yayin da tattaunawar diflomasiyya tsakanin Washington da Tehran ta tsaya cik.
Donald Trump ya yi barazanar kai hari kan Oman idan ta kawo cikas ga yarjejeniyar Amurka da Iran kan mashigar Hormuz, tare da kira ga Tehran ta mika wuya.
Shugaban matasan APC, Dayo Israel, ya ce rashin nasarar jam’iyyar a Osun ya kamata ya zama gargadi kafin 2027, tare da yin kira ga APC ta gyara kura-kurenta.
Rundunar ‘yan sandan Kebbi ta samu nasarar kama wata mata, Khadija Ibrahim mai shekaru 19 kan zargin satar jariri a Zuru tare da kai shi wurin mijinta.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari