Fadar Shugaban Kasa Ta Tanka da Peter Obi Ya Nemi Tinubu Ya Yi Murabus
- Fadar shugaban kasa ta yi martani ga Peter Obi bayan ya nemi Shugaba Bola Tinubu ya yi murabus daga gwamnatinsa
- Ta bayyana cewa kwatanta Tinubu da Keir Starmer ya nuna cewa Peter Obi bai san yadda tsarin gwamnatin Najeriya yake ba
- Ta bukaci ya jira har sai zaben shekarar 2027 domin ya san irin kallon da 'yan Najeriya ke yi wa gwamnatin Shugaba Tinubu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Fadar shugaban kasa ta yi watsi da kiran da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NDC Peter Obi ya yi, na neman murabus ɗin Shugaba Bola Tinubu.
Fadar shugaban kasa ta bayyana kiran murabus din Tinubu matsayin wasan yara kuma abin katsalandan marar amfani.

Source: Facebook
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai taimakawa shugaban kasa kan harkokin yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar ranar Litinin, 22 ga watan Yunin 2026 a shafin X.
Ta kafa hujja da bayanan tattalin arziki na ayyukan Tinubu a cikin shekaru uku da suka gabata, tana mai cewa sun sha bamban da tarihin Obi lokacin da yake gwamnan jihar Anambra.
An soki Obi kan kiran Tinubu ya yi murabus
Fadar shugaban kasar ta ce kalaman na baya-bayan nan na Obi wani yunƙuri ne na rage darajar nasarar da APC ta samu a zaɓen gwamnan jihar Ekiti da aka kammala da kuma zaɓubbukan cike gurbi.
Onanuga ya ce kwatanta lamarin Tinubu da na Firaministan Birtaniya, Keir Starmer, wanda ya yi murabus, da Obi ya yi, ya fallasa rashin fahimtar tsohon gwamnan na Anambra game da tsarin mulkin Najeriya.
Ya bayyana cewa hukuncin da Obi ya yanke na cewa Najeriya tana cikin “mafi mummunan yanayi” bai dace da bayanan tattalin arziki da za a iya tabbatarwa ba da kuma kimantawar duniya kan ayyukan gwamnatin.
Wane martani aka yi wa Peter Obi?
"Kalaman baya-bayan nan na Peter Obi na kiran Shugaba Bola Tinubu da ya yi murabus, bisa la'akari da murabus din Firaministan Birtaniya don radin kansa, ba wai kawai sun kauce hanya ba ne, har ma suna nuna ra'ayi na son kai da kuma rashin fahimtar gaskiyar lamarin Najeriya tun daga 2023."

Kara karanta wannan
CUPP ta goyi bayan wasu yan majalisa da suka ba Shugaba Tinubu zabi 1 ko ya yi murabus
“Ra'ayinsa kuma yana da sauƙi na wuce kima, kamar yadda yawancin lokuta yake kasancewa a duk lokacin da ya buɗe bakinsa. Obi ya manta cewa ƙasarmu ba ta amfani da tsarin gwamnati na majalisa kamar na Burtaniya ba.”
"Muna amfani da tsarin shugaban ƙasa ne inda ake zaɓen shugaban ƙasa na ƙayyadaddun wa'adin shekaru huɗu."
“Mutanen jihar Ekiti da mazaɓun sanata na Nasarawa, Enugu, Ondo da Rivers sun riga sun bai wa Shugaba Tinubu da jam'iyyarsa gagarumar nasara."
"Sakamakon zaɓen, wanda ke matsayin wani taron raba-gardama na farko, ya nuna cewa Shugaba Tinubu da jam'iyyarsa suna da farin jini a wurin 'yan Najeriya.”
- Bayo Onanuga

Source: Facebook
An ja kunnen Peter Obi
Fadar Shugaban Ƙasar ta gargaɗi Obi cewa sakamakon zaɓubbukan na baya-bayan nan ya fi zama barazana ga makomarsa ta siyasa fiye da ta Tinubu.
“Wannan ya kamata ya zama abin damuwa ga Peter Obi da sabuwar tafiyarsa ta musamman, NDC, yayin da muke matsawa zuwa zaɓen watan Janairun 2027.
“Ya kamata Obi ya jira har sai lokacin zaɓen shugaban ƙasa domin ya san ainihin abun da mutane ke tunani game da gwamnatin Tinubu.”
“Yin amfani da dandalin X domin matsa wa shugaban kasa lamba ya bar mulki ya kauce wa ka'ida kuma ya saɓawa tsarin dimokuradiyya."

Kara karanta wannan
An bukaci Shugaba Tinubu ya ayyana wani shirin watanni 6 don magance matsalolin Najeriya
- Bayo Onanuga
Makarfi ya ba Tinubu shawara
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Ahmed Mohammed Makarfi, ya ba Shugaba Bola Tinubu shawara.
Ahmed Mohammed Makarfi, ya buƙaci Shugaba Bola Tinubu da ya ayyana dokar ta-ɓaci ta ƙasa a kan matsalar rashin tsaro.
Tsohon gwamnan ya yi gargaɗin cewa taɓarɓarewar tsaro da Najeriya ke fuskanta tana buƙatar daukar muhimman matakai da kuma haɗin gwiwar ƙasa baki ɗaya.
Asali: Legit.ng
