Wata Sabuwa: Trump Ya Dauko Batun Kulla Yarjejeniya da Iran bayan Barazana

Wata Sabuwa: Trump Ya Dauko Batun Kulla Yarjejeniya da Iran bayan Barazana

  • Shugaba Donald Trump ya ce ana iya cimma yarjejeniya da Iran kan sake buɗe mashigar Hormuz tun ranar Laraba
  • Trump ya yi barazanar cewa za a kai wa Iran hari mai tsanani idan tattaunawar ta gaza samar da sakamako mai kyau
  • Ana sa ran yarjejeniyar ta bai wa jiragen ruwa damar wucewa cikin aminci tsakanin Iran da Oman na tsawon kwanaki 60

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Washington, Amurka - Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce ana iya cimma yarjejeniya da Iran kan sake buɗe mashigar Hormuz tun ranar Laraba, amma ya yi gargadin cewa za a kai wa Tehran hari mai tsanani idan tattaunawar ta gaza.

Harkar zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar, wadda hanya ce mai muhimmanci wajen jigilar mai da iskar gas a duniya, ta zama babban abin takaddama a tattaunawar

Kara karanta wannan

Rahoto daga Isra'ila ya tona asirin yadda Trump ya shiga tsaka mai wuya kan Iran

Trump ya yi sabuwar barazana
Shugaban kasar Amurka Donald Trump Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Trump ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da tashar Fox News a ranar Talata, 4 ga watan Agustan shekarar 2026.

Trump ya yi magana kan yarjejeniya

Trump ya ce a ranar Talata, 4 ga watan Agustan 2026 cewa ana iya cimma yarjejeniya da Iran kan buɗe mashigar Hormuz “gobe ko washegari.”

Da yake magana da manema labarai a jihar California, Trump ya ce masu tattaunawar sun samu “rana mai kyau ƙwarai.”

Tun da farko, shugaban na Amurka ya yi magana cikin salon barazana.

“Za a buɗe mashigar nan ba da jimawa ba, ko kuma za a kai musu hari mai tsanani, sannan kuma mashigar za ta buɗe,” in ji Trump a wata hira da Fox News.
“Abin da za ku iya yi kawai shi ne ku yi fada har ku fita.”

Ministan baitul malin Amurka, Scott Bessent, ya shaida wa CNBC cewa akwai yiwuwar a cimma yarjejeniya zuwa ranar Laraba ko Alhamis.

Kara karanta wannan

Dama ta karshe": Trump ya yi sabuwar barazana ga Iran

Hare-Hare sun girgiza harkar jiragen ruwa

A yayin da rikicin ke ci gaba da ɗaukar sabon salo, an bayyana wani ma’aikacin jirgin ruwa a matsayin wanda ya ɓace bayan wani abu mai fashewa ya bugi wani jirgin kasuwanci a mashigar Hormuz ranar Talata.

A wani bangare kuma, wani jirgin ruwan Indiya ya nutse a Tekun Bahar Maliya bayan wani hari da ba a bayyana wanda ya kai shi ba.

A makon da ya gabata, Trump ya yi barazanar kai wa Iran hari “mai tsanani,” inda ya nuna cewa za a iya kai hare-hare kan muhimman abubuwan more rayuwar jama'a.

Sai dai daga baya ya sassauta matsayinsa, yana nuna cewa yarjejeniya na gab da samuwa.

Shugaba Trump ya yi barazana ga Iran
Shugaba Donald Trump na kasar Amurka Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Iran ta musanta tattaunawa

Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta musanta cewa tana tattaunawa da gwamnatin Washington. Sai dai Trump ya ci gaba da jaddada cewa ana gudanar da tattaunawar.

Ministan harkokin wajen Amurka, Marco Rubio, ya ce a ranar Talata cewa Amurka tana cikin tattaunawar da Oman da Iran ke yi kan ƙara yawan zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar Hormuz.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Trump ya bayyana zabi 2 da Iran ke da su a yakin da ake yi

Kamfanin yada labarai na Axios ya ruwaito cewa Amurka da Iran da Oman na gab da cimma wata yarjejeniya ta wucin gadi kan sake buɗe mashigar.

Trump ya ba Iran zabi 2

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya ba Iran zabi a yakin da ake yi tsakanin kasashen biyu.

Shugaba Donald Trump ya ce Jamhuriyar Musulunci ta Iran na da zaɓi tsakanin cimma yarjejeniya da Amurka ko miƙa wuya gaba ɗaya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng