ADC Ta Tabbatar da Abokin Takarar Atiku bayan Fara Gunaguni kan Zabin Amaechi

ADC Ta Tabbatar da Abokin Takarar Atiku bayan Fara Gunaguni kan Zabin Amaechi

  • Batun dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam'iyyar ADC na neman kawo sabani tsakanin bangarorin Atiku Abubakar da Rotimi Amaechi
  • Sakataren yada labarai na kasa na ADC, Bolaji Abdullahi, ya fito ya yi magana kan batun ko akwai sabani dangane da nadin da aka yi wa Amaechi
  • Bolaji Abdullahi ya bayyana cewa jam'iyya ce ke da hakkin fitowa ta sanar da dan takararta kuma sai ta yi shawara kafin ta yi hakan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Jam'iyyar ADC ta yi watsi da damuwar da ake da ita game da ci gaba da tsit din da aka ji Rotimi Amaechi, ya yi biyo bayan ayyana shi dan takarar mataimakin shugaban kasa a zaben 2027.

Jam'iyyar ADC dai ta sanar da Rotimi Amaechi a matsayin abokin takarar ɗan takararta na shugaban ƙasa a zaɓen 2027, Atiku Abubakar.

Kara karanta wannan

Ekiti 2026: Rigima mai zafi ta kaure tsakanin magoya bayan APC da ADC bayan an jibge kudi

APC ta ba da tabbaci kan zabin Amaechi
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da Rotimi Amaechi Hoto: @atiku, @ChibuikeAmaechi
Source: Twitter

Sakataren yada labarai na kasa na jam'iyyar, Bolaji Abdullahi, ya jaddada cewa babu wani rikici a cikin jam'iyyar, yayin wata tattaunawa a tashar Trust tv a ranar Litinin, 22 ga watan Yunin 2026.

Me ADC ta ce kan Amaechi?

Kakakin na jam'iyyar ADC ya nuna shakku kan dalilin da zai sa ake ran Amaechi ya fito fili ya amince da naɗin da aka yi masa.

“Me kuke son ji? Cewa ya amince? Shin yana da alhakin fitowa ya sanar da cewa ya amince? Domin ya kamata ku san cewa an yi shawarwari kafin hakan ya kai ga fitar da sanarwar da jam'iyyar ta yi.”

- Bolaji Abdullahi

ADC ke da alhakin sanar da dan takara

Kakakin na ADC ya kafa hujjar cewa jam'iyyun siyasa ne, ba 'yan takara ba, ke da haƙƙin sanar da irin waɗannan shawarwari a hukumance, kuma ya jaddada cewa an bi dukkan hanyoyin da suka dace da suka kai ga zabar Amaechi.

Kara karanta wannan

'Za ta karewa Tinubu a 2027,' Momodu ya fadi yadda Atiku zai kifar da APC

“Me kuma kuke tsammani daga ɗan takarar? Ya fito ya ce, 'Iye, jam'iyyata ta zaɓe ni a matsayin abokin takara, na amince'? A ina aka taɓa yin hakan?”

- Bolaji Abdullahi

A cewarsa, rashin fitar da sanarwa a fili daga gefen Amaechi bai kamata a fassara shi a matsayin rashin jituwa ko rashin tabbas ba.

“Jam'iyya ta riga ta ɗauki matsaya, kuma jam'iyya ta sanar. Shin kun ji wani ya fito ya ce, 'A'a, ba gaskiya ba ne, ni ba abokin takara ba ne'? Jam'iyya ta riga ta sanar cewa abokin takararmu a 2027 shi ne mai girma Rotimi Amaechi."

- Bolaji Abdullahi

ADC ta yi magana kan dan takarar mataimakin shugaban kasa
Sakataren yada labaran ADC na kasa, Bolaji Abdullahi Hoto: @BolajiADC
Source: Facebook

Shin Amaechi ya ba da amincewarsa?

Yayin da aka matsa masa lamba kan ko Amaechi ya ba da amincewarsa da kansa kafin a gudanar da sanarwar, Bolaji Abdullahi ya ƙi bayyana takamaiman bayanan tattaunawar cikin gida amma ya jaddada cewa an bi matakan da suka dace.

Ya ƙara da cewa za a gabatar da Atiku da Amaechi gaba ɗayansu ga 'yan Najeriya a hukumance a lokacin da ya dace.

“A ranar da ta dace, za mu bayyana su biyun. Muna da isasshen lokaci. Yakin neman zaɓe ma bai riga ya fara ba. Ba mu ma riga mun ƙaddamar da 'yan takararmu a hukumance ba."

Kara karanta wannan

An dage ci gaba da tattaunawar Iran da Amurka.duk da sanya hannu kan yarjejeniya

- Bolaji Abdullahi

Okonkwo ya dawo daga rakiyar Atiku

A wani labarin kuma, kun ji cewa jigo a jam'iyyar ADC, Kenneth Okonkwo, ya janye goyon bayansa ga Alhaji Atiku Abubakar.

Kenneth Okonkwo ya janye goyon bayansa ne biyo saboda zabar Rotimi Amaechi, abokin takarar Atiku domin zaɓen shekarar 2027.

Ya ce ba zai goyi bayan duk wani tikiti wanda bai dauke da mutumin da ya fito daga yankin Kudu maso Gabas na Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng