Gwamna Abba Ya Canza Sunan Babban Asibiti a Jihar Kano domin Karrama Mahmoud Baffa Yola
- Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sauya sunan Babban Asibitin Dawakin Tofa zuwa Dr Mahmoud Baffa Yola General Hospital
- Abba Gida-Gida ya ɗauki matakin ne domin karrama marigayi Dr Mahmoud Baffa Yola saboda gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban Kano
- Gwamnan ya kuma umarci Ma’aikatar Lafiya ta fara aiwatar da gyaran asibitin tare da duba kayan aikin lafiya da ake bukata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da sauya sunan Babban Asibitin Dawakin Tofa zuwa Dr Mahmoud Baffa Yola General Hospital.
Gwamna Abba ya yi haka ne domin karrama marigayi Mahmoud Baffa Yola, dattijon kasa da ya yi fice wajen hidimtawa al’umma da ci gaban jihar Kano.

Source: Facebook
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya wallafa a shafinsa na Facebook yau Litinin, 22 ga Yuni, 2026.
Gwamna Abba ya ce an dauki wannan mataki ne domin tabbatar da cewa an ci gaba da tunawa da marigayi Dr Mahmoud Baffa Yola, wanda ya yi fice a harkokin siyasa da gudanarwa tare da ba da gudunmawa mai yawa ga hidimar jama'a.
Yadda ya assasa ilimin dattawa
Gwamnan ya tuna cewa marigayin na daga cikin wadanda suka fara bullo da tsarin ilimin dttwa a jihar Kano, wanda ya ba dubban mutane damar samun ilimi.
Ya ce daga baya gwamnatin marigayi Muhammadu Rimi ta rungumi wannan tsari tare da fadada shi a fadin jihar Kno.
Ya taimaka wajen kafa asibitin
Abba Kabir ya kuma bayyana cewa a shekarar 1989 marigayi Dr Mahmoud Baffa Yola ya jagoranci wani gangamin tara kudade daga al’umma wanda ya kai ga kafa asibitin a garinsu na Dawakin Tofa.
A cewarsa, wannan gudunmawa ce ta sa ya cancanci wannan gagarumar karramawa ta sanya sunansa a matsayin sunan da za a rika kiran asibitin.
Gwamnan ya bayyana marigayin a matsayin jagora mai kishin kasa wanda tarihin hidimarsa ke ci gaba da zaburar da al’umma.

Source: Facebook
Abba ya bada umarnin gyara asibitin
Ya kuma umarci Ma’aikatar Lafiya ta Kano da ta fara aiwatar da gyaran asibitin da gwamnatin ta amince da shi tun da farko, tare da tantance kayan aikin lafiya da ake bukata domin inganta ayyukan jinya.
Gwamna Abba ya ce asibitin na taimaka wa al’ummar Dawakin Tofa, Rimingado, Tofa, Bagwai da sauran kananan hukumomin da ke makwabtaka da su.
Ya jaddada cewa gwamnatin jihar Kano za ta ci gaba da daukar matakan inganta cibiyoyin lafiya domin samar da ingantaccen kiwon lafiya ga jama'a.
Abba ya nemi hadin kan Kwankwaso
A wani rahoton, kun ji cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya roki tsohon ubangidansa, Sanata Rabiu Kwankwaso ya hada kai da gwamnatinsa domin gina sabuwar Kano.
A cewarsa, gwamnatinsa ta kuduri aniyar gina Kano mai zaman lafiya, kwanciyar hankali da ci gaba domin amfanin al’ummar jihar baki daya.
Abba ya nuna damuwa kan yadda Kwankwaso ya ware kansa daga sauran manyan kusoshin siyasar jihar, yana mai kafa hujja da wani taro da aka gudanar.
Asali: Legit.ng

