'Yan Bindiga Sun Farmaki Manoma a Kaduna, an Kashe Bayin Allah
- 'Yan bindiga dauke da makamai sun kai hari kan wasu manoman da ke aiki a gona a jihar Laduna da ke yankin Arewa maso Yamma na Najeriya
- Hatsabiban 'yan bindigan wadanda suka kai harin na bazata, sun bude wuta kan manoman wanda hakan ya jawo aka samu asarar rayuka
- Harin na 'yan bindigan na zuwa ne yayin da damina ta kankama kuma hankalin manoma ya koma kan gonakinsu don noma amfanin gona
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kaduna - Wani mummunan lamari na ban-tausayi ya auku a Gundumar Kuyello da ke karamar hukumar Birnin Gwari a jihar Kaduna sakamakon harin 'yan bindiga.
Lamarin ya auku ne yayin da 'yan bindiga suka far wa gonakin Kujijiro tare da kashe aƙalla manoma tara.

Source: Facebook
Wani masanin harkar tsaro kuma jagoran al'umma, Ishaq Kasai, ya tabbatar da wannan mummunan al'amari ga jaridar Premium a daren ranar Litinin, 22 ga watan Yunin 2026.
'Yan bindiga sun kashe manoma a Kaduna
Ishaq Kasai ya ƙara da cewa har yanzu ba a san inda wasu manoma da dama suke ba bayan harin na 'yan bindiga, Daily Post ta kawo labarin.
“Zan iya tabbatar muku da cewa harin ya faru, kuma abin takaici an kashe tara daga cikin manomanmu lokacin da suke aiki a gonakansu."
- Ishaq Kasai
'Yan bindiga sun bude wuta yayin harin
Ishaq Kasai, wanda shi ne tsohon shugaban kungiyar ci gaban masarautar Birnin-Gwari (BEPU), sai dai ya ƙi bayyana sunayen mamatan, inda ya kafa hujja da wasu dalilai masu alaƙa da “harkokin tsaro.”
A cewar majiyoyi, waɗanda abun ya ritsa da su suna tsaka da yin noma a gonakansu ne lokacin da maharan ɗauke da manyan makamai suka bayyana cikin bazata kuma suka buɗe musu wuta.
Ba a ji ta bakin hukumomi ba
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, rundunar 'yan sanda da jami'an tsaro na jiha ba su riga sun fitar da wata sanarwa a hukumance ba game da wannan kisa na gilla.
Wannan hari na baya-bayan nan ya zama babban cikas ga fafutukar wanzar da zaman lafiya a masarautar Birnin Gwari, bayan da gwamnati ta shiga tsakani domin kulla yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin 'yan bindiga da manoma.

Source: Original
Yankin, wanda ake kallo a matsayin ɗaya daga cikin manyan samar da amfanin gona na jihar Kaduna, yana fuskantar sake ɓullowar ayyukan 'yan bindiga.
Yayin da damina ta riga ta kankama kuma harkokin noma suka yi nisa, fargaba ta ƙara kama al'ummomin manoma.
'Yan bindiga sun kashe mutane a Plateau
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu hatsabiban 'yan bindiga sun kaddamar da sababbin hare-haren ta'addanci a jihar Plateau.
An bayyana cewa akalla mutane 19 sun rasa rayukansu yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon wani harin da ‘yan bindiga suka kai Plateau.
Harin ya faru ne a Kauyen Kawel da ke gundumar Mushere a karamar hukumar Bokkos inda ‘yan bindigan suka yi wa garin kawanya tare da afkawa gidaje.
Asali: Legit.ng

