Rikici Ya Barke a Majalisar Dokokin Neja, An Dakatar da Zama kan Wata Takaddama

Rikici Ya Barke a Majalisar Dokokin Neja, An Dakatar da Zama kan Wata Takaddama

  • An samu barkewar rikici a majalisar dokokin jihar Neja a zaman majalisar na yau Litinin bayan wani dan majalisa ya gabatar da sabon kuduri
  • Rikicin dai ya samo asali ne daga batutuwan da suka shafi alakar majalisa da bangaren zartarwa da kuma zabukan fitar da gwani na APC
  • Hayaniya ta barke a zauren majalisar, lamarin da ya tilasta dakatar da zaman bayan mafi yawan ‘yan majalisar sun kada kuri’a kan hakan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Neja - Wani rikici mai zafi ya barke ba zato ba tsammani a majalisar dokokin jihar Neja a ranar Talata, 23 ga Yunin 2023, lamarin da tilasta aka dakatar da zaman ranar.

Rahoto ya nuna cewa zaman majalisar ya rikide zuwa ce-ce-ku-ce mai zafi kan wasu batutuwan da ‘yan majalisar suka ce har yanzu ba a shawo kansu ba tsakanin majalisa da bangaren zartarwa na gwamnati.

Kara karanta wannan

Sabon rikicin makiyaya da manoma ya barke a Kebbi, an rasa rayuka fiye da 5

Rikici ya barka a majalisar dokokin jihar Neja
Zauren majalisar jihar Neja lokacin da Gwamna Umaru Bago ya je gabatar da kasafin kudi. Hoto: Niger State
Source: Facebook

Yadda aka fara zaman majalisa a Neja

Akwai rade-radin cewa matsalolin da ake takaddama a kai na da alaka da korafe-korafen da suka biyo bayan zaben fitar da gwani na jam’iyyar APC da aka gudanar kwanan nan, in ji rahoton Tribune.

An fara samun rashin jituwar ne jim kadan bayan bude zaman ranar, lokacin da dan majalisar da ke wakiltar mazabar Chanchaga, Mohammed Abubakar Kabir (Ustaz), ya gabatar da kudurin a dakatar da ayyukan majalisar har sai an warware matsalolin da ake fama da su.

Kabir ya ce tarihi zai yi wa majalisar mummunan hukunci idan ta kyale matsalolin da ake ciki ba tare da magance su ba.

Rikici ya barke a zaman majalisar Neja

Sai dai ba a ba shi damar fadin cikakken bayanin batutuwan a zauren majalisar ba, inda ‘yan majalisar suka amince cewa za a tattauna batun ne a wani taron sirri na shugabannin majalisar.

Kara karanta wannan

Yau ake gudanar da zabe a Kano, Ekiti da wasu jihohin Najeriya

Lamarin ya kara tsananta ne lokacin da dan majalisar da ke wakiltar Lavun, Jibrin Ndagi Baba, ya kalubalanci kudurin.

Ya dage cewa ya kamata majalisar ta ci gaba da gudanar da ayyukanta saboda ta riga ta dawo daga hutun zaman majalisa, in ji rahoton Daily Post.

Rashin jituwar da aka samu ya haifar da hayaniya a zauren majalisar, lamarin da ya tilasta dakatar da zaman bayan mafi yawan ‘yan majalisar sun kada kuri’ar goyon bayan a dakatar da shi.

Kakakin majalisar Neja, Abdulmalik Sarkindaji ya nemi hadin kan 'yan majalisa
Kakakin majalisar Neja, Abdulmalik Sarkindaji ya na magana a ranar da Gwamna Umaru Bago ya gabatar da kasafin kudi. Hoto: Niger State
Source: Facebook

Shugaban majalisa ya kwantar da hankula

A yayin da ake kokarin kwantar da hankalin ‘yan majalisar, shugaban majalisar dokokin jihar Neja, Abdulmalik Sarkindaji, ya yi kira ga mambobin majalisar su zauna lafiya tare da mutunta ra’ayoyin juna.

Rt. Hon. Abdulmalik Sarkindaji ya bukaci ‘yan majalisar su ci gaba da nuna mutuntaka da fahimtar juna, domin ta hakan ne za su iya gudanar da ayyukan majalisa cikin tsari.

An sako mataimakin shugaban majalisa

A wani labari, mun ruwaito cewa, mataimakin shugaban majalisar dokokin Kebbi, Muhammad Samaila Bagudu ya shaki iskar 'yanci bayan kwashe kwanaki a hannun 'yan bindiga.

Kara karanta wannan

Ekiti 2026: Manyan 'yan takara 3 da ake ganin za su iya samun nasara a zaben

Samaila Bagudu ya shiga hannun 'yan bindiga ne lokacin da suka yi awon gaba da shi jim kadan bayan kammala sallar Isha'i.

Rundunar 'yan sandan jihar Kebbi ta tabbatar da kubutar da mataimakin shugaban majalisar dokokin a wata sanarwa da ta fitar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com