Mariya Bunkure: Ministar Tinubu Ta Kunyata 'Hadiminta' da Ya Yi Nade Naden Mukamai
- Karamar Ministar babban birnin tarayya Abuja, Mariya Mahmoud Bunkure, ta nesanta kanta daga wani mai ikirarin hadiminta ne
- Dr. Mariya ta bayyana cewa mutumin wanda ya yi nade-naden mukamai a karkashin ofishinsa, ba ya aiki tare da ita
- Karamar Ministar ta bukaci jama'a da kafafen yada labarai da su rika samun bayanan ayyukanta daga wuraren da suka dace
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Karamar Ministar Abuja Dr. Mariya Mahmoud, ta nesanta kanta daga wasu naɗe-naɗe da aka yi iƙirarin cewa Bin Usman Rano ne ya sanar da su.
Usman Rano dai ya gabatar da kansa a matsayin hadimin Ministar kan yaɗa labarai kuma ya ambaci sunayen masu ba da shawara guda bakwai a ƙarƙashin ofishinsa.

Source: Facebook
Ministar ta nesanta kanta ne a cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Litinin ta hannun mataimakinta na musamman kan yaɗa labarai, Austine Elemue, wanda aka sanya a shafinta na Facebook a ranar Litinin, 22 ga watan Yunin 2026.
Mariya Bunkure ta nesanta kanta da nade-nade
A cikin sanarwar, an bayyana naɗe-naɗen a matsayin waɗanda ba su da alaƙa da Ofishin karamar Ministar Abuja.
Elemue ya bayyana cewa shi ne kaɗai mataimaki na musamman kan yaɗa labarai da aka naɗa bisa ƙa'ida kuma yake da ikon fitar da sanarwa a hukumance a madadin Dr. Mariya Mahmoud.
Ministar ta ce ba hadiminta ba ne
A cewar sanarwar, Rano ba ya aiki a ofishin Ministar, a maimakon haka yana da alaƙa ne da ƙungiyar "Dr. Mariya Support Group," wata ƙungiyar siyasa da ke goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Abba Kabir Yusuf gabanin babban zaɓen 2027.
“Duk wani naɗi, muƙami, sanarwa ko izini da Usman Rano ya bayar, sun ta'allaka ne kaɗai da al'amuran ƙungiyar tallatawar kuma ba su da wata alaƙa ko kaɗan da ofishin mai girma karamar Ministar Abuja ko hukumar gudanarwar babban birnin tarayya Abuja (FCTA)."
- Austin Elemue
An yi nadi da sunan Ministar Tinubu
An ruwaito cewa Usman Rano ya sanar da naɗin wasu mataimaka bakwai a ƙarshen mako, ciki har da masu ba da shawara kan yaɗa labarai, yarjejeniyar taro, al'amuran ɗalibai, matasa da wasanni, al'amuran addini, da kuma ayyuka na musamman.

Source: Facebook
Ofishin Ministar ya buƙaci jama'a, ƙungiyoyin yaɗa labarai, da hukumomin gwamnati da su dogara ga hanyoyin sadarwa na hukuma kaɗai domin samun bayanai game da ayyukanta da ofishinta.
Sanarwar ta kuma sake jaddada sadaukarwar Ministar ga gaskiya, riƙon amana, da ingantacciyar sadarwa wajen sauke nauyin da ke kanta.
Tinubu ya yi wa Peter Obi martani
A wani labarin kuma, kun ji cewa Fadar shugaban kasa ta yi martani ga Peter Obi bayan ya bukaci Shugaba Bola Tinubu ya yi murabus.
Fadar shugaban kasan ta soki Peter Obi inda ta bayyana kiran murabus din da ya yi, a matsayin katsalandan ga dimojuradiyya.
Ta bayyana cewa kwatanta Tinubu da Keir Starmer, ya fallasa rashin fahimtar tsohon gwamnan na Anambra game da tsarin mulkin Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

